Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/5/2024.
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi, A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Abdulahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Ambaliya ta kashe mutum 50 a Afghanistan
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Baghlan province is prone to flooding
Jami'an Taliban sun ce aƙalla mutum 50 ne suka mutu, wasu fiye da 100 suka jikkata sakamakon mummunar ambaliya da ta auka wa arewacin Afghanistan
Mai magana da yawun ƙungiyar, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fuskanta a gundumomin biyar da ke lardin Baghlan, inda ya yi gargaɗin hasashen samun iska mai ƙarfi a cikin dare.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya riƙa yin toroƙo tare da tafiya da gidaje a ƙauyukan da dama, da kuma lalata wasu da dama.
A 'yan makonnin nan ƙasar na fuskantar mamakon ruwan sama da ke haddasa ambaliya ruwar, lamarin da ya yi sanadin kisan kusan mutum 100 tun tsakiyar watan Afrilu.
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida na ƙasar, Abdul Mateen Qaniee, ya ce fiye da mutum 150 ne suka maƙale a cikin ambaliyar, waɗanda kuma ya ce suna buƙatar taimakon gaggawa.
Mista Qaniee ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa tuni aka tura jirage masu saukar ungulu zuwa lardin na Baghlan da ke arewacin Kabul, babban birnin ƙasa.
To sai dai ya ce ''aikin ceton zai gamu da tasgaro'' saboda rashin hasken da za a yi amfani da shi don gano mutanen idan dare ya yi.
Wani jami'in gwamnatin ƙasar mai suna, Hedayatullah Hamdard ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an tura tawagar ma'aikatan agaji ciki har da sojoji domin ''ceto mutanen da suka maƙale cikin ruwa da turɓaya''.
Hukumomin ƙasar sun ce tuni suka tanadi tantuna da barguna da abinci ga iyalan da suka rasa gidajensu.
Kotu ta dakatar da 'yan majalisar dokokin Rivers 25 da ke biyayya ga Wike
Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT PRESS
Wata babbar kotu a birnin Fatakwal na jihar Rivers ta hana mambobin majalisar dokokin jihar 25 ayyana kansu a matsayin 'yan majalisar dokokin.
Yayin da yake zartar da hukuncin ranar Juma'a, Mai shari'a Charles N. Wali ya ce kotun ta ƙwace kujerun 'yan majalisun
'Yan majalisar 25 ciki har da kakakin majalisar jihar, Martin Amaewhule, da hukuncin ya shafa, masu biyayya ne ga tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike, wanda a yanzu shi ne ministan birnin tarayya Abuja.
'Yan majalisun dai sun fice daga jam'iyyar PDP mai mulkin jihar zuwa APC, a lokacin da dangantaka ta yi tsamin tsakanin Nyesom Wike da gwamnan jihar Siminalayi Fubara.
Bayan ficewarsu daga jam'iyyar ne majalisar jihar ta ce da kore su daga muƙamansu na 'yan majalisar.
Don haka kotun ta ce ta dakatar da 'yan majalisar daga halartar zaman majalisar dokokin jihar da ke birnin Fatakwal, ko duk wani wuri da majalisar ta zaɓi ta zauna don gudanar da harkokinta.
Jihar Rivers dai ta faɗa rikicin siyasa, tun bayan da aka fara samun takun saƙa tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da tsohon gwamna Nyesom Wike, kodayake daga baya gwamnatin tarayya ta shiga tsakani inda ta yi musu sulhu.
Bai kamata mu bari 'yan ta'adda su gagare mu ba – Sultan
Asalin hoton, Getty Images
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhamma Sa'ad Abubakar na uku ya shawarci 'yan Najeriya da su fahimci ƙalubalen da ke gabansu domin tunkarar su.
Sultan ɗin dai ya faɗi hakan ne yayin wata ziyara da ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru ya kai masa a fadarsa a yau Juma'a.
"Bai kamata mu bari wani ya samu galaba a kanmu ba. Ministan tsaro ya san irin girman alhakin da ke rataye a wuyansa. Na kuma yi amannar cewa yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin su taimaka masa . Muna aiki tare kuma ba za mu daina ba.
Sarkin na Musulmi ya jaddada cewa sarakan gargajiya za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya ya ɗore a ƙasar.
To sai dai Sultan ɗin ya nemi goyon bayan al'umma ga jami'an tsaron Najeriya waɗanda ya ce suna jefa rayuwarsu cikin haɗari saboda kare ƙasa.
'Yan bindiga sun kashe mutum 30 a sabbin hare-haren da suka kai Zamfara
Asalin hoton, others
'Yan bindiga a jihar Zamfara sun ƙaddamar da munanan hare-hare a jihar Zamfara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 30 ciki har da wani fitaccen malamin addini.
An kai hare-haren a ranar Alhamis a ƙauyukan Gidangoga a yankin ƙaramar hukumar Maradun da Bilbis a yankin ƙaramar hukumar Tsafe.
Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa da farko 'yan bindigar sun fara kai hari garin ƙauyen Gidangog ne kan wasu manoma da ke aikin share gonakinsu, a shirye-shiryen da suke yi na tunkarar daminar bana.
''A harin ne kuma 'yan bindigar suka kashe Mallam Makwashi Maradun Mai Jan Baki, fitaccen malamin addinin Musulunci a gonarsa'', in ji jaridar.
Mallam Makwashi, shi ne mai jan baƙi a tafsirin da ake gabatarwa a masallacin Juma'a na Maradun.
Haka kuma da maraice 'yan bindigar suka ƙaddamar da wani mummunan harin a garin Bilbis na yanƙin ƙaramar hukumar Tsafe, tare da kisan aƙalla mutum 20.
Hare-haren sun jefa al'ummar yankin cikin zulumi da fargaba.
Jihar Zamafar da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalolin 'yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.
MDD ta yi kira ga 'yan siyasar Chadi su kai zuciya nesa
Asalin hoton, MICHEL MVONDO/BBC
Wakilin Sakataren Majalisar Dinkin Duniya na yankin tsakiyar Afirka, Abdou Abarry, ya yi kira ga 'yan siyasar Chadi su kai zuciya nesa, bayan ayyana shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar, Mahamat Deby a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.
Kiran MDD na zuwa ne a daidai lokacin da babban abokin hamayyar Deby, Success Masra ya yi zargi jirkita sakamakon zaɓen.
Abdou Abarry ya yi kira ga 'yan siyasar ƙasar su rungumi hanyoyin tattaunawa da shari'a wajen magance duk wani abu na saɓani.
Tuni dai Firaministan ƙasar, Success Masra - wanda ya zo na biyu a zaɓen - ya yi kira ga magoya bayansa su gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaɓen.
Wata fitattciyar ƙungiyar farar hula ma a ƙasar ta yi kira ga jama'ar ƙasar su yi watsi da nasarar Deby, matakin da ka iya zama mai hatsari.
Shekaru biyu da suka gabata an kashe gomman masu zanga-zangar da suka fantsama kan titunan ƙasar don nuna adawarsu da tsawaita wa'adin gudanar da zaɓe da Deby ya yi.
Tuni dai hukumomin ƙasar suka jibge tarin jami'an tsaro a N’Djamena babban birnin ƙasar.
'Za a kammala kashin farko na aikin layin dogon Kano zuwa Maraɗi a 2025'
Asalin hoton, Google
Ministan sufuri na Najeriya Sanata Sa'idu Alƙali ya ce za a kammalakashi na farko na aikin layin dogo da ya tashi daga Kano zuwa Maraɗi mai nisan kilomita 387 a shekarar 2025.
Sanata Alƙali ya bayyana hakan ne a lokacin da yake duba aikin layin shimfiɗa layin dogo na zamani da ake yi tsakanin Kano zuwa Maraɗi da na Kano zuwa Kaduna.
Ministan ya ce wannan shi ne karo na biyu da yake zuwa duba aikin a Kano, tun bayan da aka naɗa shi ministan.
Gwamnatin da ta gabata ce dai ta bayar da aikin gina titin layin dogo daga Abuja zuwa Kano da na Kano zuwa Maraɗi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Yadda ziyarar Yarima Harry ke kasancewa a Kaduna
Bayanan bidiyo, ..
Ɗan majalisar tarayya Isa Dogonyaro daga Jigawa ya rasu
Asalin hoton, Yahaya Bala Haruna/Facebook
Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Garki da Babura daga jihar Jigawa ya rasu.
Cikin wata sanarwar da abokin aikin ɗan majalisar, Mohammed Bello El-Rufa’i daga jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce Isa Dogonyaro ya rasu da safiyar yau Juma'a.
Ɗan majalisar mai shekara 46, ya rasu ne sakamakon wata gajeriyar jinya, kamar yadda kafofinj yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.
Isa Dogonyaro na jam'iyyar APC ya kasance mataimakin shugaban kwamitin yaƙi da cutuka na majalisar wakilan ƙasar.
Babban Zauren MDD ya nemi Kwamitin Sulhu ya amince da ƙasar Falasɗinu
Asalin hoton, Reuters
Babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi ƙira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya tabbatar da 'yancin Falasɗinawa ta hanyar amincewa da kasar a matsayin mamba a majalisar.
Falasɗinu dai na da matsayin ƙasa 'yar sa ido tun shekarar 2012, wani abu da ke nuna rashin cikakken 'yancinta na kasancewarta ƙasa mai 'yancin a zauren.
Kwamitin Tsaro na Majalisar ta Dinkin Duniya ne kawai yake da damar tabbatar da hakan.
Amurka za ta hau kujerar naƙi dangane da zaman Falasɗinu samun matsayin zaman cikakkiyar mamba a kwmaitin.
To sai dai zaɓen na ranar Juma'a ya nuna irin goyon bayan da ake nuna wa ƙasar Falasɗinawa.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Turai ke ƙoƙarin amincewa da ƙasar Falaɗinawa.
Hotunan ziyarar Yarima Harry zuwa Kaduna
Bayanan hoto, Yariman ya samu tarbar gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani a gidan gwamnatin jihar
Bayanan hoto, Gwamnan Kadunan ya bai wa Yariman Birtaniyar kyautar hula
Bayanan hoto, Yarima Harry lokacin da gwamnan Kaduna ya ya ba shi kyautar babbar riga
Bayanan hoto, An shirya kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin nuna tarba da yariman na Birtaniya
Bayanan hoto, Kayayyakin kade-kaɗen gargajiya da aka tarbi yariman da su
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani tare da muƙarrabansa lokacin da suke karɓar baƙuncin yariman
Lupus: Cutar garkuwar jiki da ake gano ƙarin masu fama da ita a Najeriya
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
A shekarun baya-bayan nan, ana gano ƙarin mutanen da ke fama da cutar lupus a Najeriya.
Ƙwararru a fannin lafiya kamar Dr. Maryam Ahmed, likitar gaɓoɓin jiki a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, na cewa duk da yake ana gano ƙarin masu cutar amma ba lallai ne a ce tana ƙara yawa ba.
Hukumomin lafiya a duniya sun keɓe duk ranar 10 ga watan Mayun kowacce shekara domin tunawa da masu fama da lupus.
Lupus cuta ce wadda garkuwar jikin mutum maimakon ta yi aikinta na kare jiki daga miyagun ƙwayoyin cutuka, amma cikin kuskure sai ta juya ta riƙa nakasa lafiyayyun ƙwayoyin halittun jiki.
Masu cutar lupus kan yi fama da tsananin mutuwar jiki da yawan larurori sanadin alamomin cutar a sassan jiki.
Ƙwararru dai sun ce har yanzu ba a iya gano takamaimai abin da ke haddasa cutar lupus ba.
Sai dai, sun ce mai yiwuwa tana da nasaba da ƙwayoyin halittun gado kuma tana addabar sassan jikin da suka fi fitowa cikin hasken rana kamar; kai da fuska da hannuwa da fatar jiki.
Kalli bidiyon da ke sama domin ganin likita Maryam Ahmed da ƙarin bayani game da cutar lupus.
Ukraine ta ce ta daƙile shirin Rasha na kutsawa cikin ƙasarta
Asalin hoton, REUTERS/Vyacheslav Madiyevskyy
Ukraine ta ce ta daƙile wani harin Rasha mai kunshe da sojoji da tankokin yaƙi a arewa maso gabashin Kharkiv region, bayan dakarun Rashar sun ƙaddamar da wani kutse a kan iyakar ƙasar bisa tunanin karya tsaron iyakar.
Shugaban lardin na Kharkiv, Oleh Syniehubov ya ce shawagin da dakarun Rasha suka yi a ƙoƙarinsu na kutsawa iyakar ƙasar, sai dai kuma 'ba su iya tsallakawa ko da mita ɗaya ba.'
"Rasha ta ƙaddamar da sabbin jerin hare-hare a Kharkiv," in ji shugaban Ukraine, Volodomyr Zelensky.
Da ma dai dakarun Ukraine sun daɗ suna tsammanin faruwar hare-hare a lokacin bazara, watakila ma na ƙaƙarin kame birnin Kharkiv. Sai dai jami'an ƙasar sun nuna halin ko-in-kula bisa tunanin hakan ba zai yiwu ba.
Ziyarar Yarima Harry da mai ɗakinsa Meghan a Najeriya
Bayanan bidiyo, Babban maƙasudin ziyarar ta kwana uku shi ne domin halartar bukukuwan cika shekara 10 da samar da wasannin ‘Invictus Games’ – na sojojin da aka raunata a fagen daga.
'Yan bindiga sun sace ɗaliban jami'a da dama a jihar Kogi
Asalin hoton, Confluence University
Wasu 'yan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da ɗaliban jami'a tara a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.
Sai dai ana fargabar adadin zai iya zarta hakan.
Rahotonni sun ce maharan sun dirar wa jami'ar Confluence University of Science and Technology ne da ke Osara–Okene da tsakar dare ranar Alhamis.
Bayan sun isa ne kuma suka dinga shiga ɗakunan ɗaliban da ke karatu domin shirya wa jarabawar da ke tafe kuma suka buɗe wuta a sama, suka tara wasu ɗalibai kuma suka wuce da su.
"Ɗaruruwan dakarun sa-kai da suka san dazuka da kuma jami'an tsaro yanzu haka na kewaya yankin don ceto ɗaliban salin'alin," a cewar wata sanarwa da kakakin gwamnatin jihar Kingsley Fanwo ya fitar.
A farkon makon nan ne gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar - inda aka yi sace-sacen ɗalibai da yawa a baya-bayan - ta ce za ta sauya wa makarantu sama da 300 wuri saboda barazanar 'yan bindigar.
Baya ba ta da kaɗan...Harry da Meghan sun isa hedikwatar tsaron Najeriya
Yarima Harry da mai ɗakinsa Meghan sun isa hedikwatar tsaro ta Najeriya a cigaba da ziyarar aiki da suka kai ƙasar da ke yammacin Afirka.
Mrs Oghogho Musa - shugabar ƙungiyar mata ta jami'an tasron 'yansanda da soja a Najeriya - ita ce ke jagorantar tawagar tarɓar 'yan gidan sarautar ta Birtaniya a Abuja.
Ana ci gaba da dakon isowar Harry da Meghan wurin taro
Yarima Harry da mai ɗakinsa Meghan sun isa Najeriya a yau Juma'a, inda za su ziyarci biranen Abuja da Kaduna da kuma Legas.
Sai dai har yanzu ba su isa hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriya ba, inda za a yi ƙwarya-ƙwaryar bikin tarɓarsu.
Mrs Oghogho Musa - shugabar ƙungiyar mata ta jami'an tasron 'yansanda da soja a Najeriya - ita ce ke jagorantar tawagar tarɓar 'yan gidan sarautar ta Birtaniya a Abuja.
Mutane sun tsinci naman ɓera cikin Burodi a Japan
Asalin hoton, PASCO SHIKISHIMA CORPORATION
Ɗaya daga cikin manyan gidajen burodi mafi shahara a Japan na ƙoƙarin dawo da dubban sunƙin burodin da ya sayar tare da mayar wa waɗanda suka saya kuɗinsu bayan an tsinci wani ɓangare na jikin ɓera a wasu burodin da ya sayar.
Kimanin burodi sunƙi 104,000 na gidan burodin Pasco Shikishima ne aka cire daga kantuna sanadiyyar al'amarin.
An ga wani ɓangare na jikin ɓera a cikin ƙunshin burodi aƙalla biyu.
Akasarin iyalai a Japan na amfani da burodin na kamfanin Pasco, sannan burodi ne da ake iya gani a kusan kowane kanti da ke faɗin ƙasar.
Ya zuwa yanzu dai babu rahoton wani da za a ce ya kamu da rashin lafiya sanadiyyar cin burodin, kamar yadda kamfanin burodin ya sanar.
Kamfanin ya ce "Muna neman afuwar al'umma sanadiyyar damuwar da hakan ya haifar ga masu hulɗa da mu da abokan kasuwancinmu da duk waɗanda lamarin ya shafa."
Pasco bai bayyana yadda aka yi har wani ɓangare na jikin ɓera ya shiga cikin burodin ba amma "ya sha alwashi tsaurara matakan kiyaye tsafta domin ganin cewa ba a sake samun irin hakan ba a gaba."
Tuni kamfanin ya samar da wata hanyar da mutanen da lamarin ya shafa za su iya neman a biya su kuɗinsu ta hanyar shafin intanet.
Ba a cikin Japan kawai ba, ana fitar da kayan da kamfanin na Pasco ke sarrafawa zuwa ƙasashen Amurka da China da Australiya da Singapore da ma wasu da dama.
Sojoji sun miƙa ƴar Chibok da ƴaƴanta uku ga gwamnatin Borno
Asalin hoton, Nigeria Army/X
Rundunar sojin Najeriya ƙarƙashin rundunar Operation Haɗin Kai ta miƙa ƴar makarantar Chibok, Lydia Simon da aka kuɓutar daga hannun ƴan bindiga tare da ƴaƴanta uku ga gwamnatin jihar Borno.
Kaftin Mai riƙon muƙamin mataimakin daraktan yaɗa labarai na hedikwatar rundunar, Reuben Kovangiya, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar na X.
Da yake ba da bayanin yadda aka ceto ta, Birgediya Janar Abubakar Haruna ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun yi nasarar yin hakan ne ranar 17 ga watan Afrilun 2024 a ƙaramar hukumar Gwoza sakamakon cigaba da datse mashigar Mandara da sojojin ke yi.
Yayin bikin miƙa su, kwamandan rundunar Manjo Janar Waidi Shaibu ya yi ƙarin bayani kan yadda sace ƴan matan a 2014 ya janyo gagarumar suka har m aka kafa ƙungiyar da ke rajin gano ɗaliban ta Bring Back Our Girls.
Janar Shaibu ya sake tabbatar da ƙudirin rundunar na ci gaba da kuɓutar da waɗanda ke hannun ƴan bindiga.
Kotu za ta saurari ƙara kan cancantar Zuma ya tsaya takara
Asalin hoton, AFP
Kotun ƙolin Afirka ta Kudu na shirin sauraron ƙara kan ko tsohon shugaban kasar Jacob Zuma zai iya tsayawa takara a zaɓen da aka yi hasashen za a yi nan ba da jimawa ba.
Zuma, mai shekaru 82, ya jagoranci sabuwar jam'iyyar adawa ta uMkhonto we Sizwe (MK) jam'iyyar wadda masu sharhi ke ganin ka iya kawo cikas ga sakamakon babban zaɓen da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.
Wata ƙaramar kotu a watan Afrilu ta ce Zuma na da 'yancin tsayawa takara bayan da hukumar zaɓe ta hana shi a kan cin zarafin kotu.
Ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar ya hana mutane riƙe muƙaman gwamnati idan aka same su da laifi kuma aka yanke masu hukuncin ɗaurin fiye da watanni 12 a gidan yari.
An yanke wa Zuma hukuncin ɗaurin watanni 15 a gidan yari ne a shekara ta 2021 saboda ya kasa bayar da shaida kan binciken cin hanci da rashawa, ko da yake ya shafe watanni uku kacal saboda dalilai na lafiya.