Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Umar Mikail

  1. Ana fuskantar dogayen layukan mai a wasu jihohin Najeriya

    ..

    Asalin hoton, OTHER

    A baya-bayan nan ana wayar gari da ganin motoci sun kafa layi a gidajen mai yayin da wasu direbobi ke kokawa kan yadda farashin man ya tashi.

    Binciken da jaridar Daily Trust ta yi a Abuja da Kano da Kaduna da Legas ya nuna cewa ana samun dogayen layukan mai a gidajen mai da dama.

    A Abuja, babban birnin Najeriya, galibin gidajen man da ke ƙwaryar birnin ba su da man.

    Daily Trust ta ruwaito cewa wasu manyan gidajen mai sun rufe ƙofa inda suka ce ba su da mai.

    Sai dai a gidajen man NNPCL cikin ƙwaryar birnin, ana samun mai sai dai akwai dogayen layukan motoci.

    Tsirarun gidajen mai da ke da man kuma sun ƙara kuɗi da ya kai N750 kowace lita daya.

    A Kano ma direbobi na shafe tsawon sa'oi a gidajen mai kafin su samu man.

    An fi ganin layukan man a gidajen mai na NNPC da ke kan titin Zariya.

    A jihar Kaduna ma, an ga layukan mai a gidajen da ke sayar da shi.

    Haka batun yake a Legas inda NNPC ke sayar da N560 duk lita ɗaya yayin da manyan dillalan mai ke sayar wa a kan N590 da N610.

    • Ko sabuwar matatar man Dangote za ta magance matsalar man fetur a Najeriya?
  2. Jamus ta kama ƴan Najeriya da ake zargi ƴan ƙungiyar asiri ne

    ..

    Ƴan sandan Jamus sun kama ƴan Najeriya 11 da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne da suke shirya soyayyar ƙarya don yaudara.

    A wata sanarwa da ƴan sandan Bavarian suka fitar, ƴan ƙungiyar asirin ta Black Axe sun aikata manyan laifuka da dama a faɗin duniya.

    Ƴan sandan sun ƙara da cewa ƙungiyar ta mayar da hankali kan ƙulla soyayyar ƙarya da kuma halasta kuɗin haram a Jamus.

    Sanarwar ta ce, "suna yin ɓadda kama, misali suna zuwa da niyyar aure sannan bayan an ɗau wani lokaci ana soyayyar sai su nemi a basu kuɗaɗen yin wasu ɓukatu".

    Ɓangarorin da ƙungiyar take aiki a faɗin duniya sun haɗa da " safarar bil'adama da yaudara da halasta kuɗin haram da safarar miyagun ƙwayoyi".

    Waɗanda aka kama ɗin duka ƴan Najeriya ne kuma ƴan shekaru tsakanin 29 da 53.

    An tsare su a ranar Talata a sumamen da aka kai yankin Bavaria bayan binciken ƴan sanda da aka shafe sama da shekara biyu ana yi.

    Wani binciken BBC da aka ƙaddamar a 2021 kan ƙungiyar asiri ta Black Axe ya zaƙulo shedu da suke nuna ƙungiyar ta shiga harkar siyasa a Najeriya kuma tana aiwatar da kashe-kashe a faɗin duniya.

    • Black Axe: Kungiyar asiri da ta yi dumu-dumu a harkokin siyasar Najeriya
    • Black Axe mafia: Ƴan sanda sun cafke ƴan Najeriya 30 da ke ayyukan asiri a Italiya
  3. Amurka na ganawa da gwamnatin Nijar kan janye dakarunta daga ƙasar

    Amurka ta ce jami'anta na ganawa da sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar domin tattaunawa game da batun janye sojojinta daga Nijar ɗin.

    Hakan ya zo sakamakon makonni da gamayyar ƙungiyar farar hula a Nijar ta shafe tana zanga-zangar goyon bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar ranar 26 ga watan Yuli.

    "Jakadiyar Amurka a Nijar, Kathleen FitzGibbon da Manjo Janar Ken Ekman, Daraktan tsare-tsare da tattaunawa na rundunar tsaro ta Amurka da Afirka za su gana da mambobin Majalisar Tabbatar da Tsaron Ƙasa (CNSP) da ke Yamai," in ji wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar.

    A mako mai zuwa ne, wasu jami'an tsaron Amurka za su kai ziyara Yamai domin tsara yadda za a kwashe sojojin ƙasar cikin mutunci da gaskiya.

    A cewar wata sanarwa, gwamnatin Amurka za ta ci gaba da goyon bayan al'ummar Nijar yayin da suke ƙoƙarin fatattakar mayaƙa.

    Sanarwar ta kuma ce mataimakin sakataren harkokin waje, Kurt M. Campbell zai je Yamai a watanni masu zuwa domin tattauna batun yin haɗin gwiwa a batutuwan da buƙatarsu ta zo ɗaya.

    Sojojin Nijar sun sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro da Amurka yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar ƙaruwar matsalar tsaro da hare-hare daga ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

    Magoya bayan gwamnatin sojoji a Nijar sun ce kasancewar sojoji har da na Amurka da Faransa ba ya tasiri ga tsaron ƙasar.

    A yanzu, sojojin sun ƙulla yarjejeniya da Rasha, a wani mataki da zai faɗaɗa tasirin Moscow a Afrika.

    A makon da ya gabata ne, ƙwararrun sojojin Rasha suka isa Yamai domin horas da dakarun Nijar.

    • Me zuwan kwararrun sojin Rasha jamhuriyar Nijar ke nufi?
    • Me soke yarjejeniyar sojin Amurka da Nijar ta yi ke nufi?
  4. An kama gomman masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An kama gomman masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a jami’o’in Amurka, yayin da tashin hankalin ɗalibai ke ƙaruwa a jami’o’in.

    Lamarin ya fi ƙamari a Jamiar Texas, inda ‘yan sanda a kan dawaki suka hana masu zanga-zangar kafa sansani, sai kuma wadda aka yi a California.

    Wasu na ɗora alhakin a kan masu tsattsauran ra’ayi daga wajen jami’o’in, waɗanda suka yi nasarar kutsawa haraba makarantun.

    Wasu daga cikin jami’an gwamnati na kira da a ɗauki tsattsauran mataki a kan masu zanga-zangar, da cewa masu aƙidar ƙyamar Yahudawa ne.

    • Netzah Yehuda: Bataliyar Isra'ila da Amurka ke neman saka wa takunkumi kan yaƙin Gaza
    • Za a ɗauki shekaru kafin kwance bamabaman da ba su fashe ba a Gaza - MDD
  5. Barka da Hantsi!

    Masu bibiyar wannan shafin na Kai Tsaye barka da safiya.

    Kamar kodayaushe, muna wallafa maku labarai da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya musamman Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Ku kasance da mu tsawon wannan rana domin karanta labaran da suka shafi rayuwarku.

    Za kuma ku iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta.