Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 13 ga watan Mayun, 2024.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Umar Mikail
Yadda zanga-zangar ƙarin kuɗin wuta ke gudana a Kwara
Hotunan masu zanga-zangar ƙarin kuɗin lantarki a Ekiti
EFCC ta kama wasu mutum 26 da ake zargi da damfarar Intanet a Fatakwal
Jami’an Hukumar yaƙi da cin hanci da rahsawa EFCC na shiyyar Fatakwal sun kama wasu mutum 26 da ake zargi da damfara ta intanet a ta wuraren gidan talabijin na Najeriya da Choba na Fatakwal, jihar Ribas.
Hukumar EFCC ta ce a shifin sada zumuntanta na X cewa an kama su ne biyo bayan sahihan bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na hannu a ayyukan da suka shafi intanet.
Kayayyakin da aka ƙwace daga hannun su dai sun haɗa da wayoyi daban-daban da kwamfutoci da manyan motoci guda shida.
Za a kuma gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Yadda ƴan ƙwadago suka mamaye kamfanin IBEDC a Ogun
Yadda zanga-zangar NLC da TUC ke gudana a Abuja cikin hotuna
Gamayyar ƙungiyar ƙwadago na zanga-zanga kan ƙarin kuɗin lantarki a Najeriya
A yau Litinin ne ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC da takwararta ta TUC ke dafifi a harabar ofishin hukumar kula da lantarki ta ƙasar NERC da na kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki a faɗin Najeriya domin nuna adawa da ƙarin kuɗin wuta a ƙasar.
A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin kuɗin wuta ga ƴan rukunin A masu samun wuta tsawon sa'a ashirin a rana.
Lamarin ya fusata al'umma ganin irin halin matsi da ƴan Najeriya ke ciki.
Duk da cewa NERC ta yi nazari kan ƙarin kuɗin amma gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce za su mamaye harabar ofishin hukumar da kuma kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki bayan da wa'adin da suka bayar na ranar Lahadi don hukumar ta soke ƙarin kuɗin ya cika.
Ƙarin kuɗin wutar na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya sakamakon hauhawar farashi da kuma ƙalubalen da ƴan Najeriya suke fuskanta sanadin janye tallafin man fetur.
Sai dai a lokacin da yake kare matakin, ministan lantarki, Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya za ta biya kimanin naira miliyan 1.8 a matsayin kuɗin tallafi na lantarki a kasafin kuɗin 2024.
Ya bayyana cewa dokar lantarki ta 2023 ta ba da izinin a yi nazarin kuɗin wuta sau biyu a shekara.
Adadin waɗanda suka mutu sanadin ginin da ya ruguje a Afrika ta Kudu ya kai 24
Hukumomin kasar Afrika ta Kudu sun ce adadin wadanda suka mutu sanadin wani gini da ya ruguje a ranar Litinin da ta gabata a birnin George da ke kudancin ƙasar ya kai 24.
Har yanzu kuma ana ci gaba da kokarin ceto tare da kwato gawarwakin wasu mutane 28 da suka makale a karkashin baraguzan ginin.
Mutane 81 ne ke cikin ginin mai hawa biyar a lokacin da ya ruguje.
Daga cikin mutum 29 da suka tsira, 13 na kwance a asibiti.
Ana dai binciken musabbabin rugujewar ginin.
Sojoji sun gano haramtattun matatun mai 50 a Neja Delta
Rundunar sojin Najeriya ta bankaɗo haramtattun matatun mai 50 a dajin Biseni da ke ƙaramar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa, a Neja Delta mai arzikin man.
Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation Delta Safe a yankin Neja Delta, Rear Admiral John Okeke wanda kuma ya jagoranci samamen ne ya bayyana haka.
Okeke wanda yake magana da ƴan jarida ya ce a ranar 9 ga watan Mayu, sun kai samame ƙaramar hukumar Ukwa ta Yamma da ke jihar Abia kan iyaka da Rivers, ya kuma ce za su ci gaba da kai irin wannan samame domin gano wasu matatun mai da ake gudanar da su ba bisa ƙa'ida ba.
A cewarsa, sun gano wani rami da aka haƙa a ɗaya daga cikin haramtattun matatar mai wanda ke iya ɗaukan manyan motoci 10 maƙare da duro-duro na iskar gas inda kuma suke ajiye ɗanyan mai wanda daga nan kuma su riƙa shigar da shi wurin girke-girkensu.
Rear Admiral John Okeke ya ƙara da cewa za su ci gaba da kai irin wannan samame domin fatattakar masu fasa-ƙwabrin mai a yankin na Neja Delta.
Barka da Hantsi!
Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, assalamu alaikum. Da fatan mun wayi gari a wannan rana ta Litinin - tushen aiki, lafiya.
Kamar yadda muka saba, za mu kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.
Akwai shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Instagram inda a nan ma akwai ƙarin labaran da za ku iya karantawa har ma da bidiyo da za ku iya kalla.