Rufewa
Masu bin shafin namu nan kuma muka kawo ƙarshensa.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 06/04/2025
Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin namu nan kuma muka kawo ƙarshensa.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Shugabar ƴan'adawa a Faransa, Marine Le Pen ta shaida wa magoya bayanta cewa, ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da hukuncin da aka yanke mata kan almubazzaranci da dukiyar ƙasa, lamarin da ya sa aka haramta mata tsayawa takara.
Shugaban jam'iyyarta, Jordan Bardella ya shaida wa gangamin magoya bayanta cewar, kotu ta yanke mata hukunci ne don a hana ta shiga takarar shugabancin ƙasa.
Abinda ya kira hari ga dimukuradiyya kai-tsaye.
Jordan Bardella shugaban jam'iyyar Marine Le pen ya ce yana tabbatar wa abokansa ba iya Ms Lepen aka yi wa rashin adalci ba, ita ma dimokuradiyya an shaƙe ta.
To sai dai shugaban jam'iya mai mulki, Gabriel Atta ya goyi bayan hukunci inda ya ce ''ka yi sata ka biya''.
Rundunar ƴansandan Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi na II bisa wata hatsaniya da ta faru a ranar Idin Ƙaramar Sallah.
A kwanakin da suka gabata ne dai rundunar ta gayyaci sarkin domin bayar da bahasi kan abin da ya faru ranar Idin ƙaramar sallah lokacin da sarkin ke komawa gida a kan doki bayan kammala sallar Idi, inda wasu matasa suka far wa tawagarsa har suka halaka ɗaya daga cikin masu ba shi kariya..
To sai dai cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce ta janye gayyatar bisa shawarar wasu mutane da ƴansandan suka kira ''masu ruwa da tsaki da take kimantawa''.
Haka kuma ƴansanda sun ce daga cikin dalilan janye gayyatar har da muradin babban sifeto ƴansandan na tabbatar da cewa ba a siyasantar da aikin ƴansanda ba ko yi wa aikin mummunar fahimta.
''A maimakon haka babban fifeton ƴansandan ya aike da wata tawagar rundunar ta sashen tattara bayanan sirri da su je fadar sarkin domin jin bahasinsa kan abin da ya farun'', in ji sanarwar.
Gabanin bukukuwan ƙaramar sallah ne dai rundunar ƴansanda reshen jihar Kano ta fitar da sanarwar hana Hawan Salla, saboda bayan da ta ce ta samu na sirri da ke nuna cewa za a iya samun tashin hankali.
Hukumar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa a Najeriya, NCDC ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar sanƙarau a Najeriya ya kai 156.
Jaridun ƙasar sun ambato wani rahoto da hukumar ta fitar da ke nuna ƙaruwar waɗanda suka kamu da cutar daga 74 zuwa 156 a jihohin ƙasar 23.
Jihohin da aka fi samun yawan mace-macen sun haɗa da Kebbi, da Sokoto da Katsina da Jigawa da Yobe da Bauchi da Gombe da Borno da Kano da Adamawa da kuma Oyo.
NCDC ta ce ta tabbatar da kamuwar wasu mutum 126 daga cikin mutum 1,858 da aka yi zargin suna dauke da cutar a jihohin ƙasar 23.
Cutar Sanƙarau dai cuta ce da aka fi ɗauka galibi a lokacin zafi.
Wasu mutanen na iya yaɗa cutar ba tare da sun san suna ɗauke da ita ba, akasarin mutanen da ke ɗauke da ita ba su sani ba.
Wasu daga cikin alamomin cutar sun haɗa da
Ana faragabar ambaliya ruwa ta kashe aƙalla mutum 30 bayan ruwan sama mai ƙarfi a babban birnin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo.
Gwamnan Kinshasa, Daniel Bumba ya ce zaftarewar ƙasa ta haifar da ɓarna.
Ruwa ya mamaye gidaje da tituna gaba ɗaya, yayin da dubban mutane suka rasa muhallansu lokacin da kogin Ndjili ya ɓalle.
An jima ana kiraye-kirayen a inganta gine-gine a babban birnin Congo.
Kinshasa na fuskantar yawaitar ambaliyar ruwa sakamakon gine-gine ba bisa ƙa'ida ba da rashin kulawa.
Ministan harkokin wajen Faransa, Jean- Noel Barrot ya bayyana cewa ƙasar da kuma Algeria sun amince da sake farfaɗo da ƙawance da ke tsakaninsu.
Mista Barrot na jawabi ne bayan ganawa da shugaban ƙasar Algeria, Abdelmadjid Tebboune.
Rikicin diplomasiyya da aka kwashe wata takwas ana yi tsakanin ƙasashen biyu ya haifar wa Faransa barazanar tattalin arziki da tsaro a ƙasar da ta yi wa mulkin mallaka.
Takun saƙar ƙasashen biyu ta faro ne lokacin da Faransa ta mara wa Morocco baya kan ƴancin kan yankin Western Sahara da ake taƙaddama a kansa.
Matakin an zuwa ne a daidai lokacin da wasu ƙasashen Yammacin Afirka ke raba da gari da Faransar.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Southampton ta kasance ƙungiya ta farko a gasar Premier da ta faɗi daga gasar yayin da ya rage wasa bakwai a ƙarƙare gasar.
Ƙungiyar ta hada maki 10 kacal a wasa 31 da ta buga, lamarin da ya sa ta zama ta ƙarshe a kan teburin gasar.
Fatan ƙungiyar na ci gaba da kasancewa a gasar ya zo ƙarshe ne bayan da ta sha kashi a gidan Tottenham ranar Lahadi da ci 3 -1.
A kakar da ta gabata ne ƙungiyar ta hauro gasar.
Ƙaungiyar Tarayyar Afirka ta amince da naɗin shugaban ƙasar Togo, Faure Gnassingbé a matsayin sabon mai shiga tsakani a tattaunawar kawo ƙarshen rikicin DR Kongo da Rwanda da ma ƙungiyar M23.
Mista Gnassingbé zai maye gurbin shugaban Angola, João Lourenço a wannan aikin.
Zaɓar shugaban na Togo na zuwa ne gabanin taron da aka tsara gudanarwa a Qatar ranar Laraba tsakanin gwamnatin Kongo da ƴantawayen ƙasar.
ƴantawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun ƙwace garuruwa masu yawa a gabashin DR Kongo tun watan Janairun shekarar da muke ciki.
Rikicin ya raba dubban mutane tare da raba aƙalla mutum 500,000 da muhallansu.
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi Allah wadai da kashe-kashen da wasu mahara suka yi a garuruwan Ruwi da Manguna da Daffo da Josho da Hunti da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato, inda ta bayyana kisan da na rashin hankali.
Shugaban ƙungiyar, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka, inda ya ce harin - wanda ya ci rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu ciki har da mata da ƙananan yara - yana bazarana ga zaman lafiya da ci gaban yankin arewacin ƙasar.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya ce, "rayuwar ɗan'adam na da daraja da ta wuce a wulaƙanci," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna Inuwa ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang bisa matakan da ya ɗauka, sannan ya yi kira ga jami'an tsaro su ƙara ƙaima wajen kamo waɗanda suke da hannu a kashe-kashen.
"A matsayinmu na gwamnonin arewa, za mu cigaba da ƙoƙari domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin."
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana shan suka bayan kama wasu mutum biyu na kusa da shi bisa zarginsu da alaƙa da Qatar.
A ranar Talata cewa wata kotun Isra'ila ta tsawaita tsare Yonatan Urich, wanda hadimin Netanyahu ne da Eli Feldstein, wanda tsohon kakakinsa ne domin a ƙara bincike. Sai dai dukansu sun musanta aikata wani laifi.
Netanyahu - wanda shi ma da kansa ya bayar da bahasi a gaban ƴansanda game da binciken na "Qatar-gate" ba a bayyana shi a cikin waɗanda ake zargi ba.
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya sallami ɗaya daga cikin mataimakansa saboda wata tafiya shaƙatawa zuwa Antarctica da ya yi tare da matarsa Nowruz.
Shugaban ya sallami mataimakin nasa ne saboda abin da ya bayyana da "almubazzaranci" da kuɗi.
Ofishin shugaban ƙasar ya ce tafiya ta mataimakin shugaban ƙasa Shahram Dabiri "ba ta dace ba a daidai lokacin da Iran ke fama da matsain tattalin arziki, kuma ƙasar ba za ta aminta ba."
An ta yaɗa hotunan Dabiri da matarsa ne suna shaƙatawa a kafofin sadarwa a Iran, inda suka jawo ce-ce-ku-ce da suka a tsakanin al'ummar ƙasar.
Pezeshkian ya ce ya sallami Dabari a matsayin mataimakin shugaban ƙasa mai kula da harkokin majalisa saboda "'almubazzaranci' wajen kashe kuɗi, ko da kuwa daga aljihunsa ya ɗauki nauyin zuwa shaƙatawar.
"A gwamnatin da ke bin tafarkin imam na farko na Shia wato Imam Aali, tafiyar da za a kashe maƙudan kuɗi ba ta dace ba ga jami'in gwamnatin ko da kuwa daga aljihunsa ya kashe kuɗin," in ji Pezeshkian.
Sojojin Najeriya masu aiki na musamman na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun sanar da kashe ƴanbindiga uku, sannan suka lalata mazauninsu tare da ƙwace makamai a ƙaramar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.
Sojojin sun samu nasarar ce a ranar 5 ga Afrilu, kamar yadda kakakin sashen Olubodunde Oni ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa da sojojin suka isa yankin Chibi, sai ƴanbindigar suka fara tserewa, "inda sojojin suka bi sahunsu suka yi musayar wuta, inda dakarunmu suka kashe ƴanbindigar guda uku, sannan suka tarwatsa mazauninsu, tare da ƙwato makamai."
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin na Najeriya sun yi sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle a kwanakin baya, inda suka tarwatsa mazaunan ƴanbindiga da dama.
Gargaɗi: Wannan labarin Ya ƙunshi kalamai masu banƙyama da kwatancen cin zarafi mai alaƙa da jima'i
A wani daren watan Fabrairu ne wani mummunan saƙo ya shiga cikin akwatin saƙon Hannah Grundy a Sydney.
"Zan ci gaba da aika miki saƙon imel saboda ina ganin wannan ya cancanci ki mayar da hanlkali a kansa," wani wanda bai bayyana sunansa ba ya rubuta.
A cikin saƙon akwai wani link, tare da gargaɗin da cewa : "[Wannan] ya ƙunshi abubuwa masu tayar da hankali."
Hamshaƙin attajirin nan a ɓangaren fasaha Elon Musk wanda yake shugabantar hukumar da aka ɗorawa alhakin rage yawan kashe-kashen kuɗaɗen gwamnati a Amurka ya shaida wa wani taron siyasa a Italiya cewa yana fatan a gaba Turai da Amurka za su daina taƙaddamar kasuwanci su koma tsarin kasuwanci maras shinge.
Yana magana ne yayin da sabbin harajin da ShugabaTrump ya ƙaƙaba suka soma aiki lamarin da ya jefa tattalin arziki da kuma siyasar duniya cikin ruɗani.
Shugaban ya buƙaci Amurkawa da su jure wa yanayin da ake ciki bayan faɗuwar da kasuwar hannayen jarin Amurka ta yi.
Shi kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Faransa da Birtaniya za su daidaita matsayarsu a tattaunawa da Amurka game da sabbin harajin domin kare al'ummarsu da kuma harkokin kasuwanci.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce zai ƙwace takardun biza na duk masu riƙe da fasfon Sudan ta Kudu sannan zai taƙaita ba su duk wata bisa a gaba.
Ya ce an ɗauki matakan ne saboda gwamnatin rikon ƙwarya ta Sudan ta Kudu ta gaza karɓar ƴanƙasarta da aka mayar da su gida.
Wakiliyar BBC ta ce gwamnatin ta bayyana cewa ƙasashen da suka ki karɓar jama'arsu za su fuskanci hukunci ciki har da janye takardun bisa da kuma ƙaƙaba haraji.
Sudan ta Kudu na fuskantar matsala tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa da barazanar sake komawar ƙasar cikin yaƙin basasa bayan da Shugaba Salva Kir ya yi wa tsohon abokin hamayyarsa kuma mataimakin shugaban ƙasar, Riek Machar, ɗaurin talala.
Dubun dubatar mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Washington da sauran manyan biranen Amurka a jiya Asabar inda suke tur da Shugaba Trump da kuma abin da suka kira manufofinsa na kama-karya.
Ita ce zanga-zanga mafi girma da aka yi a yini guda don nuna adawa da ƙudirorin Trump tun bayan komawarsa Fadar White House.
Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da yadda aka kori ma'aikatan gwamnati daga aiki da sabbin harajin kasuwanci da ya ƙaƙaba wa ƙasashe.
A cewar wakilin BBC wasu sun soki manufofinsa na ƙasashen waje, wasu sun ɗaga tutar Ukraine yayin da wasu kuma suka riƙe tutar nuna goyon baya ga Falasɗinawa.
Galibin mutanen sun ce matakan da gwamnatin Tump ke ɗauka za su yi wa tattalin arziki illa tare da raunata Amurka.
Rundunar ƴansandan jihar Abia da ke kudu maso kudancin Najeriya ta tabbatar da kashe wasu ƴan ƙasar China guda biyu da wani ɗansanda mai ba su kariya.
Rundunar ta ce ƴansanda sun ɗauki ne bayan rundunar ta samu kiran kar-ta-kwana cewa wasu gungun mahara sun kai wa ƴan Chinan da ƴansanda da ke rakiya hari a hanyarsu ta zuwa kamfaninsu da ke titin Agukwu-Amaya a garin Ndundu a ƙaramar hukumar Isuikwuato na jihar.
A wata sanarwa da tashar Channels ta ruwaito daga kakakin rundunar ƴansandan jihar, Maureen Chinaka yana cewa an kashe Mista Quan wanda shi ne manajan kamfanin da Mista Cai abokin aikinsa da Insfekta Audu Saidu.
Rundunar ta ƙara da cewa jami'anta sun samu nasarar ceto wasu ƴan China huɗu da ƴansanda guda biyu.
A sanarwar, kwamishinan yansandan jihar, Danladi Isa ya ce jami'ansa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba har sai sun kama waɗanda suka aikata kisan.
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce a shirye yake ya tattauna da Amurka bayan da Shugaba Trump ya yi barazanar kai wa ƙasar hari idan ta gaza ƙulla yarjejeniya kan shirinta na nukiliya.
Sai dai babu tabbas kan ko Tehran za ta yi tattaunawar gaba da gaba da Mista Trump ke son a yi.
A baya, ta ƙi amincewa da haka saboda matsin lamba da kuma barazana daga Amurka.
Kafafen watsa labarai na ƙasar sun ruwaito cewa babban kwamandan rundunar juyin juya hali ta Iran ya ce ƙasar a shirye take a yi yaƙi amma ba za ta takalo shi ba.
A Najeriya, wasu kamfanonin sufurin hajji da umarah na Najeriya sun bayyana janyewarsu daga hada-hadar aikin hajjin bana, saboda yadda suka ce hukumar alhazan Najeriyar tana gudanar da wasu ayyuka da kamfanonin ya kamata su riƙa aiwatarwa.
Malam Haruna Isma'il shugaban ɗaya daga cikin kamfanonin uku, ya ce sun kwashe tsawon shekara uku suna neman a yi gyara, amma ba a yi komai ba.
Malam Haruna Isma'il shugaban kamfanin harkar sufurin hajji da umarah na Annur Air Services ya karan-tsaye da wuce gona da iri da acewarsa suke cutar da alhazai da masu harkar jigilar ne suka sa suka yanke shawarar janyewa daga aikin.
Mun dai nemi jin ta bakin jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar alhazai ta Najeriya, wadda ta yi alƙawarin aiko mana da nasu martanin kan wannan batu, amma har ya zuwa yanzu babu bayani daga wajenta ba.
Rundunar sojin Isra'ila ta amince cewa sojojinta sun yi kuskure a kisan wasu ma'aikatan agaji 15 a Gaza bayan ɓullar wani bidiyo da ke aza shakku kan yadda lamarin ya faru.
Wakilin BBC ya ce a wani taro, wani jami’an Isra’ila ya yarda cewa akwai kuskure a bayanan.
Isra’ila dai ta dage cewa shida daga cikin ma’aikatan agajin suna da alaƙa da Hamas amma ba ta fitar da hujjar tabbatar da iƙirarin ba.
An kai wa ayarin motocin hari ne kusa da Rafah a watan da ya gabata.
Isra'ila tun farko ta ce motocin sun bayyana cikin duhu ba tare da kunna fitulunsu ba.
Sai dai bidiyon da wani ma'aikacin jinya ya naɗa wanda shi ma aka kashe a harin da alama ya ci karo da iƙirarin da aka yi tun da farko.
Wani jami'in Isra'ila ya ce sojoji sun yi tunanin tawagar barazana ce lokacin da ta tsaya kusa da wata mota da mayaƙan Hamas suka taɓa amfani da ita.