Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza
Shugaban hukumar ɗaukar ma'aikatan Kano, Dr Umar Shehu Minjibir ya rasu
Asalin hoton, UMAR MINJIBIR/FACEBOOK
Allah ya yi wa shugaban hukumar ma'aikatan jihar Kano, Dr Umar
Shehu Minjibir rasuwa da safiyar Juma'a.
Marigayin mai shekara kimanin 70 wanda kuma tsohon babban sakatare ne sannan shugaban
ma'aikata a jihar Kano ya rasu bayan 'yar jinya da ya yi. Ya rasu ya bar 'ya'ya takwas.
Za a yi jana'izarsa a yau bayan sallar Juma'a a masallacin
Al-furqan da ke birnin Kano.
An janye ƴan sandan da ke samar da tsaro ga hukumar da Muhuyi ke jagoranta
Asalin hoton, FACEBOOK/MUHUYI MAGAJI RIMIN GADO
Babban sufeton ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya janye ƴan sanda kimanin 40 da ke samar wa hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano tsaro.
Matakin ya zo ne bayan binciken badaƙalar kuɗi da hukumar, ƙarƙashin jagorancin Muhuyi Magaji Rimin Gado take yi kan shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa babban sufeton ƴan sandan ya bayar da umarnin janye ƴan sandan ga kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Usaini Gumel.
Wata majiya da jaridar ta ruwaito ta ce wasu cikin ƴan sandan suna taimaka wa hukumar ta yaƙi da rashawa a Kano a binciken da take yi tare da samar da tsaro ga hedikwatar hukumar da sauran dukiyoyin da ake bincike a kansu.
Za a tantance ingancin jiragen sama na cikin gida a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama a Nijeriya za ta gudanar da cikakken bincike don tabbatar da ingancin duka jiragen sama da ke zirga-zirga cikin ƙasar.
Ministan sufuri Festus Keyamo ne ya bayyana haka ga gidan talabijin na Channels ranar Alhamis.
Ya ce baya ga dakatar da kamfanin Dana da kuma binciken da ake yi wa kamfanin, za a gudanar da bincike a kan duka kamfanonin jiragen sama a ƙasar domin tabbatar da bai wa fasinjoji kariya.
A ranar Laraba ne, Keyamo ya ba da umarnin dakatar da kamfanin na Dana inda ya ce abubuwan da suka faru da jirgin a baya-bayan nan sun saka damuwa a zukatan jama'a.
An dakatar da kamfanin Dana kwana ɗaya bayan da jirgin kamfanin ya zame daga kan titinsa a filin jirgin saman Legas.
'Muna ƙoƙarin kamo ragowar fursuna 109 da suka tsere daga gidan yarin Suleja'
Asalin hoton, @BTOofficial/X
Hukumomi a Najeriya sun ce suna aiki tare da jami'an tsaro wajen kamo duka ragowar fursunoni 109 da suka tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja.
Ministan cikin gida, Dakta Olubunmi Tuni-Ojo ne ya bayar da tabbacin lokacin da ya kai ziyara gidan yarin domin duba irin ɓarnar da ruwan sama ya yi wa ginin abin da ya bai wa fursunoni 119 dama ta tserewa ranar Laraba da daddare.
Bayan tserewar fursunonin ne kuma aka yi nasarar kamo 10 a cikinsu.
Tunji Ojo, bisa rakiyar shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali a Najeriya, Halliru Nababa, ya ce gwamnati za ta sauyawa gidan yarin mazauni saboda yadda yanzu ya kasance cikin al'umma.
A cewar hukumomin gidan yarin, wurin na tsakiyar gidajen jama'a kuma an gina shi tun 1914. Ministan ya amince cewa ginin daɗaɗɗe ne.
Minisitan ya ce kafin faruwar lamarin, gidan yarin na ɗaukan fursunoni 499, adadin daya zarce yawan mutum 250 da aka tsara ya ɗauka.
Asalin hoton, @BTOofficial/X
Asalin hoton, @BTOofficial/X
Asalin hoton, @BTOofficial/X
Barka da Juma'a!
Masu bibiyar mu barkan ku da warhaka. Barka da sake kasancewa da ku a shafinmu da muke kawo muku bayanan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.
Da fatan za ku kasance da mu a wannan rana domin ci gaba da kawo muku bayanai kai tsaye.