Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 13 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Mun zo ƙarshen rahotonnin a wannan shafi.

    Sai kuma gobe za mu kawo muku wasu sababbin rahotonnin.

  2. Allon talla ya kashe mutum takwas a Indiya

    Aƙalla mutum takwas ne suka mutu sannan wasu 60 suka jikkata bayan wani allon talla ya faɗo a lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Mumbai na kasar Indiya.

    Jami’ai sun ce ruwan saman ya zo da iska mai karfi, lamarin da ya sa allunan tallan da ke kusa da wata hanya mai cunkoson jama’a a gabashin birnin Mumbai suka fado kan gidaje da wani famfon man fetur.

    Ana dai ci gaba da aikin ceto mutanen da suka makale.

  3. Gwmanatin Kano ta ƙaddamar da asibitin tafi da gidanka zagaye na biyu

    Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ƙaddamar da kashi na biyu na aikin kula da lafiyar al’umma a motocin tafi da gidanka.

    A ƙarshen shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar ta ɓullo da shirin farko na aikin a yankunan karkara musamman wuraren da suke da wahalar shiga.

    A cewar gwamnatin, wannan bangare ne na shirin farko wanda za a dinga zuwa hedikwatar karamar hukuma ana tara jama’a da zimmar duba lafiyarsu tare da ba su magani kyauta.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Zahraddeen Lawan daga Kanon:

  4. Tsohon lauyan Trump ya faɗa wa kotu sun haɗa baki wajen binne wasu labarai

    Tsohon lauyan Donald Trump, Micheal Cohen, ya shaida wa kotu a birnin New York cewa ya haɗa baki da tsohon mai gidan nasa domin binne labaran da ke da alamun cutar da yaƙin neman zabensa na 2016.

    Mista Trump ya musanta tuhumar da ake yi masa ta shirya ƙarya a bayanan kasuwanci don mayar wa Mista Cohen kudaden da ya biya tauraruwar fina-finan batsa Stormy Daniels don rufe mata baki kan alaƙar da ke tsakaninsu da tsohon shugaban kasan.

    Da yake jawabi a wajen kotun, Mista Trump ya ce "wannan shari’ar ba komai ba ce illa bi-ta da-ƙullin siyasa".

    Ya ce "wannan shari’ar ta Biden ce, katsalandan ne a harkar zaɓe a wani matakin da ba a taɓa gani ba a kasar nan, wannan abu ne da ake gani a ƙasashe masu tasowa ba a Amurka ba".

  5. Kotu ta zabtare ɗaurin shekara 24 da aka yi wa Mubarak Bala

    Kotun ɗaukaka ƙara a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sassauta hukuncin ɗaurin shekara 24 da aka yanke wa Mubarak Bala bisa laifin ɓatanci ga addinin Musulunci zuwa shekara biyar.

    A cewar lauyan Mubarak mai suna James Ibori, kotun ta ce hukuncin kotun na farko ya yi "tsauri" kuma "ya saɓa wa doka".

    Babu tabbas kan lokacin da za a saki Mubarak, wanda ke tsare a gidan yari shekara huɗu.

    Tun a 2020 aka kama shi bisa zargin yin ɓatanci ga addini a shafinsa na Facebook.

    Sai a 2022 aka ɗaure shi shekara 24 bayan ya amsa laifukansa.

  6. Za mu sake duba ƙarin kuɗin lantarki - gwamnatin Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake duba maganar ƙarin kuɗin lantarki da aka yi wa 'yan ajin Band A a watan da ya gabata sakamakon zanga-zangar da 'yan ƙungiyar ƙwadago suka gudanar a yau Litinin.

    Da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi a Abuja, babban sakatare a ma'aikatar lantarki Mamudah Mamman ya faɗa wa 'yan ƙwadagon cewa tuni majalisar ƙasa ta nemi gwamnati ta ƙara neman shawarar masu ruwa da tsaki kan ƙarin.

    A safiyar yau ne mambobin ƙungiyar ta NLC suka yi wa ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki tsinke a faɗin ƙasar, ciki har da Aedc na Abuja.

    "Abin da za mu yi shi ne komawa kan teburi, mu sake kallon abin, kuma mu ƙarƙare abin da ya fi dacewa. Ba ni da ikon janye ƙarin amma za mu koma fagen tattaunawa da hukumomi da kuma NLC," in ji shi kamar yadda TheCable ta ruwaito.

    Ya ƙara da cewa zan ɗauki saƙonku zuwa hukumomin da suka dace, kuma za mu duba mu kawo muku rahoto".

    A watan Afrilu ne hukumar Narc ta amince da ƙarin N225 kan kowane kwh ɗaya daga N66, kafin daga baya a rage shi zuwa N206.80.

  7. Tarayyar Turai ta yi tir da 'yansandan Georgia kan zanga-zanga

    Hukumar Tarayyar Turai (EU) ta yi Allahwadai da abin da ta kira ayyukan cin mutunci da barazana da cin zarafi da hukumomin Georgia ke yi wa masu zanga-zanga a ƙasar.

    Ta ce akwai buƙatar a binciki 'yansanda kan duk wani zargin cin zarafi da aka yi masu.

    A bara, Georgia ta samu kaiwa matsayin sharar fagen shiga kungiyar ta EU, amma 'yan'adawa na fargabar wani sabon kudirin doka na iya kawo mata cikas.

    Wakilyar BBC ta ce mutane na fargabar cewa dokar na iya danne muryoyin ƴan adawa a ƙasar Georgia amma babban abin da ke ci masu tuwo a ƙwarya shi ne dokar za ta iya sa a daƙile yunkurin ƙasar na shiga ƙugiyar ta EU.

  8. Sojoji sun kashe 'jagoran 'yanfashi Dogo Bangaje' a Kaduna

    Ma'aikatar tsaro ta gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce jami'an tsaro sun kashe wani jagoran 'yanfashin daji mai suna Dogo Bangaje tare da abokan aikinsa uku.

    Wata sanarwa da Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Punch ne suka yi nasarar kashe 'yanbindigar a ƙaramar hukumar Giwa.

    "Dakarun sun fara kai samame ƙauyen Tumburku da kuma Sabon Sara, inda suka kashe mutum biyu tare da ƙwace abubuwa da suka haɗa da babura, da wayar hannu, da sigari, da layoyi, da jakunkunan leda cike da man fetur," in ji kwamashinan.

    "An kai irin wannan hari a ƙauyen Basurfe, inda dakaru suka murƙushe 'yanfashin dajin da suka yi musu ƙofar rago kuma suka kashe biyu daga cikinsu. Daga baya kuma suka gano wani sansaninsu a cikin daji.

    "Daga cikin abubuwan da aka ƙwato akwai bindigar AK-47, da harba-ruga, da jakar harsasai 16, da rediyo biyu, da bam, da babur, da wayar hannu, da ƙwayoyi, da sigari, da sauran kayan kiwon lafiya."

    Aƙalla mutum 1,097 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilun da ya gabata - akasarinsu sakamakon hare-haren 'yanbindiga - a cewar wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting ya fitar a yau Litinin.

  9. NFF ta gabatar da Finidi George a matsayin kocin Najeriya

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta ƙaddamar da Finidi George a hukumance a matsayin kocin tawagar ƙasar ta Super Eagles na dindindin bayan sanar da sunansa a ƙarshen watan da ya gabata.

    Tsohon ɗan wasan na tawagar Super Eagles, da ma shi ne ke jan ragamar tawagar na riƙon-ƙwarya tun bayan da ɗan ƙasar Portugal Jose Piseiro ya ajiye aikin bayan kammala gasar Kofin Afirka a Ivory Coast.

    Da yake magana yayin gabatar da shi a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja, Ministan Wasanni John Enoh ya nemi NFF ta bai wa tsoohon ɗan wasan gefen dukkan taimakon da yake buƙata don ya yi nasara.

    "Abin alfahari ne gabatar da ni a matsayin kocin Super Eagles, godiya ta musamman ga NFF, da ma'aikatar wasanni, da kuma 'yan Najeriya da suka amince da ni," in ji Finidi cikin saƙon da ya wallafa a X.

    Ya ƙara da cewa "aikin babba ne amma da goyon bayan 'yan Najeriya za mu tsallake duk wani ƙalubale kuma mu sa ƙasarmu alfahari".

    Finidi zai fara wasansa da Afirka ta Kudu ranar 5 ga watan Yuni, sannan ya kara da Benin ranar 8 ga watan a wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya.

  10. Yaƙin Sudan: An kashe fararen hula 44 a Al-fasher - MSF

    Ƙungiyar bayar da agajin lafiya ta Medecins sans Frontieres ta ce har yanzu ana kan gwabza kazamin faɗa a birnin Al fasher da ke yankin Darfur yayin da Dakarun RSF ke ƙoƙarin ƙwace iko da birnin.

    Ƙungiyar ta ce ta tabbatar da mutuwar aƙalla fararen hula 44 tun bayan da RSF ɗin ta kai hari kan sojojin Sudan da mayaƙan sa-kai a ranar Juma'a.

    Ta yi kira ga ɓangarorin biyu da suka kwashe shekara guda suna yaƙi da su yi ƙoƙarin tabbatar da tsaron fararen hula.

    Wakilin BBC ya ce yaƙin basasar da ake yi a Sudan ya haifar da mummunar matsalar jin-ƙai, inda aƙalla mutum 13,000 suka mutu.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin al'ummar ƙasar na buƙatar agaji.

  11. An kashe mutum 1,097 a Najeriya cikin watan Afrilu - Rahoto

    Wani rahoto ya bayyana cewa yawan mutanen da aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilun 2024 ya zarce na watan Maris da ya gabace da kimani9n 34.4 cikin ɗari.

    Rahoton tsaron na wata-wata wanda kamfanin Beacon Consulting ke fitarwa ya nuna cewa a cikin watan na Afrilu an kashe mutum 1,097 yayin da a watan Maris aka kashe mutum 816.

    Hakan a cewar rahoton "abu ne mai ban tsaro", tare da bukatar hukumomi su ɗauki matakan da suka dace wajen daƙile matsalolin tsaron da ke haifar da irin waɗannan kashe-kashe.

    Jihar da aka fi kashe mutane a cikin watan na Afrilu ita ce Borno, inda aka kashe mutum 367, sai Zamfara mai biye mata a matsayi na biyu, inda aka kashe mutum 113, yayin da Kano ta zo a matsayi na uku, inda aka kashe mutum 64.

    Borno ce jihar da ta fi shan wahala sanadiyyar matsalar hare-haren ƴan ƙungiyar Boko Haram.

    Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta yi ƙoƙari wajen rage ayyukan mayaƙan na Boko Haram amma har yanzu akan samu hare-hare nan da can.

    Haka nan mayaƙan na Boko Haram kan dasa nakiyoyi a hanyoyin ababen hawa, wani abu da ke haifar da asarar rayuka.

    A ɓangaren garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa kuwa jihar Zamfara ce a gaba, inda aka yi garkuwa da mutum 122, sai Borno a matsayi na biyu, inda aka yi garkuwa da mutum 40, yayin da jihar Delta take a matsayi na uku, inda aka sace mutum 29.

    Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

    Ƴan bindigan na kai hare-hare a ƙauyuka, inda suke satar dukiya da mutane domin neman kuɗin fansa.

    Duk da cewa gwamnati na cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar amma har yanzu matsalar na ci gaba da haifar da asarar rayuka da tagayyara al'umma a faɗin jihohin arewa maso yammacin ƙasar.

    Rahoton ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutum 311 yayin da aka raunata mutum 342 a cikin watan na Afrilu a faɗin Najeriya.

    Sai dai a ɓangare guda rahoton ya ce an samu raguwar yawan kai hare-hare da kuma sace-sacen al'umma domin neman kuɗin fansa.

  12. Yawan kayan da ake fitarwa a Najeriya ya ragu da kashi 166 – Bankin Duniya

    Kuɗaɗen shiga da Najeriya ke samu daga bangaren masana'antu na fitar da kayayyaki ya ragu da kashi 166 cikin 100 zuwa naira 778.4bn daga adadin da ya kai naira tiriliyan 2.2 a shekarar 2019.

    Tun daga shekarar 2019, yanayin ya koma ƙasa, tare da raguwa sosai zuwa naira 960.7 biliyan a cikin 2020 saboda cutar COVID-19 yayin da aka samu murmurewa a shekarar 2021 a kan naira triliyan 1.15 inda a shekarar 2022 kuma aka sami raguwa mai yawa zuwa naira biliyan 781.1 kuma raguwar naira biliyan 778.4 a 2023.

    Babban bankin ya dora alhakin raguwar kasuwancin ketare a kasar kan rashin kyawun ababen more rayuwa da kuma rashin ingantaccen kayan aiki da dai sauransu.

    Rahoton ya ce kuɗin da ake samu daga kasuwanci a Najeriya da Habasha ya ninka wanda ake samu a Amurka sau hudu zuwa biyar saboda rashin tsaro da tsadar sufuri da yanayin kasa da kuma rashin ingancin hanyoyi.

    “Nazari daga yankin Afirka a koyaushe yana samun bambance-bambance a cikin farashin kayayyakin da ake shigowa da su na kayan abinci da wanda baabinci ba da kuma kayan amfanin gona da kuma farashin dillalan kayayyaki.

    "Misali, farashin ciniki ya ninka sau hudu zuwa biyar a Habasha da Najeriya fiye da na Amurka, saboda rashin kyawun ababen more rayuwa da karancin gasa a fannin sufuri, da kuma yanayin kasa," in ji rahoton.

    Rahoton ya kuma kara da cewa, illar wadannan ƙalubalen, sun hada da fifita masana'antun Afirka su sayar da kayyayaki a cikin gida maimakon fitar da su zuwa kasashen waje.

    Masu masana'antu da masu gudanar da ayyukan fitar da kayayyaki sun koka kan yadda yanayin kasuwanci a kasar ya yi kamari yana sa kayayyakin cikin gida ba su da gasa a duniya.

    Rahoton na bankin ya zo ne bayan da hukumar bunkasa fitar da kayayyaki ta Najeriya (NEPC), ta bukaci masu fitar da kayayyaki daga Najeriya su bi ka’idojin fitar da kayayyaki zuwa kasashe daban-daban.

  13. Ɗalibar da 'aka ci zalinta' a makarantar Leads British na neman diyyar naira miliyan 500

    Wata ɗaliba a Najeriya ta maka hukumomin makarantar Lead British a kotu bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda ake 'cin zalin ta' ya yaɗu a intanet.

    Lauyoyin Namitra Bwala sun ce makarantar ta Lead British da ke Abuja, babban birnin ƙasar ta gaza samar da ingataccen yanayin karatu.

    Ta buƙaci makarantar da ta nemi afuwa a bayyane kuma ta biya ta diyyar naira miliyan 500, kwatankwacin dalar Amurka 350,000.

    Bidiyon da ke nuna yadda wata ɗaliba ke zazzabga mata mari ya karaɗe shafukan sada zumunta a farkon wannan wata na Mayu.

    Makarantar ta ce tana yin bincike kan lamarin kuma tana fatan ɗalibar za ta koma aji domin ci gaba da karatu.

  14. Vladimir Putin ya sake wa ministan tsaronsa muƙami

    Shugaban Rasha, Vladimir Putin zai cire daɗaɗɗen abokinsa, Sergei Shoigu daga matsayin ministan tsaro, kamar yadda Kremlin ta sanar.

    Mista Sargei mai shekaru 68 dai ya dade a kan muƙamin tun 2012 inda yanzu kuma za a maye gurbinsa da mataimakin firaiminista, Andrei Belousov - masanin tattalin arziki wanda kuma yake da 'yar fahimta a soji.

    Za a naɗ mista Shoigu a matsayin sakataren Majalisar Tsaron Rashar.

    Rasha ta ce ma'aikatar tsaron ƙasar na buƙatar zama "mai ƙirƙira".

    Ba dai kasafai ake samun sauye-sauyen muƙamai ba, a saboda haka wannan babban abu ne a siyasar Rasha.

    To sai dai Vladimir Putin ya kasance mutumin da shi kaɗai ke tsara yadda za a tafiyar da al'amura. Shi ne ya yanke shawarar fara yaƙi a Ukraine da ma duk wasu manya-manyan abubuwa.

    Naɗin mista Belousov a matsayin ministan tsaro ka iya zuwa da bazata ga mutane da dama, idan aka yi la'akari da gogewarsa.

    To sai dai masu sharhi na ganin shugaba Putin na ƙoƙarin daidaita tattalin arzikin Rasha da yaƙin da ƙasar ke yi.

  15. Firaiministan Chadi ya nemi a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa

    Firaiministan Chadi Succes Masra ya shigar da ƙara a majalisar tsarin mulkin ƙasar inda yake ƙalubalantar sakamakon farko na zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ƙasar a makon da ya gabata.

    An ayyana Janar Mahamat Deby a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da kashi 61 cikin 100 na ƙuri'un da aka jefa amma Mista Masra na iƙirarin shi ne ya lashe zaɓen.

    "Da taimakon lauyoyinmu, a yau, mun miƙa buƙata ga majalisar tsarin mulkin ƙasa da ta bayyana sakamakon gaskiya," kamar yadda Mista Masra ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

    Ɗan hamayyar da jam'iyyarsa ta Transformer sun nemi a soke sakamakon inda ta yi zargin an yi cushe a akwatunan zaɓen sannan sojoji sun ɗauke wasu domin ƙirga ƙuri'u a wasu wuraren.

    An kama wasu ƴan ɓangaren hamayya yayin da Mista Masra da magoyta bayansa ake masu barazana, in ji jam'iyyar.

    Sai dai Mista Masra ya nanata cewa magoya bayansa mutane ne masu son zaman lafiya yana mai cewa sauyin da kuke son gani, ba zai faru ba a ƙasar da ta lalace.

    Jim kaɗan kafin bayyana sakamakon zaɓen, Mista Masra ya yi kira ga magoya bayansa da su gudanar da zanga-zanga domin kare ƙuri'unsu.

  16. Ƙazamin rikici na ƙara janyo asarar rayuka a Sudan

    Aƙalla mutum 16 ne suka mtu sakamakon ƙazamin rikici a El Fasher da ke Sudan ranar Lahadi, a cewar ƙungiyar likitoci ta Doctors without Borders, sai kuma wasu 114 da suka ji rauni.

    Ƙungiyar ta ce adadin ya ƙara yawan mutanen da suka mutu da ta san da mutuwarsu a birnin cikin kwana uku da suka gabata zuwa 44.

    Rikici ya tsananta tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, da ta mamaye El Fasher tun Juma'ar da ta gabata.

    Shi ne babban birnin da ya rage a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar da har yanzu ke ƙarƙashin ikon sojojin Sudan bayan fiye da shekara ɗaya da ɓarkewar yaƙin basasa a ƙasar.

    A ƙarshen mako MSF ta ba da rahoton cewa an tilasta rufe wani asibitin yara da take tallafawa lokacin da wani hari na sojojin Sudan ya faɗa a kusa da wurin lamarin da ya halaka yara biyu da ke samun kulawa a sashen gaggawa na asibitin.

    MSF ta sami rahoton mutum 290 da suka ji rauni a jumulla a wani asibitin a ranar Juma'a.

    Jami'an MSF da Majalisar Ɗinkin Duniya, sun shafe makonni suna cewa ta'azzarar rikici na barazana ga gomman farar hula a El Fasher, galibinsu sun ɗaiɗaita sakamakon yaƙin da aka yi a wani garin, sannan Amurka na gargaɗi kan gagarumin kisan kiyashin da aka yi.

    MSF ta yi kira ga bangarorin biyu da su tabbatar wa farar hula da cibiyoyin kula da lafiya kariya.

  17. Dalilan da suka sa Nijar ke ɗari-ɗari da jamhuriyar Benin

  18. Ana bincike kan mutuwar jami'in kwastam da ake zargin ya kashe kansa a Kano

    Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fara gudanar da cikakken bincike kan mumunan al’amuran da suka faru dangane da mutuwar jami’in kwastam da aka ce ya kashe kan shi ta hanyar harbin kansa da bindiga da kuma mutuwar wasu matasa biyu a rikicin baya-bayan nan da aka yi a unguwar Darmanawa da ke Kano.

    Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya fitar ta hannun jami’in hulda da jama’a na runduna, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

    Abubuwan da suka faru a lokuta daban-daban, sun haifar da damuwa a cikin al'umma inda aka dauki matakin gaggawa daga jami'an tsaro.

    "Tun da farko dai, kisan kai na jami’in kwastam CSC Abdullahi Abdulwahab Magaji ya haifar da tambayoyi, lamarin da ya sa ‘yan sandan gudanar da bincike mai zurfi." in ji sanarwar.

    A wani ɓangare kuma, wani rikici da ya samo asali daga wani taron Gangi da Muhammad Barde ya shirya domin bikin auren ‘ya’yansa ya rikide zuwa tashin hankali, ya yi sanadin jikkata mutane da kuma hasarar rayukan mutum biyu in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ‘yan sandan ta cafke Barde da wasu mutum biyu da ake zargi.

    Ta kuma ce yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula, rundunar ‘yan sandan Kano ta sha alwashin ba za ta bar wani abu ba wajen bankado al’amuran da suka haddasa wadannan munanan lamura.

    "Asarar rayuka da suka hada da na Sadiq Abdulkadir da Muhammad Sani ya jefa al’umma cikin duhu, lamarin da ya sa ake kira da a gaggauta yin shari’a tare da gudanar da cikakken bincike."

    Sanarwar ta ce a halin yanzu dai 'yan sanda na gudanar da cikakken bincike kan al'amuran biyu wanda za a bayyana cikakkun bayanansu ga bainar jama'a.

    Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tana ci gaba da jajircewa wajen ganin ta tabbatar da bin doka da oda da kuma tabbatar da tsaro da tsaron dukkan mazauna yankin.

  19. Buɗe makarantu a Kenya a yanayin ruwan sama mai ƙarfi ya janyo taƙaddama

    Bayan tsaikon da aka samu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa, an sake buɗe makarantu da dama a Kenya.

    Sakamakon haka ne aka tura jami’an ‘yan sanda da na sufuri domin tabbatar da cewa dalibai sun shiga aji cikin aminci.

    Hukumomin kasar sun bayyana cewa sama da makarantu 1,600 na iya kasancewa a rufe sakamakon ambaliyar ruwa da ake fama da ita, tare da jaddada tsananin halin da ake ciki.

    Shuwagabannin musulmi sun bayyana damuwarsu dangane da lafiyar daliban, inda suka yi kira da a sanya ido sosai kan lamarin da kuma yanayin.

    Suna kuma yi kira ga direbobi da su sanya ido sosai kan hanyoyin da ambaliyar ruwa ta shafa.

    Makarantu da dama ne ambaliyar ruwa ta lalata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 250 a fadin Kenya.

    Ya kamata dai a bude makarantu tun a ranar 29 ga watan Afrilu kafin sabon wa'adin ya koma baya.

    Tun da farko an tsara buɗe makaranta a ranar 29 ga Afrilu, amma aka jinkirta saboda tsananin yanayin yanayi.

  20. NLC da TUC a Osun sun bi sahun zanga-zangar ƙarin kuɗin wuta