Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage
CBN ya sake karya farashin dala zuwa N1,021
Asalin hoton, Getty Images
Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,021.
CBN ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da darakta a sashen musayar kuɗi na bankin, Dakta Hassan Mahmud ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce bankin ya tsara sayar da dala miliyan 15.88 ga ƴan canji 1,588 da suka cancanta.
A cewar sanarwar, su kuma ƴan canji ana sa ran su ci ribar da ba ta wuce kashi 1.5 ba cikin 100.
Hakan na nufin za su sayar da dala ɗaya ne a kan N1,117.
Sanarwar na cikin matakan da CBN ke ɗauka domin daidaita kasuwar musayar kuɗi a Najeriya da kuma tabbatar da gaskiya da bin doka a tsakanin masu canjin kuɗi.
Ko sayar wa 'yan canji dala zai iya farfaɗo da darajar naira?
Mutum biyar sun mutu cikin kwale-kwalen ƴan ci-rani
Asalin hoton, PA Media
Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar ranar Talata, in ji hukumomin Faransa.
Masu gadin teku sun ce mutanen da lamarin ya rutsa da su na koƙarin zuwa Birtaniya ne cikin wani kwale-kwale maƙare da ƴan ci-rani 110.
Tuni aka ƙaddamar da aikin ceto domin zaƙulo mutanen da suke cikin ruwa.
Sakataren harkokin cikin gida na Birtnaiyam James Cleverly ya ce: "Dole ne a magance wannan bala'i. Ba zan amince da halin da ake ciki ba da ke janyo asarar rayuka."
Mista Cleverly ya ce gwamnatin Birtaniya tana yin duk mai yiwuwa na kawo ƙarshen miyagu masu safarar mutane."
Tun farko, majalisar dokokin Birtaniya ta amince da ƙudirin neman tura masu neman mafaka a Birtaniya zuwa Rwanda bayan shafe watanni ana ƙiƙi-ƙaƙa a kai.
Kudurin ya ayyana Rwanda a matsayin kasar da ba ta da wata matsala dangane da ƙudurin, bayan da kotun ƙolin Birtaniya ta zartar a watan Nuwamba cewa shirin na gwamnati ya saba doka.
An rufe kantin China kan zargin nuna wa ƴan Najeriya wariya
Asalin hoton, @fccpcnigeria/X
Jami'an hukumar kare haƙƙin masu sayen kayayyaki FCCPC a Najeriya ta garƙame wani kantin sayar da kayayyaki na ƴan China da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Jami'an hukumar ta FCCPC sun rufe kantin ne bayan da suka yi dirar mikiya a wajen ranar Litinin saboda zargin yadda ake nuna wa ƴan Najeriya ƙyama.
Jami'an hukumar sun ɗauki matakin ne bayan da suka yi wa ma'aikatan wurin ƴan Najeriya tambayoyi.
Tun farko, a ranar Lahadi ne al'umma suka bayyana damuwa game da yadda ake hana ƴan Najeriya shiga kantin na China.
Jami'in da ke kula da kantin, Shaibu Sanusi ya tabbatar cewa ƴan Najeriyar da ke aiki a wajen ne kaɗai suke iya zuwa yin siyayya ban da sauran ƴan Najeriya.
Hukumar ta ɗauki matakin ne bayan da jama'a a shafukan sada zumunta suka yi ta cece-kuce game da yadda aka ce kantin ke hana ƴan Najeriya zuwa siyayya.
Asalin hoton, @fccpcnigeria/X
Me ya kamata iyayen yaran da ake cin zali a makaranta su yi?
Jirgin kamfanin Dana ya zame daga kan titinsa
Asalin hoton, DANA AIR
Wani jirgi mallakin kamfanin jirgin sama na Dana ya sauka daga kan titin jirgi a jihar Legas.
Babu cikakken bayani game da haɗarin zuwa yanzu sai dai wata majiya ta shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ba a samu asarar rai ba.
Bobrisky ya ɗaukaka ƙara don ƙalubalantar hukuncin ɗaurin wata shida
Asalin hoton, BOBRISKY INSTAGRAM
Fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta, Idris Olanrewaju Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky ya ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotu da ta same shi da aikata laifuka hudu da ke da nasaba da wulaƙanta takardun naira.
A ƙarar da ya shigar ta hannun lauyansa, Bimbo Kusanu, Bobrisky na neman kotu ta jingine hukuncin wata shida a gidan yari da aka yanke masa tare da neman kotu ta ba shi zaɓin biyan tarar naira dubu 50 kan duka laifukan da aka same da saikatawa.
A ranar 12 ga watan Afrilu nemai shari'a Abimbola Awogboro na tabbatar kotun tarayya a Legas ta yanke wa Bobrsiky hukuncin wata shida a gidan yari ba tare da zaɓi biyan tara ba saboda wulaƙanta naira.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa yayin yanke hukunci, mai shari'a ta ce hukuncin zai zama izina ga sauran mutane da suka saba wulaƙanta naira.
A ranar 5 ga watan Afrilu, Bobrisky ya amsa aikata laifuka huɗu da hukumar EFCC ke tuhumarsa da aikatawa.
Lead British ta ƙaddamar da bincike kan bidiyon cin zalin ɗalibar makarantar
Asalin hoton, LEAD BRITISH INTERNATIONAL SCHOOL ABUJA/FACEBOOK
Hukumar gudanarwar makarantar Sakandare ta Lead British International da ke Abuja, babban birnin Najeriya sun mayar da martani game da wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda ke nuna matsalar cin zali a tsakanin ɗalibai.
Cikin sanarwar da makarantar ta wallafa a shafinta na Fesbuk, sun yi allah-wadai da lamarin inda suka ce sun soma gudanar da bincike a kai.
"Makarantar Lead British na bayyana matuƙar damuwarta kan batun cin zalin da ya bayyana cikin wani bidiyo kuma muna bai wa jama'a da ɗalibai tabbacin cewa za mu ɗauki mataki mai ƙarfi a kai."
Tsokacin makarantar na zuwa ne bayan ɓullar bidiyo da dama a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda ake cin zalin ɗalibai a makarantar.
A cikin bidiyon da BBC ta gani a shafin X, wata ma'abociyar shafin @mooyeeeeeee ta ce tana neman adalci ga wata ɗalibar makarantar da ƴan ajinta suka ci zalinta.
''Yata ta sha suma saboda cin zali da ta yi fama da shi a makaranta'
Najeriya ba ta kai lokacin kafa ƴan sandan jihohi ba – Sifeton Ƴan sanda
Asalin hoton, NPF/X
Babban spetan ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya ce ƙasar ba ta kai ta kafa rundunar ƴan sandan jiha ba duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wani taron tattaunawa game da kafa rundunar ƴan sandan jiha da aka gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar da aka yi wa taken "Hanyoyin samun zaman lafiya: Sake fasalin ƴan sanda a Najeriya".
Babban Spetan ƴan sandan ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai lokacin da za ta kafa rundunar ƴan sandan jihohi ba, in ji shi wanda ya samu wakilcin AIG Ben Okolo a taron da kakakin majalisar wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas ya shirya.
Babban spetan ya ce akwai yiwuwar wuce gona da iri daga gwamnatocin jihohi.
"Gwamnonin jihohi na iya amfani da ƴan sandan domin buƙatarsu ta siyasa ko ta ƙashin kai tare da murƙushe haƙƙoƙin bil adama da tsaro."
Sai dai ya bayar da shawarwari na yadda za a inganta ayyukan ƴan sanda wajen haɓaka tsaro a ƙasar.
"Da farko, hukumar tsaron Civil Defence da hukumar kare afkuwar haɗura su kasance sashe aƙarƙashin rundunar ƴan sandan Najeriya," in ji shi.
A cewar babban spetan, akwai buƙatar a ƙara yawan jami'an tsaron da ake ɗauka aiki duk shekara. Da kuma basu horo, abin da ya ce na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro a Najeriya.
A taron da ya samu halartar manyan jami'ai a Najeriya, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan yana ganin duk da ƙalubalen da ake fuskanta, kafa rundunar ƴan sandan jihohi a Najeriya abu ne na dole.
Ya ce ƙaruwar sace-sacen mutane da sauran laifuka ya sa kafa rundunar ƴan sandan jihohi ya zama wajibi a halin da ake ciki a Najeriya.
Ba ya ga Jonathan, taron ya samu halarta mataimakin shugaban ƙasa Kassim Shettima inda ya bayyana ƙudirin shugaba Bola Tinubu na inganta ayyukan ƴan sanda a ƙasar.
Me kaddamar da dakarun sa-kai da jihohin arewacin Najeriya ke yi ke nufi?
Majalisa ta gayyaci ministan lantarki kan ƙarin kuɗin wuta
Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ya gayyaci ministan lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu da hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasar NERC da su bayyana gabansa a wani zaman bincike da za a yi game da ƙarin kuɗin lantarkin da aka yi a baya-bayan nan.
Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ne ya bayyana haka yayin gudanar da ayyukan kwamitin da kuma kai ziyara zuwa ma'aikatar lantarki da ke Abuja.
Abaribe ya ce majalisar dattawa tuni ta amince a yi zaman ranar 29 ga watan Afrilu inda hukumomin gwamnati za su amsa tambayoyi.
Ministan ya bayyana tarin matsalolin da suka addabi ɓangaren lantarki a Najeriya da suka haɗa da rashin isassun kuɗi da rashin iskar gas inda ya buƙaci kwamitin da ya tallafa wa ma'aikatar lantarki domin cimma ƙudurorinta.
Kwamitin majalisar ya kuma duba wani aikin samar da wuta a harabar ma'aikatar. Sanata Abaribe ya kuma bayyana damuwa kan duk da maƙudan kuɗin da ake zubawa a ɓangaren lantarki, masu ruwa da tsaki na ci gaba da kokawa kan matsalolin da ake fuskanta.
Ya kuma nemi sanin dalilin da ya sa kamfanin samar da wutar lantarki da sauran hukumomi da ke ɓangaren wutar ke bari babban layin wutar lantarki ke yawan lalacewa cikin shekaru.
Yadda cire tallafin lantarki a Najeriya zai shafe ku idan farashin ya ninka uku
Mene ne babban layin wutar lantarki na Najeriya kuma yaya yake aiki?
Barka da Safiya!
Jama'a barkanku da safiya. Muna maku barka da zuwa wannan shafi da muke kawo muku labaran duniya kai tsaye da ɗumi-duminsu daga sassan duniya musamman Najeriya da Nijar.
Sai ku gyara zama don kasancewa da mu tsawon yinin wannan rana ta Talata.