Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 17 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Ku san Malamanku tare da Malam Ibrahim Mai Ashafa

    Fitaccen malamin nan na jihar Kano Malam Ibrahim Kabiru wanda aka fi sani da Malam Ibrahim Mai Ashafa ya ce ba bu inda ya fi burge shi cikin littafin Ashafa kamar babin suffofin Annabi Alaihissalam.

    Malamain wanda aka haifa a jihar Kano a 1976, ya ce ya tashi ne a gaban Sheik Aliyu Harazimi, ya ce babu wani waje a cikin littafin Ashafa da ba ya da daɗin karantawa.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  2. Matatar man fetur ta Dangote za ta sayi ɗanyen mai ganga miliyan 24 daga Amurka

    .

    Asalin hoton, Others

    Matatar mai ta Dangote na shirin sayo aƙalla ganga miliyan 24 na ɗanyen man fetir daga Amurka nan da shekara mai zuwa domin ƙarfafa ayyukan matatar.

    Cikin wani rahoto da jaridar Bloomberg ta fitar, ya nuna cewa matatar man fetir ɗin ta gabatar da buƙatarta nasayen ganga miliyan biyu a kowane wata daga kamfanin dilklancin man fetur na 'West Texas Intermediate Midland' har na tsawo wata 12 da za a fara daga watan Yuli, wanda hakan zai sa matatar ta sayi ganga miliyan 24 a tsowan shekarar.

    Buƙatar neman man fetur daga Amurka na nuna irin fama da ƙarancin tono mai da ƙasar ke fama da shi, tare da nuna irin tasirin da matatar za ta yi a kasuwan man fetur ta duniya, da zarar ta fara aiki.

    Najeriya dai ta kasa cimma kason da ƙungiyar OPEC ta ware mata na yawan man da za ta fitar na aƙalla shekara guda.

    A watan Afrilu ƙasar ta riƙa tono kusan gangar mai miliyan 1.45 a kowace rana, abin da ya yi ƙasa da kason da OPEC ta ware wa ƙasar na ganga miliyan 2.6 a kowace rana

  3. Gwamnatin Najeriya za ta buɗe shafin neman bashin ɗalibai cikin mako mai zuwa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Asusun Kula da Bashin Karatu ga Dalibai na Najeriya (NELFUND), ya ce zai buɗe shafin neman bashin karatu ga ɗaliban ƙasar da ke sha'awar karɓar bashin a ranar 24 ga watan Mayu domin su cike.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun asusun, Nasir Ayitogo ya fitar ya ce bayan buɗe shafin ɗalibai za su iya neman bashi domin ci gaba da biyan kuɗin karatunsu ba tare da wata matsala da ta danganci kuɗi ba.

    “Shafin zai kasance mai sauƙin ta'ammali, ta yadda ɗaliban za su iya cike shi cikin sauki tare da aikewa da buƙatarsu ba tare da wata tangarɗa ba'', in ji sanarwar.

    Sanarwar ta kuma yi kira ga duka ɗaliban ƙasar da suka cancanci cin bashin karatun da su yi amfani da wannan dama wajen gyara makomarsu da kuma ci gaban ƙasar baki ɗaya.

    ''Daliban za su iya samun shafin a kan wannan adireshi: http://nelf.gov.ng domin fara cike buƙatarsu da zarar lokacin ya yi'', in ji sanarwar.

    A shekarar da ta gabata nedai shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ɓullo da tsarin bayar da bashi ga ɗaliban ƙasar domin samun damar faɗaɗa karatunsu a manyan makarantun ƙasar, a wani mataki na rage wa ɗaliban wahalhalun da suke fuskanta da suka danganci kuɗi.

  4. Lauyoyin Isra'ila za su bayar da bahasi a Kotun Duniya kan ƙarar Afirka ta Kudu

    A yau ne Lauyoyin da ke kare Isra'ila za su mayar da martani a kan kiran da Afirka ta Kudu ta yi na kawo ƙarshen matakin sojin da Isra'ila ta ɗauka a Rafah da kuma sassan Gaza a babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya.

    Gwamnatin Isra'ila ta yi korafin cewa Afirka ta Kudu na amfani da kotun ne domin ta kawo cikas ga harkokin shari'a.

    Ma'aikatar harkokin wajen isra'ila ta ce an gabatar da korafe korafe a kan Hamas a kotun.

    Sannan kuma ta haƙiƙance Isra'ila na ɗaukar mataki ne kamar yadda dokokin duniya suka tanadar a kan Hamas.

    Lauyoyin Afirka ta Kudu sun shaida wa kotun da ke birnin Hague cewa dama tun da farko Isra'ila na da niyyar lalata rayuwar Falasdinawa ne.

    Daya daga cikin lauyoyin ta ce idan ba man fetur asibitoci ba za su iya kula da kwalbar da ake ajiye jarirai ba, sannan ba za a iya amfani da injinan da ake amfani da su wajen taimaka wa masu fama da matsalar numfashi ba.

    Asibitoci a Gaza sun shiga wani yanayi na ƙarancin abinci da man fetur da iskar Oxygen da magunguna da kuma alluran kashe radadi.

  5. Senegal na duba yiwuwar rufe sansanonin sojin Faransa a ƙasar

    ..

    Asalin hoton, Senegal Presidency/X

    Firaministan Senegal Ousmane Sonko, ya bayyana yiwuwar rufe sansanin sojin Farance da ke ƙasar.

    Da yake jawabi a wajen wani taro a Dakar, ya ce me yasa har yanzu Senegal ke da sansanonin sojin Faransa shekaru 60 bayan samun 'yancin kai daga Faransar.

    Mista Sonko ya ce mene ne amfanin kasancewar sojin Faransa a ƙasar da ke da 'yancin kanta?

    Akwai sojojin Faransa kusan 350 a Senegal

    Firaministan ya alƙawarta ƙarfafa dangantaka da Mali da Burkina Faso da kuma Nijar waɗanda tuni suka kori sojojin Faransa daga ƙasashensu sannan suka mayar da hankali wajen neman taimakon Rasha a yaƙin da suke da masu ikirarin jihadi.

  6. Assalamu Alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da Hausawa ke yi wa kirari da Haji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ne fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.

    Ku biyo mu...