Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Kotu ta gaza saurarar ƙarar EFCC kan hana kama Yahaya Bello

    ..

    Asalin hoton, Yahaya Bello/Facebook

    Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta gaza zaman sauraron ƙarar da hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa ta shigar don ƙalubalantar umarnin wata babbar kotu a Kogi da ta hana ta kama tsohon gwamna Yahaya Bello.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa kotun ta Kogi a hukuncinta na ranar 17 ga watan Afrilu, ta dakatar da EFCC daga kamawa ko tsarewa ko kuma tuhumar Yahaya Bello.

    Alƙali A.A Jamil ne ya bayar da umarnin ranar Laraba a wani hukunci da aka shafe sa'a biyu ana yi a Lokoja, babban birnin jihar ta Kogi.

    Hukuncin ya zo daidai da samamen da jami'an EFCC suka kai gidan Yahaya Bello da ke Abuja a wani yunƙurin cafke shi.

    EFCC na neman gurfanar da tsohon gwamnan kan zargin aikata laifuka 19 da suka shafi halasta kuɗin haram da cin amana da kuma karkatar da kudin da ya kai naira biliyan 80 da ɗoriya.

    EFCC dai na son Bello ya fuskanci shari'a saboda laifin da ake zargin ya aikata abin da ya sa ta shigar da ƙara gaban kotun tarayya a Abuja domin samun izinin kama shi.

    • Abin da masana ke faɗi kan masu hana EFCC ta kama Yahaya Bello
  2. Ƴan bindiga sun harbe farfesan shari'a a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar Farfesa Yinka Olomojobi na sashen koyar da shari'a a jami'ar Babcock da ke Ilishan a jihar.

    Ƴan bindigar da yawansu ya kai takwas ne suka harbe farfesan a ɓangaren shari'a ranar Juma'a.

    Sun kuma sace wasu mutum biyu.

    Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Ogun, Omolola Odutola wadda ta tabbatar da lamarin ta ce maharan sun harbe malamin a ƙirjinsa saboda ƙin yadda a yi garkuwa da shi.

    Ta bayyana cewa an kama mutum ɗaya da hannu a kisan farfesan.

  3. Najeriya ta samu rancen sama da dala biliyan biyu daga bankin duniya

    ..

    Asalin hoton, @FinMinNigeria/X

    Gwamnatin tarayya na sa ran karɓar rancen dala biliyan 2.2 daga bankin duniya da kuma wani tallafin daga bankin raya ƙasashen Afirka, AfDB.

    Ministan kuɗi, Wale Edun ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwa a ƙarshen tarukan bankin duniya da IMF a birnin Washington DC da ke Amurka.

    Da yake magana kan hanyoyin samun kuɗaɗe don tallafa wa tattalin arzikin Najeriya, Edun ya lissafa kuɗaɗen da ƴan Najeriya mazauna ƙetare ke tura wa ƙasar da hannun jari da cibiyoyin bankin duniya da sauran ƙungiyoyin samar da ci gaba na ƙasashen duniya.

    Ya ƙara da cewa Najeriya za ta kuma amfana daga tallafin kasafin kuɗi da yake da kuɗin ruwa ƙalilan daga bankin raya ƙasashen Afirka inda ya ce ana tattaunawa da ƴan ƙasashen waje masu zuba hannun jari.

    Edun ya bayyana cewa kuɗin da ake samu daga man fetur ne babbar hanyar samun kuɗin shiga ga Najeriya sannan ƙudirin shugaban Najeriya Bola Tinubu na ƙara samar da ɗanyen mai daga ganga miliyan 1.6 duk rana zuwa ganga miliyan biyu kowace rana.

  4. Nijar ta yi barazanar ƙwace lasisin haƙar Uranium daga kamfanin Goviex

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomin mulkin sojan Nijar sun bai wa kamfanin Goviex Uranium na kasar Canada wa'adin zuwa farkon watan Yulin wannan shekara na soma aikin hakar Uranium.

    Kamfanin dai ya samu lasisin haƙar makamashin ne kimanin shekaru biyu da suka gabata.

    Gwamnatin ta yi barazanar cewa kodai kamfanin na Goviex Uranium ya fara aikin ko kuma Nijar ta karɓe lasin aikin da ta ba shi.

    Sai dai a cikin wata sanarwa da kamfanin na GOVIEX ya fitar ya ce yana aiki tukuru domin ganin ya kadamar da aikin a lokacin da gwamnatin ta bashi.

    Kamfanin ya ƙara da cewa akwai kimanin guraben aikin 800 da kamfanin zai samar a tsawon shekaru 20 na aikin hakar da zai yi .

  5. Aiyedatiwa ya lashe zaɓen fitar da gwani na APC a Ondo

    ..

    Asalin hoton, Lucky Aiyedatiwa/Facebook

    An sanar da gwamnan jihar Ondo Lucky Orimisan Aiyedatiwa a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar APC takara a zaɓen gwamnan jihar da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.

    An yi zaɓen fitar da gwanin a mazaɓu 203 da ke sassan ƙananan hukumomi 18 ranar Asabar, ban da ƙaramar hukumar Okitipupa wanda aka yi ranar Lahadi.

    An ɗage zaɓen na Okitipupa saboda hargitsi.

    An yi ta tattara sakamakon zaɓe daga ƙananan hukumomi har zuwa safiyar yau Litinin ƙarƙashin kwamitin zaɓe na gwamna Usman Ododo.

    Jami'an zaɓe daga ƙananan hukumomi sun sanar da sakamakon gaban kwamitin mai mutum bakwai.

    Daga bisani kuma aka tattara sakamakon zaɓen baki ɗaya.

    Sakamakon zaɓen ya nuna Aiyedatiwa ya samu ƙuri'a 48,569 sai Samuel Akinfolarin mai ƙuri'u 15,182 da Olusola Oke mai 14,453 sai Jimoh Ibrahim da ya samu 9,457 da Wale Akinterinwa da ya tashi da ƙuri'a 1,952.

    Sai dai wata hatsaniya ta kaure yayin tattara sakamakon zaɓen inda jami'in tattara sakamakon a ƙaramar hukumar Ifedore, Chief Oliver Okpala ya ce babu ɗan takarar da ya samu ƙuri'a saboda ba a yi zaɓe ba.

  6. Mutum bakwai sun mutu bayan motar tsere ta faɗa kan ƴan kallo a Sri Lanka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum bakwai sun mutu, wasu 21 sun ji rauni bayan wata motar tsere ta afka cikin taron masu kallo a wani wurin tseren motoci a Sri Lanka.

    Haɗarin ya faru a tseren motoci na Fox Hill Supercross ranar Lahadi a Diyatalawa, wani gari da ke da sansanin sojoji.

    Cikin waɗanda suka mutu akwai jami'ai huɗu da ƴan kallo ciki har da yarinya ƴar shekara takwas, in ji sojoji.

    Babu cikakken bayani game da direban da yanayin da yake ciki sannan ko zai fuskanci tuhuma.

    Sai dai hukumomi sun ce ana gudanar da cikakken binciken ƴan sanda a haɗarin.

    Kakakin rudnunar ƴan sanda Nihal Talduwa ya ce haɗarin ya faru lokacin da motar ta yi tsalle ta yi gefen hanya, kamar yadda BBC Sinhala ta bayyana.

    A cewar shaidu, haɗarin ya faru ne bayan da wata mota ta yi alkafura.

    Jami'ai sun yi ƙoƙarin rage gudun da motocin ke yi amma da motocin suka wuce da gudu, wata jar mota ta fice daga kan titi tare da faɗa wa kan ƴan kallo a gefen hanya.

  7. Uba da ɗansa da makwabcinsu sun mutu a cikin masai a Kano

    Salga

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi sun tabbatar da mutuwar uba da ɗansa da kuma wani mutum na daban duka a cikin wata shadda a jihar Kano.

    Al'amarin dai ya faru ne ranar Lahadi bayan da wani mutum mai suna Mallam Danjuma Bilack mai shekaru 60, bisa tsautsayi wayarsa ta faɗ cikin shadda, kamar yadda mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusuf ya shaida.

    "Lokacin da ya shiga cikin masan domin ya ciro wayar tasa da ta faɗ sai ɗansa Ibrahim Ɗanjuma mai shekara 35 shi ma ya shiga domin ya taimaka masa to amma dukkannin su biyun suka maƙale a ciki.

    Shi ma wani makwabcinsu mai suna Aminu T Gaye sai ya shiga masan domin kai musu ɗauki inda shi ma ya maƙale a ciki." In ji jami'in kashe gobarar.

    Yusuf ya ƙara da cewa sun samu kiran neman kai ɗauki amma lokacin da suka fito da mutanen uku daga masan tuni hankalinsu ya gushe inda kuma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu a asibiti.

    Har yanzu dai miliyoyin 'yan Najeriya na amfani da masai wajen yin buƙatarsu ta bayan gida sakamakon talauci.

  8. An zaƙulo gawawwaki fiye da 200 daga makeken kabari a Khan Younis – Hamas

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tsaro ta Civil Defence a Gaza ta ce an zaƙulo gawawwaki fiye da 200 daga wani makeken kabari da ke asibitin Nasser a birnin Khan Younis.

    Hukumar - wadda take ƙarƙashin ikon Hamas ta ce gawawwakin na wani ɓangare na asibitin.

    Hukumar ta bayyana cewa wasu a cikin su an kashe su nan take ba tare da yi masu shari'a ba, yayin da wasu kuma aka zaƙulo su tare sannan aka sake binne su a wata maƙabarta ta hukuma da aka haƙa lokacin mamayar Isra'ila.

    Isra'ila ta ce tana nazari kan rahotannin.

    Sojojin Isra'ila sun janye daga Khan Younis makonni biyu da suka wuce bayan tsanantar yaƙi a harabar asibitin.

    • Abin da muka sani game da ƴaƴan shugaban Hamas da Isra'ila ta kashe a Gaza
    • Halin da ake ciki a Gaza wata shida da fara yaƙi
  9. Shugaban sashen tattara bayanan siri na sojin Isra'ila ya yi murabus

    ..

    Asalin hoton, IDF

    Shugaban sashen tattara bayanan sirri na sojin Isra'ila, Manjo Janar Aharon Haliva ya ajiye muƙaminsa bisa bayan ɗukar alhakin gazawa dangane da harin da ƙungiyar Hamas ta kai ƙasar ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

    Rundunar sojin Isra'ila ta IDF ta ce manjo janar Aharon Haliva zai ajiye aikin ne bayan an zaɓ mutumin da zai gaje shi.

    A wata wasiƙa, manjo Aharon ya amince cewa sashensa na tattara bayanan sirri "ba mu sauke nauyin da aka rataya mana."

    Shi ne wani babban mai muƙami da ya fara ajiye aiki tun bayan harin na ranar 7 ga watan Oktoba.

    Sashen tattara bayanan sirri na Isra'ila dai bai iya ko kuma ya yi biris da jerin gargaɗin da ya samu kafin harin da Hamas ta kai ƙasar cewa ɗaruruwan 'yan bindiga sun keta iyakar da ke tsakaninsu da Gaza a ranar inda suka kai hari kan wasu garuruwa da ke makwabtaka da sansanin soji da kuma wurun bukukuwa.

  10. Ƙasashen Afirka na taro kan ta'addanci a Abuja

    ..

    An buɗe taron yini biyu kan yaƙi da ta'addanci a ƙasashen Afirka da ke gudana a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya ƙaddamar da taron mai taken 'ƙarfafa ayyukan haɗin kai tsakanin ƙasashe da bunƙasa hukumomi don murƙushe ta'addanci' wanda ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro ya shirya.

    An shirya taron domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci a tsakanin ƙasashen nahiyar Afirka ta hanyar haɗin kai na sojoji da daƙile kwararar makamai da kuɗade tsakanin ƙasashen da zummar tallafa wa masu aikata manyan laifuka.

    Taron na zuwa ne yayin da ƙasashen Afirka da dama ke fuskantar barazanar tsaro daga ƙungiyoyin masu iƙirarhin jihadi da ƴan bindiga musamman a sassan yankin Sahel.

    Najeriya, wadda ke karɓar bakunci bisa haɗin gwiwar ofishin yaƙi da ta'addanci na majalisar ɗinkin duniya na jagorantar taron daidai lokacin da rundunar sojin ƙasar ta ɗauki alwashin ɗaukan fansa ga kisan da aka yi wa dakarunta shida a wani harin kwanton ɓauna yayin da suka je aikin kwantar da tarzoma a jihar Neja.

    Rundunar ta ce ƴan bindiga ne ke da hannu a kai wa sojojin hari ranar Juma'a da daddare.

    Wasu daga cikin waɗanda za su yi jawabi a taron akwai shugaban ƙungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat da shugaban ECOWAS, Omar Touray da shugaba Bola Tinubu wanda gwamnatinsa ke fama da matsalar tsaro.

    Shugabannin Ghana da Togo sun bi sahun takwaransu na Najeriya, Bola Tinubu a halartar taron. Akwai kuma masana harkar tsaro daga ƙasashen EU da sauran ƙasashen Afirka.

    ..
    ..
    ..
  11. Mambobin Boko Haram sun miƙa wuya ga dakarun MNJTF

    ..

    Asalin hoton, MNJTF

    Rundunar dakarun haɗin gwiwa ta ƙasashe huɗu da ke yaƙi da Boko Haram (MNJTF) da ke Ndjamena na ƙasar Chadi ta bayar da rahoton yadda ƴan ta'adda suke ci gaba da miƙa wuya.

    Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, Laftanal Kanar Abubakar Abdullahi ta ce cikin waɗanda suka ajiye makamansu dun haɗa da wasu matasa biyu da aka bayyana su a matsayin ƙwararru a kwance abubuwan fashewa

    Abubakar Mohammed mai shekara 19 da Bana Modu ɗan shekara 13, sun miƙa wuya a garin Munguno a ranar 21 ga watan Afrilu abin da ya zama nasara a yaƙin da sojoji suke na murƙushe mayaƙan Boko Haram a yankin.

    Cikin kayayyakin da aka gano a wurinsu akwai abubuwan fashewa biyu da wayoyin hannu biyu da kuɗi naira dubu 53.

    ..

    Asalin hoton, MNJTF

  12. An kwashe gomman mutane bayan mummunar ambaliya a China

    ..

    Asalin hoton, XINHUA

    Hukumomi sun kwashe kusan mutum 60,000 daga gidajensu da ke Guangdong yayin da mamakon ruwan saman da aka shafe kwanaki ana yi ya janyo ambaliyar ruwa a lardin da ke da mafiya yawan al'umma a China.

    Mutum 11 ne suka yi ɓatan dabo sai dai ba a bayar da rahoton asarar rai ba.

    Bidiyo daga kafafen yaɗa labaran ƙasar sun nuna yadda ambaliyar ruwan ta shafe wurare inda kuma masu aikin ceto cikin kwale-kwale ke kwashe mutane daga ruwan da tsayinsa ya kai ƙugunsu.

    Manyan kogunan ƙasar sun tumbatsa sannan hukumomi suna sa ido kan lamarin.

    A sassan lardin,. kusan gidaje miliyan 1.16 sun faɗa cikin duhu a karshen mako amma an gyara wutar kashi 80 cikin 100 na gidajen ranar Lahadi da daddare.

    An soke tashin jirage, wasu kuma an jinkirta lokacin tashin su a filin jirgin saman Baiyun da ke Guangzhou saboda ruwan daka ayi ta zabgawa yayin da kuma aka buƙaci makarantu a birane aƙalla uku su rufe.

    Gidaje da dama a sassan lardin ko dai sun ruguje ko kuma sun gamu da ɓarna mai girma, inda hukumomi suka ƙiyasta cewa tattalin arziki ya yi asarar kusan dala miliyan 19.8.

    • Bidiyon yadda ambaliyar ruwa ke gudu da mutane a China
  13. Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin ɗaukar fansar kisan dakarunta shida

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin ɗaukan fansa kan kisan da aka yi wa sojojinta shida bayan yi masu kwanton ɓauna yayin da suka je jihar Neja domin aikin kwantar da tarzoma.

    Sojojin sun je aiki ne ƙauyen Karaga a yankin Shiroro ranar Juma'a inda wasu da rundunar ta kira ƴan ta'adda suka kai masu hari.

    Wata sanarwa daga rundunar sojin ta ce an kashe da dama cikin maharan sannan kuma ana neman wasu a cikinsu.

    Rundunar ta yi alƙawarin ɗaukar fansa kan kisan sojojin.

    Sojojin da aka kashe sun haɗa da manyan jami'an soji biyu da wasu sojoji huɗu, a cewar rundunar.

    Sojoji biyu sun ji rauni a harin.

    Rundunar ba ta tabbatar da rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wani jami'in soji.

    Babu ƙarin bayani game da waɗanda suke da hannu a harin amma ana zargin ƴan bindiga da hannu a kai wa jami'an tsaro hare-hare a baya-bayan nan.

    Harin ya zo ne yayin da Najeriya ke karɓar baƙuncin taron yini biyu kan yaƙi da ta'addanci a Abuja, babban birnin ƙasar.

    Harin kwanton ɓaunan ya so ƴan makonni bayan kisan sojoji 17 a lokacin da suke wanzar da aikin zaman lafiya a tsakanin wasu al'umomi da ba sa ga maciji da juna a jihar Delta.

    Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da suka shafi yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke kai hare-hare a sassan ƙasar sai dai hukumomi sun sha bayyana irin ƙoƙarin da suke na magance ƙalubalen da tsaron ƙasar ke fuskanta.

    • Lokuta biyar da mutanen gari suka yi wa jami'an tsaro kisan gilla a Najeriya
  14. Barka da wannan lokaci!

    Barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a wannan hantsi na Litinin - tushen aiki!

    Nabeela Mukhtar Ubake fatan kun tashi lafiya.

    Za mu kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu daga bisani kuma mu miƙa ragama ga sauran abokan aiki,

    Ku biyo mu.