Jami'an Taliban sun ce aƙalla mutum 50 ne suka mutu, wasu fiye da 100 suka jikkata sakamakon mummunar ambaliya da ta auka wa arewacin Afghanistan
Mai magana da yawun ƙungiyar, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fuskanta a gundumomin biyar da ke lardin Baghlan, inda ya yi gargaɗin hasashen samun iska mai ƙarfi a cikin dare.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya riƙa yin toroƙo tare da tafiya da gidaje a ƙauyukan da dama, da kuma lalata wasu da dama.
A 'yan makonnin nan ƙasar na fuskantar mamakon ruwan sama da ke haddasa ambaliya ruwar, lamarin da ya yi sanadin kisan kusan mutum 100 tun tsakiyar watan Afrilu.
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida na ƙasar, Abdul Mateen Qaniee, ya ce fiye da mutum 150 ne suka maƙale a cikin ambaliyar, waɗanda kuma ya ce suna buƙatar taimakon gaggawa.
Mista Qaniee ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa tuni aka tura jirage masu saukar ungulu zuwa lardin na Baghlan da ke arewacin Kabul, babban birnin ƙasa.
To sai dai ya ce ''aikin ceton zai gamu da tasgaro'' saboda rashin hasken da za a yi amfani da shi don gano mutanen idan dare ya yi.
Wani jami'in gwamnatin ƙasar mai suna, Hedayatullah Hamdard ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an tura tawagar ma'aikatan agaji ciki har da sojoji domin ''ceto mutanen da suka maƙale cikin ruwa da turɓaya''.
Hukumomin ƙasar sun ce tuni suka tanadi tantuna da barguna da abinci ga iyalan da suka rasa gidajensu.