Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/5/2024.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza

  1. Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga da lalata mafakarsu a Kaduna

    Dakarun sojojin Najeriya da aka tura domin yaki da ta'addanci a jihar Kaduna sun kashe wasu ƴan bindiga tare da dakile ayyukansu a karamar hukumar Giwa da ke jihar.

    A wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumuntata na X, rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kai farmakin ne a sansanin ƴan bindiga da ke kauyen Basurfe da ke kudu maso yammacin Kidandan, bayan da wasu bayanan sirri suka tabbatar da cewa wasu 'ƴan ta'adda' na amfani da ƙauyen a matsayin mafakar gudanar da ayyukansu.

    Sanarwar ta ƙara da cewa a yayin da sojoji suka tunkari ƙauyen, ƴan bindigan sun yi musu kwanton-ɓauna amma sojojin sun yi nasarar tarwatsa su

    A yayin zazzafar arangama ne sojojin suka hango wasu daga cikin 'ƴan ta'addar' suna yunkurin tserewa daga yankin a kan babura, inda suka yi nasarar fatattakar su tare da kashe mutum biyu daga cikin su - in ji sanarwar.

    Sojojin sun kuma ƙwace makamai da dama har da babura guda biyu.

  2. Me ya sa iyalan masarautar Birtaniya ke ziyara a Najeriya?

  3. EFCC ta kama wasu mutum 39 da ake zargi da damfarar Intanet a birnin Benin

    Jami’an shiyyar Benin na Hukumar yaƙida cin hanci da rashawa, EFCC sun kama mutum 39 da ake zargi da damfara ta intanet a wurare daban-daban a cikin birnin Benin.

    An kama wadanda ake zargin ne biyo bayan samun bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na damfara ta hanyar amfani da kwamfuta.

    Kayayyakin da aka ƙwace daga hannunsu sun haɗa da wasu manyan motoci guda takwas, kwamfutar tafi-da-gidanka da wayoyi, za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

    Hakazalika kuma, a jihar Akwa Ibom, Jami’an EFCC sun kama mutum 21 suma da zargin damfara ta intanet a Uyo.

  4. Netanyahu ya sha alwashin kakkaɓe Hamas duk da barazanar Amurka

    Firaminstan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya lashi takobin cewa Isra’ila za ta iya “tsayawa ita kadai”, bayan da Amurka ta yi gargadin cewa za a iya dakatar da jigilar makamai idan Isra'ila ta ba da umarnin kai farmaki a Rafah dake Gaza.

    Dubban mutane ne dai suka tsere daga kudancin birnin bayan da sojojin Isra'ila suka fara wani farmaki a ranar Litinin.

    Shugaban Amurka Joe Biden ya sha yin gargadi game da wannan farmakin, yana mai cewa zaiiyahaifar da mummunan sakamako.

    Sai dai Netanyahu ya yi watsi da gargadin na Amurka, yana mai cewa Isra'ila za ta ci gaba da yaƙar Hamas.

    "Idan akwai buƙata, za mu tsaya mu kaɗai domin kawar da Hamas" in ji Netanyahu.

  5. An fara tattaunawar zaman lafiya a Sudan ta Kudu a Nairobi

    An fara tattaunawar zaman lafiya a Nairobi tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu da kuma 'yan adawar 'yan tawaye da ba sa cikin yarjejeniyar 2018.

    Muhimman batutuwa, kamar rundunonin tsaro na hadin gwiwa, har yanzu ba a warware su ba.

    'Yan adawar dai sun yi kira da a gudanar da tattaunawa kafin zaben na watan Disamba domin gudanar da sahihin zabe.

    Shugabannin kasashen Afirka da suka halarta ciki har da shugaba Sudan ta Kudu, Salva Kiir, sun jaddada kawo karshen rikicin da ke durkusar da tattalin arzikin ƙasar.

    Shugaban kasar Kenya William Ruto ya jaddada shiga tsakani na bai daya domin samun mafita a cikin gida, tare da yin daidai da shirin ''Silencing the Bins in Africa''.

    Shugaba Kiir ya bayyana fatan samun sakamako mai kyau gabanin zaben, yana mai kira ga dukkan bangarorin da su ba da fifiko ga zaman lafiya domin dorewar kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki.

  6. Tsare Daniel Ojukwu barazana ne ga ƴancin aikin jarida a Najeriya – HRW

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta ce tsare ɗan jaridar nan a Najeriya, Daniel Ojukwu ya take ƴancinsa a matsayin mai bayar da rahoto.

    Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar wadda ta aike wa kafafen yaɗa labarai a Najeriya.

    HRW ta nemi hukumomin Najeriya su gaggauta sakin Ojukwu idan ba a tuhume shi da aikata babban laifi ba.

    A cewar ƙungiyar, ƴan jarida da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama a Najeriya na zanga-zanga kan kama Daniel Ojukwu tare da tsare shi.

    Ɗan jaridar da ke aiki a gidauniyar aikin jarida na bin diddigi, ya ɓata ne a ranar 1 ga watan Mayu. Daga bisani kuma an gano cewa yana hannun ƴan sanda, inda aka zarge shi da take dokar yaƙi da laifukan intanet ta Najeriya.

    Ƙungiyar ta ƙara da cewa hukumomi sun yi ta watangaririya da shi a tsakanin ofisoshin ƴan sanda har da cibiyar daƙile laifukan intanet da sashen binciken manyan laifuka a Abuja.

    HWR ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ta yi tanadi cewa duk wanda ake zargi da aikata laifi a gurfanar da shi a gaban kotu cikin sa'a 48 da aka kama shi.

    Ƙungiyar ta ce "Ojukwu ya ci gaba da zama a tsare ba tare da tuhumarsa ba fiye da kwana tara."

    Wurin aikin Ojukwu ya ce an kama ɗan jaridar ne kan wani rahoto da ya yi wanda aka wallafa a watan Nuwamba, inda ya zargi wani tsohon babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan shirin tabbatar da muradun ƙarni, Adejoke Orelope-Adefulire, da tura naira miliyan 147 na asusun gwamnati domin gina makarantu zuwa wani asusun banki na gidan abinci.

    • Ƙalubale biyar da ƴan jarida ke fama da su a duniya
  7. Yarima Harry da Meghan na ziyara a Najeriya

    A ranar Juma'a ne yarima Harry da mai ɗakinsa Meghan Markle - masu riƙe da sarautar Duke da Duchess na Sussex na Birtaniya, ke wata ziyara ta yini uku a Najeriya.

    Ma'auratan za su je Najeriya - a karon farko - bisa gayyatar da suka samu daga babban hafsan tsaron ƙsar Janar Chritopher Musa.

    Ana sa rai za su kai ziyara wata cibiyar gyaran hali tare da ganawa da ƙungiyoyi da ke aiki domin tallafawa walwalar ƴan mazan jiya.

    A yayin ziyarar tasu ta yini uku, za su je jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya domin tattaunawa da sojojin da suka ji rauni da iyalansu.

    Za kuma su kai ziyara zuwa jihar Legas.

    Rundunar sojin Najeriya sun ce ziyarar ta wanda ya assasa wasan Invictus da ake shiryawa domin ƴan mazan jiya da sojojin da suka ji rauni a filin daga, za ta taimaka wa sojojin da suka ji rauni sanadiyyar aiki.

    Najeriya dai na neman ta karɓi baƙuncin gasar ta Invictus Games a 2029.

    Meghan kuma za ta jagoranci wani taron mata a shugabanci.

    Ofishin jakadancin Birtaniya a Abuja ya ce ba shi da hannu a ziyarar ta Meghan da Harry saboda ma'auratan na ziyarar ne a ƙashin kansu.

    • Yarima Harry: Ba na son abin da ya faru da mahaifiyata Diana ya samu matata
  8. Ƴanbindiga sun sace ɗalibai a jami'ar kimiyya da ke Kogi

    A ranar Alhamis da daddare ne ƴan bindiga suka mamaye jami'ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Okene a jihar Kogi inda suka sace wasu ɗalibai.

    Wani shaida ya ce ƴan bindiga sun kutsa jami'ar cikin dare yayin da wasu ɗalibai ke karatu domin shiryawa jarrabawar da ke tafe.

    Majiyar ta ce ƴan bindigar sun shiga jami'ar ne ta daji inda suka shiga ɗakunan karatu uku tare da buɗe wuta.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya ce majiyar ta bayyana cewa ƴan bindigar sun tsare ɗaliban a ajujuwansu inda suka riƙa ɗibansu, "an jefa makarantar cikin ruɗani yayin da ɗalibai cikin fargaba a wasu ajujuwan suka nemi mafaka, suka kuma watsu zuwa wasu wuraren jami'ar."

    A cewar majiyar, ɗaliban na shiryawa jarabawar zango na farko da za a soma ranar 13 ga watan Mayu, lokacin da ƴan bindigar suka afka masu.

    Shugaban jami'ar, Farfesa Abdulrahman Asipita, ya tbbatar da faruwar lamarin sai dai bai ce komai ba game da adadin ɗaliban da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su.

    Ƙoƙarin ji daga kwamishinan ƴan sandan Kogi, Mista Bethrand Onuoha, bai yi nasara ba.

  9. Birtaniya ta fita daga ƙangin taɓarɓarewar tattalin arziki

    Ƙididdiga daga hukuma na nuna cewa Birtaniya ta fita daga ƙangin taɓarɓarewar tattalin arziki sakamakon bunƙasar da tattalin arzikin ya yi a watanni ukun farko na wannan shekarar.

    Tattalin arzikin Birtaniya ya bunƙasa da kashi 0.6 cikin 100 bayan shafe rubu'i biyu na shekarar bara cikin matsalar tattalin arziki.

    Ana ganin ƙididdigar baya-bayan nan a matsayin wani ci gaba ga Firaiminista Rishi Sunak wanda ya bunƙasa tattalin arziki ke kan gaba cikin ƙudurorinsa gabanin babban zaɓen da ake sa rai zai kira a wannan shekarar.

  10. Ina fatan daƙile bambancin da ke tsakani na da Biden – Netanyahu

    Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce yana fatan kawo ƙarshen bambance bambancen da ke tsakaninsu da Joe Biden, to amma duk da haka ya sha alwashin ci gaba da kai farmaki Rafah.

    Wakilin BBC ya ce Mr Netanyahu ya ce ƙasashen biyu sun sha warware rashin fahimtar da suka samu a baya a don haka yana fatan za su sake yin hakan.

    Firaiministan na Isra'ila na magana ne da kafar yaɗa labaran Amurka bayan da shugaba Biden ya tabbatar da cewa Amurka ta daina samar da makamai ga Isra'ilan muddin sojojin ƙasar suka kai wa Hamas hari a Rafah.

    Mr Netanyahu, ya ce dole Isra'ila ta yi galaba kan Hamas a Rafah.

    Ya ƙara da cewa idan ana so a dawo da zaman lafiya a Gaza, akwai buƙatar a kafa gwamnatin farar hula tare da sanya hannun Haɗaɗɗiyar daular Labarawa ko kuma wasu ƙasashe.

  11. Barka da Juma'a – Babbar rana

    Barka da safiya da fatan mun wayi gari lafiya.

    Nabeela Mukhtar Uba tare da abokan aiki ke fatan kasancewa tare da ku a wannan safiya.

    Za mu kawo muku labarai da rahotanni masu ƙayatarwa daga ko ina cikin sassan duniya.