Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Umar Mikail
Hotunan wasu tankokin yaƙin Isra'ila a yankin Gaza na Rafah
Isra'ila ta fitar da waɗannan hotuna da ke nuna tankunan yaƙin ta da ke aiki a mashigar Rafah, mahaɗar Zirin Gaza da Masar kuma hanyar da ake amfani wajen shigar da kayan taimakon kasashen duniya zuwa Gaza.
Asalin hoton, Israel Defense Forces
Asalin hoton, Israel Defense Forces
Asalin hoton, Israel Defense Forces
Asalin hoton, Israel Defense Forces
An janye tuhumar da ake yi wa mataimakin shugaban ƙasar Malawi
Asalin hoton, AFP
Wata kotu a ƙasar Malawi ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima na cin hanci da rashawa bayan da mai gabatar da kara na kasar ya bayar da sanarwar dakatar da shari'ar.
Ba a bayar da dalilan yanke hukuncin ba.
An kama Chilima ne a watan Nuwamba 2022 bisa zarginsa da karɓar kuɗi a madadin ba da kwangilolin gwamnati amma kuma ya musanta zargin.
Matakin ya haifar da ayar tambaya kan yadda gwamnati ke tafiyar da shari’a kan zargin cin hanci da rashawa.
Kamen mataimakin shugaban kasar ya biyo bayan tuhumar da ake masa na karbar kudi domin bayar da kwangiloli ga kamfononin Xaviar Ltd da Malachitte FZE, kamfanoni biyu da ke da alaƙa da ɗan kasuwa kuma ɗan Birtaniya Zuneth Sattar.
Sattar dai ya musanta aikata wani laifi.
Mataimakin shugaban kasar dai ya gurfana gaban kotu da dama tun bayan kama shi, duk da cewa ba a fara shari'ar ta gaskiya ba.
A ranar Litinin din da ta gabata ne alkalin kotun Redson Kapindu ya bayar da umarnin a sallame shi ba tare da ɓata lokaci ba, sakamakon ƙarar da daraktan da ke kula da kararrakin jama'a (DPP) ya shigar a ranar Juma'ar da ta gabata na "a dakatar da tuhumar da ake yi mataimakin shugaban ƙasar.
An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi - Ma'aikatar lafiyar Hamas
Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba, bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙinta na soji a matsayin martani ga hare-haren Hamas a kudancin Isra'ila.
Adadin waɗanda suka mutu ya haɗa da aƙalla mutane 54 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji ma'aikatar.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kuma ce Falasdinawa 78,204 ne suka jikkata tun ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da yaƙin ya shiga wata na takwas.
A ranar 7 ga watan Oktoba ne 'yan bindigar Hamas suka kai hari a kudancin Isra'ila, inda suka kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da fiye da mutum 250.
Ana zargin Isra'ila da laifukan yaƙi bayan kisan yaro Bafalasɗine
Zanga-zangar yaƙin Gaza: Me ake nufi da Intifada?
Ana ƙidayar ƙuri'u bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa a Chadi
Asalin hoton, MICHEL MVONDO/BBC
An ci gaba da ƙidayar kuri'u bayan kammala zaɓen shugaban kasa a jiya a ƙasar Chadi da nufin kawo karshen mulkin soji na tsawon shekaru uku.
Hukumar zaɓe ta ƙasar (Ange) ta ce an samar da tsauraran matakai na hana maguɗi yayin kidayar kuri’un.
Shugaban mulkin sojin kasar Janar Mahamat Idris Deby ya ce ya cika alkawuran da ya ɗauka wa 'yan kasar Chadi na shirya zabe.
“Na cika alƙawuran da na dauka kuma na cika burina, yanzu haka makomar kasarmu tana hannun Allah da al’ummar Chadi,” inji shi
Babban abokin hamayyarsa Firaminista Succes Masra ya buƙaci 'yan kasar Chadi da su fito da yawa don kaɗa ƙuri'arsu idan suna son "ganin wani gagarumin sauyi a kasarsu".
Hukumar zaɓen zata sanar da sakamakon zaɓen nan da ranar 21 ga watan Mayu kuma idan babu ɗan takara da ya samu cikakkiyar rinjaye, za a gudanar da zagaye na biyu a ranar 22 ga watan Yuni.
Zaɓen Chadi na 2024: Masra da Deby, sabuwar gwamnati ko tazarce
Shugaban ƙasa tsohon fursuna da ke bai wa matasan Afirka ƙwarin gwiwa
Za a fara cire wa masu tura kuɗi ta banki harajin tsaron intanet a Najeriya
Asalin hoton, CBN
Babban bankin Najeriya CBN ya bai wa bankuna a ƙasar umarni da su fara cire kashi 0.5 cikin 100 a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki a matrsayin kuɗaɗen tabbatar da tsaro ta intanet.
Cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun Chibuzor Efobi, Daraktan kula da tsarin biyan kuɗi da Haruna Mustafa, Daraktan kula da manufofin kuɗi, babban bankin ya ce za a fara aiwatar da wannan tsari ne nan da makonni biyu masu zuwa.
A cewar CBN, kuɗin da za a cira domin tara harajin tsaron intanet ya zo ne sakamakon amincewa da dokar yaƙi da laifukan intanet ta 2024 da aka yi wa gyaran fuska.
Sanarwar ta ce za a zuba kuɗin da aka cira ne a asusun tsaron intanet na ƙasa wanda zai kasance a ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
Tsarin bai shafi masu karɓa da biyan bashi ba da kuɗaɗen albashi da kuma mutumin da zai tura kuɗi daga asusun ajiyarsa na banki zuwa wani asusun nasa na daban da kuma masu tura kuɗi zuwa wani asusun na banki ɗaya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Kenya za ta sake tsugunar da iyalai 40,000 da ambaliyar ruwa ta shafa
Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Kenya ta yi alƙawarin sake tsugunar da iyalai 40,000 waɗanda ambaliyar ruwa da ruwan sama mai karfi suka shafa a Nairobi babban birnin kasar tun tsakiyar watan Maris.
Shugaba William Ruto ya wallafa a shafin X cewa gwamnatin ƙasar ta ware dala miliyan 7.3 don sake gina makarantun da ambaliyar ruwa ta lalata a mafi yawan sassan ƙasar.
Ya bayyana hakan ne bayan ya ziyarci unguwannin marasa galihu na Mathare a birnin Nairobi.
A ranar 3 ga watan Mayu, ya ɗage buɗe makarantu kwata-kwata saboda ruwan sama da ake ci gaba da yi wanda ya haddasa mummunar ambaliyar ruwa.
Nairobi na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da lamarin ya fi shafa, inda ambaliyar ta kashe mutane da dama, tare da lalata hanyoyi da sassan hanyar jirgin ƙasa a babban birnin kasar.
Aƙalla mutane 229 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a ƙasar da ke gabashin Afirka, a cewar gwamnatin ƙasar.
'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'
NEMA ta yi Gargadin fuskantar ambaliyar ruwa a Najeriya
Yau ake rantsar da Putin a matsayin shugaban Rasha karo na biyar
Asalin hoton, Reuters
A yau
ake bikin rantsar da Vladimir Putin a matsayin shugaban Rasha karo na biyar.
Nasararsa
a zaɓen watan Maris na zuwa ne makonni da mutuwar fitaccen abokin hamayyarsa,
Alexei Navalny, a gidan yari.
Wakilin
BBC ya ce kusan shekara 25 yanzu da Putin ke mulki a Rasha a matsayin shugaban
ƙasa ko shugaban gwamnati
Ƙasashen
yamma sun yi alla-wadai da zaɓensa a wannan lokaci da suka ce babu sahihanci da
daraja dimokuraɗiyya.
Ƙasashen
Amurka da na Tarayyar Turai sun ce za su ƙauracewa bikin da aka shirya a
Kremlin - kodayake Faransa da wasu ƙasashen na Turai za su tura wakilai duk da
roƙon da Ukraine ta yi cewa su yi biris.
Abun da ya sa Putin ke samun ƙarfin iko fiye da kowane lokaci
Ko kun san makomar masu adawa da Putin?
Gomman mutane sun maƙale bayan rugujewar gini mai hawa biyar a Afirka ta Kudu
Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatan agaji a Afrika ta Kudu sun dukufa wajen lalubo mutanen da ke da sauran numfashi bayan da wani gini mai hawa biyar da ake ginawa ya ruguje, lamarin da ya halaka mutum biyar, sai wasu 50 da suka maƙale.
Jami'ai a birnin George, da ke lardin Western Cape sun ce mutum 24 aka zaƙulo daga ɓuraguzai kuma an kai su asibiti.
Wasu ma'aikata 75 na wurin lokacin da ginin ya ruguje ranar Litinin.
Ana gudanar da bincike kan musabbabin da ya janyo haɗarin.
Jami'an bayar da agajin gaggawa sun yi hanzarin zuwa wurin bayan ginin ya rufta da ƙarfe 12:09 agogon GMT.
Biyu cikin 22 da aka zaƙulo daga ɓuraguzai sun mutu sakamakon raunin da suka ji. An kuma ba da rahoton mutuwar ƙarin mutum uku.
"Muna tare da iyalai da duka waɗanda hatsarin ya shafa," in ji magajin garin George Ald Van Wyk.
Masu aikin ceto fiye da 100 ne tafe da karnukan farauta suka shafe dare suna aiki domin gano mutanen da suka maƙale cikin ɓuraguzai.
Jami'ai sun ce sun yi nasarar ji daga mutanen da suka maƙale cikin ɓuraguzan gini.
An rushe rabin gine-ginen Gaza - Binciken BBC
Wa zai kai wasan ƙarshe tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu?
Assalamu Alaikum!
Muna yi maku barka da wannan lokaci.
Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma wasu sassan duniya.
Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.