Wasu iyalai masu alaƙa da ƙungiyar IS sun koma Australiya bayan shafe shekaru a Syria

Asalin hoton, Getty Images
Wasu iyalai da suka ƙunshi mata huɗu da yara 9 da ke da alaka da ƙungiyar masu ikirarin jihadi na Islamic State, sun isa Australia a yau, bayan shafe shekaru a wani sansani a Syria.
Ƴan sandan Australia sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar za a kama wasu daga cikin matan a kuma tuhume su.
Komawarsu Australia dai ya fuskanci adawa mai ƙarfi a siyasance, amma masu fafutuka na ganin bai kamata a hukunta yaran saboda abin da iyayensu suka aikata ba.
Yaran da ake tunanin shekarun su sun kama ne daga shekara shida zuwa sama - za su sami tallafi ta fannin kula da lafiyar kwakwalwarsu da kuma sauya musu tunani don kar su kasance masu tsattsauran ra'ayi.


