Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/4/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Gwamnonin Arewa na ganawa a Kaduna

    ..

    Asalin hoton, @Abdool85/X

    Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun hallara a jihar Kaduna inda suke wata ganawa.

    Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya a jawabin da ya gabatar, ya miƙa saƙon jaje ga al'umomin jihar Kaduna da Katsina da Nijar da Filato da Zamfara saboda ƙalubalen tsaro da suka fuskanta a baya-bayan nan.

    A cewarsa, tsaro na daga cikin abubuwan da taron ya fi mayar da hankali a kai inda yace tun bayan taron da suka yi a baya, sun gana da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro da hafsoshin tsaro da gamayyar ƙungiyar farar hula a arewa da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da hanyar tabbatar da zaman lafiya da daidaito a yankin.

    "Yayin da ƙasar ke ci gaba da tattauna batun ƴansandan jiha, yana da muhimmanci mu fara duba tsarin samar da ƴansandan jihohi da aka gina kan tubalin haɗin kai tsakanin jihohin arewa." in ji shugaban ƙungiyar.

    Gwamna Inuwa Yahaya ya ƙara da cewa samar da bunƙasar tattalin arziki abu ne "mai muhimmanci ga yankinmu" kuma "muna ganin samar da ci gaban tattalin arziki malsaha ce mai ɗorewa ga ƙalubalen tsaron da muke fuskanta."

    Ya bayyana cewa farfaɗo da kamfanin bunƙasa Najeriya, NNDC na daga cikin manyan abubuwan da suka shafi tattalin arzikin yankin arewa.

    Game da batun ilimi, shugaban ƙungiyar ta gwamnonin arewa ya ce abin damuwa ne a ce yankin arewa a yanzu yana da mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya, abin da ya ce ya zama dole a ɗauki mataki a kai.

    Gwamna Yahaya ya kuma bayyana muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnonin yankin musamman ta ɓangaren samar da abubuwan more rayuwa da samar da harkokin kasuwanci da tsaro da musayar abubuwan al'ada.

    Yankin arewacin Najeriya na fama da tarin matsaloli da dama da suka shafi tsaro da talauci.

    Matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa ta zama ruwan dare a yankin.

    ..

    Asalin hoton, @Abdool85/X

    ..

    Asalin hoton, @Abdool85/X

  2. Sojojin Sahel sun kashe babban kwamandan ƙungiyar IS

    Dakarun haɗin gwiwa daga Mali da Burkina Faso da Nijar sun halaka babban kwamandan ƙungiyar IS da aka yi shelar ba da ladan dala miliyan biyar idan aka kashe shi.

    Kisan shi wani ɓangare ne na samamen da aka kai kan iyakokin da ke tsakanin ƙasashen uku na yankin Sahel, in ji gidan talabijin na Mali.

    An kashe Abu Huzeifa, ɗan ƙungiyar ISGS a yankin Menaka da ke arewacin Mali ranar Lahadi.

    An alaƙanta shi da sumame da dama da ƴan ta'adda suka yi a yankin, ciki har da harin da aka kai a 2017 inda aka halaka sojojin Amurka huɗu da wasu sojin Nijar huɗu.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi tayin ba da ladan dala miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayani a kan Huzeifa saboda rawar da ya taka a kai harin.

    Masu amfani da shafukan sada zumunta a Mali sun nuna farin ciki da samamen inda suka jinjinawa sojojin yankin bisa nasarar da suka yi a wurin da sojojin ƙasashen yamma suka gaza.

  3. Me ya sa gaba tsakanin Davido da Wizkid ta ƙi ci ta ƙi cinyewa?

  4. Majalisar ministocin Kenya na taro kan ƙaruwar ambaliya

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Kenya William Ruto ya kira taron majalisar ministoci domin tattauna batun ambaliyar ruwan da ake fama da ita a ƙasar.

    Kimanin mutum 169 ne suka mutu sanadin ambaliya da ta ɗaiɗaita yankunan Kenya a watan da ya gabata, kamar yadda kakakin gwamnati Isaac Mwaura ya ce.

    Adadin ya haɗa da mutum 45 da suka mutu da safiyar Litinin bayan da ambaliyar ta lalata ƙauyuka kusa da Mai Mahiu da ke da nisan kilomita 60 daga Nairobi, babban birnin ƙasar.

    Ƙungiyar agaji ta Kenya Red Cross ta ce mutum 50 ne suka mutu.

    A wata hira da BBC, Shugaba Ruto ya kare matakin gwamnatinsa bayan sukar da gwamnatocin larduna ke yi cewa tana jan ƙafa.

    Mista Ruto ya ce taron majalisar ministocin zai tattauna ƙarin matakan da ya kamata a ɗauka domin magance matsalar ambaliyar.

    Fiye da mutum 130,000 ne suka ɗaiɗaita sakamakon ambaliya inda mutane da dama suke samun mafaka a makarantu.

  5. Kotu ta ɗaure tsohon da ya yi sama da faɗi da naira miliyan 12 na magada

    ..

    Asalin hoton, EFCC/X

    Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan gyaran hali da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda samun shi da laifin sama da faɗi da kuɗin magada kimanin naira miliyan 12.

    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati ce ta wallafa bayanin ranar Talat a shafinta na X.

    Tun a ranar 3 ga watan Yulin 2023 ne hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotun kan zargin karkatar da dukiyoyin magada da aka ƙiyasta kuɗinsu ya kai kimanin naira miliyan 12 ga buƙatar kansa maimakon amfani da ita wajen kula da magada.

    Dukiyoyin sun haɗa da gidaje uku da filaye biyu da aka kange - ɗaya daga ciki ɗauke da shaguna bakwai sai gidajen burodi biyu da wani fili da manyan tankoki biyu sai babban injin janareto.

    Isiyaku Ibrahim ya musanta zargin da ake masa lamarin da ya sa lauyan masu ƙara Faruqu Muhammad ya gabatar da shaidu shida gaban kotu.

  6. Kotu ta ƙi tilasta wa shugaba Akufo sa hannu kan dokar hana neman jinsi

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Babbabr kotu a Accra, babban birnin Ghana ta yi fatali da buƙatar tilasta wa shugaban ƙasar sa hannu kan ƙudurin hana neman jinsi da ya janyo ce-ce-ku-ce wanda majalisar dokokin ƙasar ta amince da shi a watan Fabarairu.

    Ofsihin shugaba Nana Akufo Addo a watan da ya gabata ya ce shugaban ba zai sa hannu kan ƙudirin ba har sai koyun ƙoli ta yanke hukunci kan matsayinsa a kundin tsarin mulki lamarin da ya janyo rikicin siyasa a ƙasar.

    Alƙali Ellen Lordina Serwaa Mireku ta goyi bayan matsayar fadar shugaban ƙasa inda ta yanke hukuncin cewa bai dace ba a tilasta wa Mista Akufo-Addo ya sa hannu kan ƙudirin saboda har yanzu ƙudirin na fuskantar ƙalubale biyu a gaban kotun ƙoli, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Wasu ƴan Ghana biyu ne - ƴar fafutuka Amanda Odoi da lauya Richard Dela Sky suka shigar da ƙara gaban kotun ƙolin.

    Suna neman a hana amincewa da ƙudirin a amtsayin doka.

    Ƙudirin ya tanadi hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara uku ga duk wanda ke neman jinsi da kuma hukuncin shekara biyar a gidan gyaran hali idan suka tallata ɗabi'unsu.

    Ɗan majalisa Rockson-Nelson Dafeamekpor ya gabatar da ƙudirin tilasta wa Mista Akufo-Addo ya sa hannu kan ƙudirin da ya janyo taƙaddama

    Lauyansa ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin, in ji kafafen yaɗa labaran ƙasar.

    Ƙudirin ya janyo rarrabuwar kai tsakanin mutane a Ghana inda ma'aikatar kuɗi ke gargaɗin cewa ƙasar na iya asarar tallafin bankin duniya na aƙalla dala biliyan 3.8 idan har ƙudirin ya zama doka.

    Sai dai ƴan majalisa da dama da mutane na matsa wa shugaba Akufo-Addo lamba ya sa hannu kan ƙudirin.

    • Me ya sa Ghana ke fama da ƙarancin lantarki a kwanan nan?
  7. Sojoji sun tarwatsa maɓoyar ƴanbindiga, sun kuɓutar da mutane a Taraba

    ..

    Asalin hoton, Nigeria Army/X

    Dakarun Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar murƙushe ayyukan ƴanbindiga a jihar Taraba ta Whirl Stroke sun tarwatsa wani sansanin ƴanbindiga inda suka kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da gano tarin makamai da alburusai.

    Rundunar sojin Najeriyar ce ta wallafa hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

    A cewar sanarwar, dakarun da aka girke a Fikyu, a ranar 29 ga watan Afrilu sun kai ɗauki kan wasu rahotanni da suka samu cewa wasu da ake zargi ƴanbindiga ne sun buɗe wuta a yankin Pukun da ke Fikyu a ƙaramar hukumar Ussa. Sojojin sun yi musayar wuta da su har suka samu galaba a kansu.

    Ƙarin binciken a yankin ya sa sojoji sun gano bindiga ƙirar AK47 da ƙunshin alburusai.

    Kazalika, sojojin da aka tura Kufai Amadu da Kasuwan Haske tare da haɗin gwiwar sojoji daga runduna ta ɗaya sun ɗauki mataki kan wani bayanin sirri da suka samu game da maɓoyar ƴanbindiga a ƙauyen Vingir da ke ƙaramar hukumar Katsina Ala a jihar Benue. A nan ma sojojin sun yi arangama da ɓatagarin inda suka murƙushe su.

    Sojoji sun kama wani da ake zargi mai garkuwa da mutane ne da aka same shi da wayoyin hannu biyu ƙirar Techno da kuɗi naira dubu 40.

    An yi bincike a sansaninsu inda kuma aka gano bindiga ƙirar AK47 sannan aka samu kuɓutar da Dakta James Raphael da ɗansa a Gbeji a ƙaramar hukumar Ukum da ke jihar Benue.

    Sanarwar ta kuma ce sojojin da ke aiki a bataliya ta 20 sun kama wani mutum a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba tare da buhu huɗu na wani abu da ake tunanin tabar wiwi ce.

    Rundunar ta ce mutumin ya daɗe ana neman shi ruwa a jallo saboda yadda yake ta'amali da miyagun ƙwayoyi da kuma samar wa ƴan bindiga da sauran masu laifi miyagun ƙwayoyi.

    ..

    Asalin hoton, Nigeria Army/X

    • Me ake nufi idan sunanka ya fito a jerin masu tallafa wa ta'addanci?
    • Abin da ya sa nake cinikin kuɗin fansa tsakanin ƴanbindiga da iyalai
  8. Barka da Hantsi!

    Muna yi maku barka da wannan lokaci.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma wasu sassan duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.