Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 21 ga watan Yuli, 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. ADC ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman karɓuwa - Fadar Shugaban ƙasa

    ...

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da martani kan zargin da jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi na cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na amfani da rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari, don samun tagomashi na siyasa da neman karɓuwa a idon jama'a.

    Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya bayyana zargin na ADC a matsayin “abin kunya,” inda ya ce jam’iyyar ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman suna.

    ADC dai ta ce gwamnatin Tinubu ta yi amfani da yadda aka gudanar da jana’izar Buhari da kuma yadda aka shirya bikin bankwana da shi a Daura da ke jihar Katsina, domin ƙara samun ƙarbuwa a idon ƴan ƙasa.

    Fadar shugaban ƙasar ta ce marigayi Muhammadu Buhari ya cancanci yi masa jana'izar ban-girma kuma sun yi haka ne don girmamawa saboda hakan ne ya dace da shi a matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa.

    Ɓangarori da dama a Najeriya sun yaba da karramawar da gwamnatin ta Tinubu ta yi wa marigayin, sai dai masu suka sun ce gwamnatin na yi ne domin "lallaɓa masoya tsohon shugaban ƙasar da nufin janyo su a jika".

    Ana kallon Buhari a matsayin ɗaya daga cikin ƴan siyasa mafiya karɓuwa tsakanin al'umma a tarihin Najeriya.

    ADC, jam'iyya ce wadda ƴan siyasa masu adawa da gwamnatin ƙasar suka tare a cikinta da nufin haɗa ƙarfi wajen yaƙar jam'iyyar APC mai mulki a babban zaɓen ƙasar da za a yi a 2025.

  2. Iran za ta tattauna da ƙasashen Turai kan shirin nukiliyarta a Istanbul

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa tsakaninta da Birtaniya da Faransa da Jamus a Istanbul kan shirinta na nukiliya.

    Kafar yaɗa labaran Iran ta ce ma'aikatar harakokin wajen ƙasar ta tabbatar da cewa Tehran ta amince da tayin tattaunawar da za a yi a ranar Juma'a.

    Tattaunawar za ta kasance ta farko tun bayan hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai wa Iran a watan Yuni.

    Iran kuma na fuskantar matsin lamba na ta amince ta hau teburin tattaunawa da Amurka.

    Shugabannin ƙasashen Turai sun ce za su lafta wa Iran sabbin takunkumai idan har babu ci gaba a yarjejeniyar nukiliyar

  3. MDD ta gargaɗi Isra’ila kan tilasta wa al'ummar Deir al-Balah na Gaza tashi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce umurnin da sojojin Isra'ila suka bai wa Falasɗinawa na ficewa tsakiyar Gaza, babban koma baya ne ga ƙoƙarin ceton rayukan al'ummar yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.

    A ranar Lahadi ne Isra’ila ta umarci Falasɗinawa a Deir el-Balah, da su koma kudancin Gaza saboda ayyukan soji.

    MDD ta sake nanata gargaɗin da ta yi cewa al'ummar Gaza da dama na mutuwa saboda yunwa kuma suna buƙatar agajin abinci cikin gaggawa yayin da Isra'ila ke ci gaba da taƙaita shigar da kayan agaji.

  4. Sabon rikici ya ɓarke a yankin Sweida na Syria

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce wani sabon rikici ya ɓarke a yankin Sweida na Syria inda aka kashe mutum sama da 110 a cikin mako guda na rikicin kabilanci.

    Hukumar da ke sa ido kan rikicin Syria ta ce an kai wa ƙauyuka da dama hari ciki har da al-Ariqah inda aka ƙona gidaje.

    Mayakan Bedwin da sauran masu taimaka masu sun janye daga Sweida amma sun kasance a wajen garin.

    Rikicin ɗaya ne daga cikin manyan ƙalubalen da ke gaban sabon shugaban ƙasar ta Syria

  5. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Litinin.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.