Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. An ƙona sinadaran haɗa ƙwayar da ake zargi ana haɗawa da ƙasusuwan mutane a Saliyo

    Hukumomi a Saliyo sun ƙone sinadaran da ake amfani da su wajen haɗa wani maganin da aka fi sani da kush, wanda kudinsu ya kai dala 200,000 .

    Al'amarin ya faru, makwonni niyu bayan shugaba Julius Maada Bio ya ayyana dokar ta-ɓaci kan yawaitar shan muggan ƙwayoyi a ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce babban sinadarin da ake haɗa Kush da shi, shi ne ƙashin mutum, abin da ya sa hukumomin suka tsaurara tsaro a maƙabartu don hana masu ta'ammali da shi tone ƙaburbura.

    Da yake jawabi gabanin ƙone sinadaran a Freetown babban birnin ƙasar, babban jami'in yan sanda mai kula da laifuka Mohamed Alieu, ya ce suna lalata kayan haɗin maganin mayen ne domin gudun kada su sake komawa cikin al'umma.

    Kush, wani nau'in ƙwaya ce mai tasiri a jikin mutum kamar tabar wiwi, wadda a yanzu ta zama ruwan dare a Afirka ta Yamma shekaru da dama.

  2. Amurka za ta aike da tallafin soji zuwa Ukraine cikin mako guda

    Jami'an Amurka sun ce ƙunshin taimakon soji zai isa Ukraine cikin mako guda mai zuwa, bayan majalisar wakilai ta amince da tallafin dala biliyan sittin wanda ya haɗa da harsasai a ranar Asabar bayan shafe watanni ana kai ruwa rana.

    'Yan jam'iyyar Democrat da masu matsakaicin ra'ayi daga jam'iyyar Republican sun yi haɗin gwiwar wucin gadi don ganin ba a samu koma baya ba a taimakon da Ukraine take buƙata.

    Kakakin jam'iyyar Republican, Mike Johnson ya raba gari da masu sukar ƙudirin a jam'iyyarsa don tabbatar da dokar.

    Shugaba Joe Biden ya ce zai rattaɓa hannu kan buƙatar nan take, da zarar hakan ta faru kuma za a fara aika wa Ukraine da taimakon sojoji cikin gaggawa.

    Shugaban na Amurka ya ƙara da cewar ƙuri'ar ta aike da saƙo ƙarara game da shugabancin Amurka a fagen duniya.

    Mista Biden ya kuma buƙaci majalisar dattawan Amurka - wadda ake sa ran za ta amince da ƙudirin - ta gaggauta aike masa da shi domin ya saka hannu ya zama doka don gaggauta aika makamai zuwa Ukraine.

    Sakatare janar na ƙungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana farin cikinsa game da zartar da ƙudirin wanda ya ce ya tabbatar da haɗin kan ƙasashen ƙungiyar.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da hutun ƙarshen mako,

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan kasancewa da ku a wannan shafi, don kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tamka muhawa kan labaran da muke wallafawa.