Gasar kofin duniya 2026: Ghana ta bukaci a duba dalilin hana Partey shiga Kanada

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan gasar kofin duniya 2026 da aka fara ranar Juma'a a birnin Mexico

Taƙaitattu

  • Gasar cin kofin duniya ta 2026: Amurka da Kanada za su fara wasannin farko
  • Mexico ta fara gasar kofin duniya da cin Afirka ta Kudu 2-0 a Mexico City
  • Koriya ta Kudu ta doke Jamhuriyar Czech da ci 2-1 a ɗaya wasan rukunin A
  • A karon farko a tarihi an kori mutum uku a wasan farko a gasar kofin duniya
  • Gasar Kofin Duniya 2026: Me kuke son sani kan wasan Mexico da Afirka ta Kudu?
  • Wane ne zai lashe gasar cin kofin duniya na bana?
  • Kasa 10 ce daga Afirka da za su buga gasar kofin duniya a bana
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Lokaci ya yi da za a fara wasan farko a gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Za a fafata tsakanin tawaga 48, wasanni 104 da za a yi a birane 16.

    Gasar cin kofin duniya mafi girma a tarihin shekara 96 da ake gudanar da wasannin.

    Gasar cin kofin duniya a kan titi

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a wannan lokacin da za mu kawo muku kai tsaye a wasan gasar kofin duniya tsakanin Mexico da Afirka ta Kudu.

    Sunana Mohammed Abdu zan gabatar muku da shirin tare da taimakon AI, za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.