Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 19 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Muhammad Annur Muhammad

  1. Usyk ya zama zakaran duniya na damben ajin masu nauyi

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan damben boksin na ƙasar Ukriane, Oleksandr Usyk ya zama zakaran duniya na ajin masu nauyi a karon farko cikin shekara 25.

    Usyk ya doke Tyson Fury na Birtaniya bayan zagaye 12 a fatatawar da aka yi a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

    Duk da rashin nasarar da Fury ya yi, shi ne zai samu kaso mafi tsoka na kuɗin da za a biya 'yan damben, wanda ake hasashen adadinsu zai kai dala miliyan 100.

  2. Amurka ta tattauna da Saudiyya kan yaƙin Gaza

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro ya tattauna da yarima mai jiran gado na Saudiyya a wani sabon mataki na shirin diplomasiyyar Amruka na ƙoƙarin dakatar da yaƙin Gaza.

    Jake Sullivan ya gana da Mohammed bin Salman a birnin Dhahran a ƙasar Saudiyya.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ce tattaunawar ta ƙunshi yadda za a ɓullo da hanyoyin samar da kayan agaji zuwa Gaza.

    Rahotonni na cewa akwaiyiywuwar Isra'ila ta rage zafafa hare-haren da take kai wa Rafah, yayin da Mista Sullivan ke yankin Gabas ta Tsakiya.

    Ana sa ran ci gaba da tattaunawa tsakanin jami'an Amurka da na Isra'ila a cikin wannan wata.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da makwabtanta.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa muku