An ƙona sinadaran haɗa ƙwayar da ake zargi ana haɗawa da ƙasusuwan mutane a Saliyo
Hukumomi a Saliyo sun ƙone sinadaran da ake amfani da su wajen haɗa wani maganin da aka fi sani da kush, wanda kudinsu ya kai dala 200,000 .
Al'amarin ya faru, makwonni niyu bayan shugaba Julius Maada Bio ya ayyana dokar ta-ɓaci kan yawaitar shan muggan ƙwayoyi a ƙasar.
Wakilin BBC ya ce babban sinadarin da ake haɗa Kush da shi, shi ne ƙashin mutum, abin da ya sa hukumomin suka tsaurara tsaro a maƙabartu don hana masu ta'ammali da shi tone ƙaburbura.
Da yake jawabi gabanin ƙone sinadaran a Freetown babban birnin ƙasar, babban jami'in yan sanda mai kula da laifuka Mohamed Alieu, ya ce suna lalata kayan haɗin maganin mayen ne domin gudun kada su sake komawa cikin al'umma.
Kush, wani nau'in ƙwaya ce mai tasiri a jikin mutum kamar tabar wiwi, wadda a yanzu ta zama ruwan dare a Afirka ta Yamma shekaru da dama.

