Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 9/5/2024.
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Nabeela Mukhtar Uba
Burtaniya ba za ta goyi bayan manyan hare-haren Isra'ila a Rafah ba - Cameron
Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Burtaniya, Lord Cameron ya sake nanata matsayin Burtaniya kan ƙin goyon bayan manyan hare-haren da Isra'ila ke shirin aiwatarwa a Rafah "sai dai idan akwai fayyaceccen tsari kan yadda za a kare rayukan fararen hula".
"Ba mu ga wannan tsarin ba, saboda haka a yanzu ba za mu goyi bayan manyan hare-haren a Rafah ba," in ji Cameron.
Amurka ce dai babbar ƙasar da ke bai wa Isra'ila makamai. Gwamnatin Burtaniya ba ta bai wa Isra'ila makmai, muna lasisi masu yawa, kuma ina tunanin kai kayan yaƙi zuwa Isra'ila da muke yi yana ƙasa da kaso ɗaya na kayan yaƙin da suke samu." In ji Cameron.
Jirgi ƙirar Boeing 737 ya yi hatsari yayin tashi a Senegal
Asalin hoton, Getty Images
Wani jirgi ƙirar Boeing 737-300 ya yi hatsari a lokacin da yake ƙoƙarin tashi sama a Senegal, abin da ya yi sanadiyyar jikkatar mutum 11 - hudu daga ciki sun samu mummunan rauni .
Jirgin dai wanda ke tashi zuwa birnin Bamako na ƙasar Mali ya yi saɓi zarce daga kan titinsa da safiyar yau Alhamis, kamar yadda jami'an filin jirgin saman Blaise Diagne na Senegal suka ce a wata sanarwa.
Tuni dai aka dakatar da sauka da tashin jirage a filin jirgin saman.
An fara bincike kan musabbabin faruwar hatsarin.
Sojoji sun daƙile shirin ‘yan ta’adda na kai hari a jihar Adamawa
Asalin hoton, Getty Images
Dakarun sojojin Najeriya da ke yaƙi da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya tare da rundunar haɗin gwiwar sojoji da ƴan sa-kai sun yi nasarar kame wasu gungun 'yan ta'adda da ke kan hanyarsu ta kai hari a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa.
Rundunar sojin Najeriyar wadda ta wallafa hakan a shafinta na X, ta ce dakarunta sun ci karo da ƴan ta'addar da ke shirin kai wa al’ummar hari ne a lokacin da suke sintiri a kusa da Wuro Jabbe.
Ta kuma ce anyi zazzafar musayar wuta tsakanin sojojin da ƴan ta'adda da har ya tilasta wa ‘yan ta’addar miƙa wuya tare da barin makamansu. Sojojin sun kuma ƙwace makamai da harsasai 402.
A wani samame na daban kuma amma mai alaka da wannan, sojojin sun ce sun kama wasu mutane uku da ake zargi da harbin bindiga a yankin Sukuk, da ke karamar hukumar Madagali ta jihar. An kama waɗanda ake zargin da makamai da dama.
Sojojin Najeriya na ci gaba da taka-tsan-tsan tare da jajircewa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a yankunan ƙasar.
Lokuta biyar da mutanen gari suka yi wa jami'an tsaro kisan gilla a Najeriya
Fuskokin 'ƴan ta'addan' da sojojin Najeriya ke nema ruwa-a-jallo
Ana zanga-zangar neman sakin dan jarida a Abuja
Asalin hoton, FIJ/X
Wasu ƙungiyoyin fararen hula
da ‘yan jarida sun mamaye hedikwatar rundunar ƴan sandan Najeriya da ke Abuja, inda suka buƙaci a
saki wani ɗan jarida da ke aiki da gidauniyar tallafawa ‘yan jarida masu binciken kwakwaf mai
suna Daniel Ojukwu wanda ke tsare a ofishin ‘yan Sanda.
Masu zanga-zangar sun haɗa da Deji Adeyanju da kuma dan rajin kare dimokradiyya, Omoyele Sowore.
Jami’an leken asiri na Sufeto
Janar na ƴan sandan Najeriya Olukayode Egbetokun ne suka kai Ojukwu cibiyar da
ke Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.
Masu zanga-zangar sun ce sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin a sake shi, amma abin ya ci tura.
''Matasan yanzu ba su damu da karanta jarida ba''
An zargi Trump da tunzura cin zarafin 'yan jarida
Hotunan yadda Falasɗinawa ke barin Rafah sakamakon luguden wutar Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
Yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza an samu aƙalla mutum 80,000 da suka gudu daga birnin Rafah a cewar hukumar majalisar ɗinkin duniya da ke kula da Falasɗinawa ƴan gudun hijira.
"Ana ƙara tilastawa mutane shiga halin rashin matsugunni a zirin Gaza", "matsin yayi tsanani a kan mutane. babu wani wajen tsira. Muna buƙatar a tsagaita wuta nan take". a cewar UNRWA a shafinsu na X.
A baya sama da Falasɗinawa miliyan ɗaya inda rabinsu ƙananan yara ne ke yin mafuka a wajen.
Asalin hoton, Reuters
A ranar Litinin ne sojoji suka faɗa wa dubban mutane da ke ɓangarorin yammacin Rafah da su bar inda suke su koma wajen "ƴan agaji da aka faɗaɗa" inda suka ce akwai tantina da asibitoti da kuma sauran kayan ɓukatu na yau da kullum.
Ga wasu hotuna da BBC ta samo na yadda Falasɗinawan ke yin ƙaura.
Nan da kwana uku mai zai ƙare a asibitocin Rafah - Shugaban WHO
Asalin hoton, PA Media
Darekta Janar na Hukumar Lafiya Ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargaɗin cewa nan da kwanaki uku main fetur zai ƙare a asibitocin Rafah.
Tedros wanda ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X, ya ce hakan na faruwa ne saboda man da hukumar ta yi tsammanin zai kai ga Rafah ba a bar shi ya shiga ba.
"Ɗaya daga cikin asibitocin Rafah guda uku - Al-Najjar an tilasta masa dakatar da aiki. An ɗauke marasa lafiya zuwa wasu wuraren sannan ma'aikatan asibitin suna cire wasu kayayyakin aiki domin tseratar da su." In ji shi.
Ghebreyesus ya ce hukumar WHO ta ajiye wasu magunguna da ɗakunan ajiya da asibitoci to amma idan har ba za a samun ƙarin tallafi ya shiga Gaza ba to fa "ba za mu iya ci gaba da gudanar da ayyukan tallafi ga asibitoci ba."
Ina tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ta tsaya?
Asalin hoton, Reuters
Ana ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza inda tawagogin Isra'ila da Hamas da kuma Amurka ke ganawa da masu shiga tsakani a birnin Alkahira.
To, ko ina tattaunawar tsagaita buɗe wuta a Gaza ta tsaya?
Hamas ta fada a ranar Litinin cewa ta amince da shawarar tsagaita buɗe wuta daga Masar da Qatar, wanda tushensa shi ne tsagaita bude wuta na tsawon makonni a yakin da kuma sako wasu da dama da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Sai dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ba zasu amince da shawarar da Hamas ta amince da ita domin ta yi nisa da bukatun Isra'ila.
Natenyahu ya kuma ce ya umurci tawagar masu matsakaicin matsayi na Isra'ila da aka aika zuwa birnin Alkahira da su tsaya tsayin daka kan sharuddan da ake bukata na mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma "muhimman sharuddan tabbatar da tsaron Isra'ila".
A ranar Laraba dai Hamas ta ce ba za ta yi wa Isra'ila ƙarin sassauci a tattaunawar tsagaita buɗe wuta ba.
A cikin wata sanarwa da Izzat El-Reshiq, mamba a ofishin siyasa na Hamas a Qatar ya fitar, ya ce kungiyar ba za ta wuce kudurin tsagaita buɗe wuta da ta amince da shi a ranar Litinin ba.
Isra'ila dai har yanzu ba ta mayar da martani ga sanarwar ba.
Watakila Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza
Isra'ila ta karɓe iko da mashigar Rafah a Gaza
Labarai da dumi-dumi, Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da 'yarsa
Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika da 'yarsa Fatima wadanda aka gurfanar da su yau a gaban kotu.
An bayar da belin ne kan kudi naira miliyan 100 ga kowannen su, har da ma sauran mutum biyu da aka gurfanar tare da su.
Ana zargin Sirika ne da sauran mutanen da laifin badakalar kudi da suka kai naira biliyan 2.7.
Sauran ka'idojin belin sun hada da kawo wadanda za su tsaya musu wadanda suka mallaki kadarori a Abuja.
EFCC ta kama wasu mutum 29 da ake zargi da damfara ta Intanet a Abuja
Asalin hoton, EFCC/X
Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC na shiyyar Abuja sun ce sun kama mutum 29 da ake zargi da damfara ta intanet.
Hukumar EFCC ta sanar da hakan a shafinta na X.
Hukumar ta ce an kama su ne a unguwannin Apo da Gwarimpa da Katampe da ke Abuja sakamakon samun bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na damfara ta intanet.
Kayayyakin da aka kama daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyi 43 na kera daban-daban da motoci shida da agogo mai kaifin basira guda biyu.
Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Yadda ake damfarar tsofaffi a intanet
Wasika daga Afirka: Abin da ya sa 'yan Najeriya ke kaunar masu damfara ta intanet
An kashe fiye da Falasɗinawa 34,900 tun fara yaƙi - Hukumar lafiyar Hamas
Asalin hoton, Reuters
Fiye da Falasdinawa 34,900 ne aka kashe tare da jikkata 78,500 tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da yakinta na soji a Gaza, in ji ma’aikatar lafiya ta Hamas a yankin.
A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an kashe mutum 60 tare da raunata 110 in ji ma'aikatar.
Sojojin Isra'ila sun fara wani gagarumin farmakin ramuwar gayya a Gaza bayan da aka kashe kimanin mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 252 a harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
Za a ɗauki shekaru kafin kwance bamabaman da ba su fashe ba a Gaza - MDD
Zanga-zangar yaƙin Gaza: Me ake nufi da Intifada?
Sirika da ‘yarsa sun gurfana a kotu
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika da karin wasu a yau Alhamis, a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama.
Sirika, minista ne a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma an gurfanar da shi a gaban kuliya ne bisa tuhume-tuhume shida. Sauran wadanda aka gurfanar da su tare su uku akwai ‘yarsa Fatima Hadi Sirika da Jalal Sule Hamma da kamfanin Al-Duraq Investment Ltd, bisa laifin almundahanar kudin da suka kai Naira biliyan 2.7.
A wani bangare na binciken da hukumar EFCC ke yi kan badakalar kudi da ake zargin tsohon ministan ya aikata sun hada da bada kwangilar damfara da ma’aikatarsa ta yi a karkashin sa.
Wata majiyar EFCC ta shaida wa BBC cewa sun gayyaci tsohon ministan domin yi masa tambayoyi daga masu binciken da ke kula da badakalar kwangilar da ake zarginsa da aikatawa lokacin da yake ministan ma'aikatar sufurin jiragen sama.
Ya mutunta gayyatar kuma aka tsare shi.
An tattaro cewa hukumar EFCC ta dade tana binciken badakalar kwangilar da ake zargin ministar yana kan aiki, har ma ya gana da masu bincike kafin a tsare shi da aka yi.
Tun da farko dai an shirya gudanar da shari’ar ne a ranar Talatar da ta gabata amma saboda rokon da EFCC ta yi na gyara wasu tuhume-tuhumen, an bayar da sabuwar rana zuwa yau.
A cewar hukumar EFCC, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya bai wa wani kamfani Engirios Nigeria Limited wasu manyan kwangiloli guda hudu da ake zargin yana da alaƙa da ɗan uwansa Abubakar Sirika.
Kamar yadda EFCC ta bayyana, binciken ya tabbatar da cewa an bayyana Abubakar a matsayin Darakta na Kamfanin.
An ambaci cewa shi kadai ne mai izinin sanya hannu kan asusun ajiyar kudi biyu na kamfanin.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta bayyana cewa tsohon Ministan, Hadi Sirika, ya sanya wa dan uwansa Abubakar kwangilolin, duk da sanin cewa Abubakar na rike da mukamin ma’aikacin gwamnati
Da gaske Hadi Sirika ya yi barazanar ɗaure Yari da Fintiri?
Majalisar Dattijan Najeriya ta musanta zargin almundahana kan aikin Hajji
Jihar Kaduna za ta sauya wa makarantu matsuguni saboda rashin tsaro
Asalin hoton, X/@GovKaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana shirinta na sauya wa makarantu 359 matsuguni sanadiyyar ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a jihar.
Lokacin da yake magana a wani taro na masu ruwa da tsaki, Gwamna Uba Sani wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar, ya ce ayyukan ƴan bindiga kamar satar ɗalibai a Kuriga da wasu makarantu da ke faɗin jihar na dagula al'amura a ɓangaren ilimi.
Ya ce a dalilin haka ne yanzu haka gwamnati ta fara shirin sauya wa makarantu 359 matsuguni zuwa wasu wuraren da babu matsalar tsaro.
Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da hare-hare na ƴanbindiga waɗanda ke kashewa tare kuma da satar mutane domin neman kuɗin fansa a arewa maso yammacin Najeriya.
Hari na baya-baya nan da ya ɗauki hankali shi ne wanda ƴan bindigar suka kai a ƙauyen Kuriga da ke cikin ƙaramar hukumar Chikun, inda suka sace ɗalibai da malaman makarantar.
'Rashin tsaro ya nakasa mu, dusa muke ci domin rayuwa a yanzu'
Rashin tsaro: Mutum '6000' na gudun hijira a Kaduna
Assalamu alaikum
Muna yi maku barka da wannan lokaci.
Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma wasu sassan duniya.
Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.