Ƙasashen Sahel na atisayen nuna ƙarfin soji a Nijar

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashe biyar a yankin Sahel na gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa a yammacin jamhuriyar Nijar, wanda shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan atisayen a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na masu iƙirarin jihadi.
Kafar yaɗa labaran kasar ta Nijar ta bayar da rahoton cewa sama da sojoji 2,500 daga ƙasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Nijar da kuma Togo ne ke gudanar da wannan shirin.
Hukumomin soji a Burkina Faso da Nijar da Mali na ƙara neman goyon bayan Rasha bayan korar dakarun Faransa da ta yi mulkin mallaka a Nijar daga ƙasar
Waɗannan ƙasashe dai sun fice daga ƙungiyar Ecowas na yankin yammacin Afirka a watan Fabrairu tare da ƙulla yarjejeniyar kare juna da aka fi sani da kawancen kasashen Sahel.
- Me ya rage wa Nijar, Mali da Burkina Faso bayan ficewa daga Ecowas?
- Jamhuriyar Benin za ta haɗa kai da ƙasashen da aka yi juyin mulki







