Mu kwana lafiya
Karshen rahotanni kenan a wannan shafi.
Mu tara gobe da safe - idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage
Karshen rahotanni kenan a wannan shafi.
Mu tara gobe da safe - idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin mayar da ‘yan gudun hijirar ƙasar aƙalla 6000 daga ƙasashen Chadi da Kamaru.
Kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira (NCFRMI), Tijjani Ahmed ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja a karshen wani da aka shirya don mayar da ‘yan gudun hijirar Najeriya gida.
Ya ce kimanin ‘yan gudun hijira 21,000 ne ke a ƙasar Chadi yayin da Kamaru ke da wasu 14,000.
Ahmed ya ƙara da cewa za a mayar da mutane 6,000 daga Chadi zuwa gida yayin da za a tantance adadin waɗanda za a mayar da su daga Kamaru kafin a fara shirin wanda ake sa ran kammalawa nan da watanni biyu masu zuwa.
“Muna shirin mayar da waɗanda suke da sha’awar komawa gida, an kuma ƙulla yarjejeniya tsakanin hukumar UNHCR da gwamnatin Kamaru da kuma gwamnatin tarayya kan batun mayar da mutanenmu gida daga Kamaru," in ji shi.
Ya ce ana tattaunawa da gwamnatin jihar Borno kan wajen da za a ajiye ‘yan Najeriya da za a mayar da su gida, inda ya ce a yanzu haka ana gina gidaje a Banki da Baga domin ajiye su.
A cewarsa, galibin ‘yan gudun hijirar sun rasa matsugunansu ne sakamakon ambaliyar ruwa a 2022, rikicin Boko Haram, rikicin manoma da makiyaya da kuma kalubalen sauyin yanayi a yankin Arewa maso Gabas.
Mataimakiyar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Bernadette Muteshi, ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa jagorantar aikin mayar da 'yan gudun hijirar.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu manoma a Uganda sun ɗauki hayar ‘yan bindiga don kare musu gonakin koko domin guje wa sata daga ɓarayi waɗanda ke yin awon gaba da amfanin gona.
Farashin koko ya tashi a duniya cikin sama da shekaru goma yayin da rani ke hana manoma a Ghana da Ivory Coast, wadanda ke kan gaba wajen noman koko a duniya, samun amfanin gona mai kyau.
A cewar Mutanga Grace, wani manomin koko ɗan ƙasar Uganda kuma Shugaban hukumar fitar da kayayyaki waje a Uganda, ya ce ana satar kusan kashi 30 cikin 100 na kokon da ake nomawa a ƙasar da ke gabashin Afirka.
Ya shaida wa shirin BBC Newsday cewa manoma a ƙasar na biyan masu gadi da karnuka kuɗi don kare kokon da suke da shi.
"Koko ya zama da wahala wajen samunsa a ƙasar a halin yanzu," in ji shi.
Gwamnatin Najeriya ta ce nan da kwanaki uku za a kawo karshen tsada da kuma wuyar mai da ake fama da ita a faɗin ƙasar.
Hakan ya biyo bayan ziyarar gani da ido da manyan jami’an bangaren man fetur na ƙasar suka kai wasu gidajen mai a Abuja babban birnin ƙasar.
Yayin ziyarar, jami’an sun tattauna da manajojin gidajen man da suka ziyarta, domin tabbatar da suna da isasshen mai da za a ci gaba da sayar wa a nan gaba.
Misis Maijidda Abdulƙadir, ita ce babbar jami’ar yankin arewa maso tsakiyar Najeriya ta Hukumar kula da harkokin Sarrafa man fetur da tace wa da sufuri ta Najeriya, ta kuma yi wa Buhari Muhammad Fagge ƙarin bayani kan dalilin ziyarar tasu.

Asalin hoton, Bauchi State Government
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta kammala taron da ta gudanar a jihar Kaduna, wanda ya samu halartar kusan dukkan gwamnonin yankin 19.
Wannan ne karon farko da gwamnonin suka yi irin wannan tattaunawar a 2024.
Ƙungiyar Northern Governors' Forum (NGF) ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ta cimma ƙudirori 13 a taron.
Ga manya uku daga cikinsu

Asalin hoton, Ibrahim Yunusa
Ana can ana ci gaba da zaman alhini a Kano, bayan da kifewar wani kwale-kwale dauke da wasu ɗalibai a madatsar ruwan karamar hukumar Dambatta.
Ana fargabar cewa mutum biyu sun rasa rayukansu a hatsarin.
Lamarin ya ritsa da su ne bayan da suka shiga kwale-kwalen don yin shawagi a cikin ruwan da ke kusa da makarantar.
Ɗalibai uku ne a cikin jirgin ruwan sai kuma direba, amma dalibi daya ya kubuta tare da direban, yayin da biyu kuma suka bata.

Asalin hoton, Ibrahim Yunusa
Masu aikin ceto mutum biyun da suka bata, sun fito da gawar mutum guda.
Sai dai har yanzu ba a kai ga gano gawar mutum dayan ba.
Madatsar ruwan da lamarin ya auku da ake kira Thomas Dam, na da tazarar kilomita biyar da kwalejin.

Asalin hoton, Ibrahim Yunusa
Ana yawan samun haɗarin jiragen ruwa a Najeriya, al’amarin da ake alakantawa da yawan amfani da matattun jirage da kuma rashin bin tsari wajen amfani da jiragen ruwan.

Asalin hoton, Ibrahim Yunusa

Asalin hoton, Reuters
Hukumar kula da magunguna ta Tarayyar Turai, ta bayyana cewa akwai buƙatar sabunta allurar riga-kafin cutar Korona.
Ta ce sabon nau’in cutar mai suna JN1, shi ne ya zama ruwan dare a duk faɗin duniya, amma ya bambanta sosai da na’ukan da aka kirkiro allurar riga-kafin domin yaƙi da su.
Har yanzu cutar korona na kashe dubban mutane kowane wata.
Hukumar ta buƙaci masu sarrafa magunguna da su tuntuɓe ta, don tattauna yadda za a sarrafa sabbin magungunan domin gudanar da shirin riga-kafi na bana.
An sami rahoton kashe wani babban kwamandan ƙungiyar IS da ake nema ruwa a jallo a Afirka.
Gidan talabijin ɗin gwamnatin ƙasar Mali ya ce Abu Huzeifa, wanda ke da ladar dalar Amurka miliyan biyar a kansa ya gamu da ajalinsa ne a hannun sojojin haɗin gwiwa na ƙasashen Burkina Faso da Nijar.
Hukumomin Amurka sun sanya lada a kansa ne saboda wani hari da aka kai a shekara ta 2017 inda sojojin Amurka da na Nijar aƙalla takwas suka rasa rayukansu.
Burkina Faso da Nijar da Mali duk suna ƙarƙashin mulkin soja ne a halin yanzu kuma suna ƙulla alaƙa ta ƙut-da-ƙut da Rasha yayin da suke yanke ƙawance da ƙasashen yamma da suka haɗa har da Amurka.

Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook
Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.
Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa yau Talata.
“Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba, 1 ga watan Mayu, a matsayin hutu domin bikin ranar ma’aikata,” a cewar sakatariyar dindindin na ma’aikatar a cikin wata sanarwa.
Ta ambato ministan na sake nanata bukatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkan matakai.

Asalin hoton, Reuters
Alkalin da ke sauraron shari’ar Donald Trump kan zargin biyan tauraruwar fina-finan batsa kuɗi domin ta ɓoye mu'amalr da suka yi a birnin New York na Amurka, ya samu tsohon shugaban na Amurka da laifin ci gaba da saɓa wa dokar kotu.
Umarnin ya haramta wa Trump yin magana a bainar jama'a da yaɗa wa a shafukan sada zumunta game da mutanen da ke da hannu a shari'ar.
A ranar Talata, alkalin kotun Juan Merchan ya ce Trump ya saɓa wa umarnin sau tara.
Kotun ta ci tarar Trump dala 1,000 kan kowanne saɓa umarni.
Masu gabatar da ƙara sun ba da cikakken bayani game da yiwuwar saɓa wa kotun har sau 14, kuma Merchan na iya yanke shawara a zaman da za a yi ranar Alhamis.

Asalin hoton, NASS/FACEBOOK
Majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci ministan albarkatun mai saboda matsalar ƙarancin man da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a sassan ƙasar.
Shugaba Bola Tinubu ne ministan albarkatun mai yayin da Heineken Lokpobiri ne ƙaramin ministan albarkatun mai.
Ƴan majalisar dai ba su fayyace wanda suka gayyata ba duk da cewa ba lalle bane su gayyaci shugaban ƙasar.
Matakin gayyatar ministan ya zo ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa Shehu Ajilo daga jihar Kaduna ya gabatar bayan dawowar majalisar bakin aiki bayan hutun kwana 40.
Ministan zai yi wa ƴan majalisar bayani game da matsalar ƙarancin mai a ƙasar.

Asalin hoton, Reuters
Kotun duniya ta yanke hukuncin cewa ba za ta umurci Jamus ta dakatar da tallafin soji ga Isra'ila ba
Nicaragua ta zargi Berlin da keta yarjejeniyar kisan kare dangi da kuma taimakawa wurin kashe fararen hula a Gaza.
Gwamnatin Jamus ta ce zargin ba shi da tushe domin ba ta kai wani harsashi ko makaman roka zuwa Isra'ila ba tun watan Oktoba.
Jamus dai na daya daga cikin manyan kawayen Isra'ila, amma tana kara yin suka kan halin jin kai da ake fuskanta a Gaza.

Asalin hoton, Ajuri Ngelale/Facebook
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya miƙa saƙon jaje ga mutanen da fashewar gas ta rutsa da su a Ita-Oshin da ke ƙaramar hukumar Abeokuta ta arewa a jihar Ogun.
Fashewar ta janyo mutuwar mutane da dama da kuma salwantar dukiya mai yawa.
Tinubu ya bayyana haka ne a sanarwar da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Talata.
Shugaban ya kuma jajanta wa gwamnatin jihar Ogun da al'ummarta game da ibtila'in.
Ya kuma yaba wa gwamna Dapo Abiodun kan irin ƙoƙarinsa na tunkarar matsalar da kuma gaggauta kwantar wa da mutane hankali.
Ƴan bindiga sun bude wuta a wani masallaci a yankin yammacin Afghanistan inda suka kashe aƙalla mutane shida.
Shugaban wata ƙabila a yankin Herat ya ce an kai harin a yayin da mutane ke fitowa daga masallacin da yammacin jiya litinin.
Ya ce mata biyu da wani ƙaramin yaro na cikin wadanda aka kashe.
Wakilin BBC ya ce har yanzu ba a tabbatar da wadanda ke da Alhakin kai harin ba, amma wani reshen ƙungiyar Islamic State da ke yankin sun sha kaiwa ƴan shi'an da ke Afghanistan hari a baya.
Yankin Yammacin Herat wanda ke kan iyaka da Iran, ya zame gida ga galibin tsirarun musulmi 'yan Shi'a da ke Afghanistan
Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar dai ta ce akwai bukatar daukar matakan gaggawa don tabbatar da tsaron ƴan Shi'a.

Asalin hoton, Getty Images
Daga yau Talata ne al'ummar Zimbabwe suka fara amfani da sabbin takardun kuɗi da tsaba da gwamnati ta ƙaddamar karo na uku cikin shekara 10.
Sabon kuɗin Zig an samar da shi ne domin magance matsalar hauhawar farashi a ƙasar.
Sai dai da alama sabon kuɗin tuni ya fara fuskantar ƙalubale.
Sabon kuɗin da aka zamanantar ya rasa kashi ɗaya bisa huɗu na darajarsa idan aka kwatanta shi da dala a kasuwar ƴan canji.
Takardar kuɗi mafi daraja a ƙasar ita ce Zig 200 wadda a dala ta kai kusan 15.
Mutane na iya cirar adadin da ya kai Zig dubu uku sai kamfanoni da suke da damar cirar Zig dubu 30 duk mako, kamar yadda hukumomi suka ce.
Sai dai sharaɗin da aka gindaya bai shafi ƴan majalisa da kotuna da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ba, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar ta Zimbabwe suka ruwaito.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta kai farmaki kan Hamas a Rafah ba tare da la'akari da ko an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba.
A cikin wata sanarwa daga ofishinsa ya kara da cewa dakatar da yakin kafin cimma burin fatattakar Hamas ba shi da wata ma'ana.
Shugaban hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Philippe Lazzarini ya ce mutane a Rafah na rayuwa cikin dar-dar da tashin hankali.
Ya ce akwai wani babban tashin hankali mai tsanani a yanzu a Gaza.
Domin tambayar da kowa ke yi shi ne ko, e ko a'a, kan batun kai farmakin soji a Rafah, wanda ya danganta ne ga ko an iya cimma yarjejeniyar tsagaita wuta cikin wannan makon.

Asalin hoton, EFCC
Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin alƙali Emeka Nwite ta bai wa hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati izinin rufe asusun bankuna 1146 mallakin mutane da kamfanoni da ake gudanar da bincike a kansu saboda zarginsu da hada-hadar kuɗin waje ba bisa ƙa'ida ba da halasta kuɗin haram da tallafa wa ta'addanci.
Alƙalin ya umarci a rufe asusun bankunan har zuwa lokacin kammala bincike.
Da aka yanke hukuncin kan ƙarar da lauyan EFCC, Ekele Iheanacho ya shigar, alƙalin ya ce binciken da za a gudanar zai ɗauki kwana 90.
Alƙalin ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa asusun bankunan na da alaƙa da mutanen da ke amfani da manhajojin musayar kuɗi na kirifto wajen durƙusar da darajar naira.
Alƙalin ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar alkinta kuɗaɗen a asusun bankunan da aka gano har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan lamarin.
Alƙalin ya kuma ɗage ƙarar zuwa 23 ga watan Yulin 2024.