Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Miliyoyin mutane aka nemi su zauna cikin shiri a kudancin China saboda wata ambaliyar ruwa da ake tsammanin za ta ƙazanta nan gaba.
Masu hasashen yanayi sun ce wani kogi ne a lardin Guagdong zai yi cikar da bai fi sau daya yake irinta ba cikin shekaru 100.
Duk da cewa babu rahoton mutuwa zuwa yanzu, amma ana tsammanin mutane da dama ne suka maƙale a cikin wurare masu yawa saboda zabtarewar ƙasa.
Ambaliyar dai ta janyo tsaiko a harkokin sufuri a ƙasar.
Mutum bakwai sun mutu a Sri Lanka yayin wata gasar tseren mota da aka gudanar a Diyatalawa.
Hukumomi sun ce sama da mutum a 20 sun jikkata yayin da motocin tseren suka kwace suka yi kan 'yan kallo.
Sojoji ne suka haɗa wannan gasa domin sadar da zumunta.
'Yan sanda sun ce har da wata yarinya 'yar shekara takwas cikin wadanda suka mutu.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ci gaba da kai wa Hamas hari ita ce hanya ɗaya da za ta taimaka wajen kwato Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su.
A yayin wani saƙo da ya aika lokacin bikin Yahudawa na Pasova, Netanyahu ya yi alƙawarin ci gaba da kai wa Hamas hari da duka ƙarfinsa.
Bai bayyana matakin da zai ɗauka ba a nan gaba, amma ya yi ta maimaita cewa sojoji za su kai hari birnin Rafah da ke kudanci, inda miliyoyin Falasɗinawa da rikicin ya raba da muhallansu ke fakewa.
Iyalan waɗanda ake riƙe da 'yan uwansu sun yi bikin ne da zanga-zanga a ƙofar gidan Netanyahu, suna sukar yadda yake tafiyar da lamarin.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami'anta guda shida na shiya ta ɗaya, bayan wani harin kwantan-ɓauna da wasu 'ƴan bindiga suka kai musu yayin da suke sintiri a kauyen Karaga da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama`a na sojojin Najeriya, Birgediya-janar Onyema Nwachukwu Daraktan ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a, 19 ga watan Afrilu, 2024.
Nwachukwu ya ce duk da koma bayan da sojojin suka samu, sun yi artabu da ‘yan bindigar inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da ƙwace kayan aikinsu.
"Al'amarin abin takaici ne. Babban hafsan sojin ƙasan ya jajanta wa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu," in ji Nwachukwu.
Ya ce sojojin za su mayar da martani kan kisan jami'an nasu.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu sojoji suna bin wasu daga cikin ‘yan bindigar da suka tsere bayan arangamar.
TikTok ya ce yiwuwar dakatar da manhajarsa a Amurka "zai cutar da 'yancin faɗin albarkacin baki" na Amurkawa miliyan 170.
Majalisar wakilan Amurka ta kaɗa kuri'a a ranar Asabar don dakatar da TikTok idan mamallakin manhajar bai yanke hulɗa da China ba.
Dokar dai wani ɓangare ne na tsarin manufofin ketare na Amurka wanda ya haɗa da taimako ga Ukraine kuma za ta iya zama doka nan da mako mai zuwa.
A cikin 'yan watannin nan, jami'an Amurka sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da TikTok.
Suna da'awar cewa ana ganin kamfanin da ya mallaki TikTok, Bytedance a cikin Beijing - zargin da TikTok ya sha musantawa.
Ƴan bindiga sun kashe mutum aƙalla uku yayin da wasu da dama suka samu raunuka bayan wani hari da suka kai a wata kasuwa a garin Tsafe, a karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara.
Wani ganau ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi wa kasuwar dirar mikiya ne da misalin karfe 11 na safiyar yau Lahadi inda suka buɗe wuta kan ‘yan kasuwar.
Kakakin ‘yan sandan jihar ta Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels kai harin, inda ya ce kawo yanzu ba a tantance waɗanda harin ya shafa ba.
Abubakar ya ce an tura sojoji da ‘yan sanda zuwa wajen da lamarin ya faru domin fatattakar ‘yan bindigar da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Mazauna garin na Tsafe sun ce dakarun Hadarin Daji da aka tura zuwa yankin sun fafata da ƴan bindigar tare da tilasta musu tserewa zuwa cikin daji.
Wani ma'aikacin jirgin ruwan Japan ya rasa ransa yayin da wasu bakwai suka yi ɓatan-dabo, bayan faɗowar wani jirgin mai saukar ungulu a tekun Pacific.
Jirgin ruwan mai laƙabin Sikorsky Seahawk na tsaka da atisayen yaƙi da jiragen ruwa cikin dare a kusa da tsibiri Izu kilomita 600 kudu da Tokyo kafin a daina ganinsa.
Ministan tsaron Japan Minoru Kihara, ya bayyana cewar akwai alamun jiragen biyu sun yi taho mu gama da juna, bayan an gano 'ɓaraguzan na'urar adana bayanan jiragen.
An tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin ma'aikatan jirgin bayan an tsamo shi daga ruwa.
Ministan tsaron ya ƙara da cewa za su ci gaba da laluɓen mutane bakwai da suka ɓace.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai buɗe taron yaƙi da ta'addanci na Afirka da za a gudanar a Abuja fadar gwamnatin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce taron - wanda Najeriya da haɗin gwiwar ofishin yaƙi da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya suka shirya - za a fara shi ranar Litinin 22 ga watan Afrilu.
Manufar taron ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta'addanci a ƙasashen Afirka tare da sake fasalin yadda duniya ke kallon ta'addanci a Afirka, da kuma lalubo sabbin hanyoyin magance matsalar a faɗin nahiyar.
Ana sa ran shugabannin gwamnatoci da manyan jami'an gwamnatocin ƙasashen Afirka, da wakilan ƙungiyoyin duniya da cibiyoyi, da jami'an diplomasiyya da ƙungiyoyin fararen hula za su halarci taron.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed za ta halarci taron.
''Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu, da sakataren sashen yaƙi da ta'adancin na Majalisar Dinkin Duniya, Vladimir Voronkov, za su gabatar da jawabai a wurin taron'', kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
Ɗaruruwan mutane ne suka gudanar zanga-zanga a Agadez da ke arewacin Nijar, don matsa wa Amurka lamba ta kwashe dakarunta 1,000 da ke aikin yaƙi da masu iƙirarin jihadi a ƙasar.
A ranar Juma'a ne Amurka ta sanar da amincewa da janye dakarun nata.
Nijar ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka ta Yamma da shugabannin mulkin sojinsu ke raba gari da ƙasashen Yamma tare da ƙulla alaƙa da ƙasar Rasha.
A baya Amurka ta kasance babban ƙawar Nijar wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi.
A yayin da Amurka ke shirin rufe sansaninta na jirage marasa matuƙa, Rasha ta fara kai sojojinta da kayan aiki zuwa Nijar.
Haka ma a makwabtan ƙasar Mali da Burkina Faso sojojin da suka yi juyin mulki na ƙoƙarin ƙulla ƙawance da Rasha.
Hakan na zuwa ne a yankin da masu iƙirarin jihadi ke cin karensu babu babbaka, inda suka raba miliyoyin mutane da muhallansu.
Gwamnan jihr Borno, Babagana Umara Zulum ya ce dole ce ta sa gwamnatinsa ke yawan rabon tallafin abinci ga mabuƙatan jihar.
Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X ya ce gwamnatinsa na rabon tallafin ne domin magance wahalhalun da mutane suka shiga sakamakon rikicin Boko Haram, amma buƙatar gwamnatinsa shi ne kawo ƙarshen matsalar baki-ɗayanta.
Zulum ya ce yayin da gwamnatinsa ke raba tallafi ga mabuƙata da mutanen da rikicin Boko Haram da ya shafe fiye da shekara 10 ya shafa, a gefe guda kuma gwamnatin ta samu gagarumar nasara a wasu fannonin da suka shafi kiwon lafiya, da ilimi da tsaro da kuma ababen more rayuwa a jihar.
Gwamnan ya ce gwamnati na rabon tallafin ne domin rage raɗaɗi ga mutanen da suka rasa sana'o'insu sakamakon ayyukan ƙungiyar Boko Haram.
Mista Zulum ya kuma jaddada buƙatar samar da wata gidauniya da za a jima ana mora har na dogon zango, maimakon moro na lokaci guda, kamar rabon tallafi.
“Ba wai muna sa mutane su riƙa dogara da tallafin ba ne, kuna ganin ƙoƙarin da muke yi wajen farfaɗo da fannin noma, mutane su fahimci cewa dole ce take sa muke wannan abu. Mukan raba tallafi ne kawai ga mutanen da rikicin ya ɗaiɗaita, kuma sannu a hankali muna samun ci gaba'', in ji shi.
Gwamnan ya kuma duba yadda aka raba tallafin kayan abinci da wanda ba na abinci ba da kudin da suka kai naira miliyan 25 ga fiye da iyalai 25,000 a Gajiram, da ke ƙaramar hukumar Nganzai
An gudanar da jana'izar babban hafsan tsaron ƙasar kenya, Janar Francis Ogolla a garin Siaya da ke yammakin ƙasar.
A saƙonsa na ta'aziya, shugaban ƙasar, William Ruto ya ce Kenya ta yi rashin mutum jajirtacce mai kima.
Janar Ogolla ya mutu ne sakamakon hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi ranar 18 ga watan Afrilu.
Hatsarin jirgin - da ya auku a yankin da ke fama da ayyukan 'yan fashin daji - ya yi sanadin mutuwar wasu jami'an sojin tara.
Shugaba Ruto ya ƙara da cewa za a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin jirgin saman.
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wasu mutane da ta shafe wata biyu tana farautarsu bayan da ta zarge su da ƙwarewa wajen safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu da Mozambique da ƙasashen Turai da Amurka.
Cikin wata sanarwa da hukumar ke fitarwa mako-mako, da mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya aike wa da BBC ya ce hukumar ta kama mutanen ne bayan kama wata hodar ibilis mai yawa a filin jirgin sama na Legas.
Sanarwar ta ce hukumar samu nasarar kama biyu daga cikin mutanen da ta jima tana nema ruwa-a-jallo, watao Onyinyechi Irene Igbokwuputa da kuma Frankline Uzochukwu ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu a filayen jirgin saman Legas da na Awka.
Sai kuma Osita Emmanuel Obinna wanda ta kama shi a birnin Legas.
Hukumar ta NDLEA ta kuma ce takama wani mutum da ya yi yunƙurin fita da tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 9.80, daga Najeriya zuwa ƙasar Oman.
''Bayan hukumar ta kama shi ya bayyana cewa an ƙulla yarjejeniyar cewa za a biya shi naira miliyan 1,200,000 idan har ya fitar da tabar zuwa Oman'', in ji sanarwar.
Babafemin ya kuma ce a ranar 20 ga watan Afrilu hukumarsa ta kama wani direban mota a Girei kan hanyarsa ta zuwa Mubi, inda jami'an hukumar suka kama ƙwayar 'opioids' da ke sa maye da yawanta ya kai miliyan 1,250,000 mai nuyin kilogiram 450.
Wasu alƙaluma daga ƙungiyar 'Joint Organizations Initiative' (JODI) sun nuna cewa adadin man fetur da Saudiyya ke fitarwa ya ƙaru a watan Fabrairu zuwa ganga miliyan 6.317 a kowace rana, saɓanin yadda yake a watan Janairu.
Saudiyya da sauran ƙasashe mambobin OPEC sun bayar da rahoton alƙaluman man da suka fitar ga ƙungiyar JODI, wanda ta wallafa a shafinta a intanet, kamar yadda Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito.
Wanda rahoton ya nuna cewa man da ƙasar Saudiyya ke fitarwa ya ƙaru da ganga miliyan 9.01 a kowace rana.
Alƙaluman sun kuma nuna cewa man da matatun man Saudiyyar ke tacewa ya ƙaru daga ganga 250,000 a kowace rana zuwa ganga miliyan 1.675 a kowace rana.
Hotunan tauraron ɗan'adam da aka fitar cikin kwana guda sun nuna shaidar yiwuwar ɓarnar da aka yi wa sansanin sojin saman Iran, bayan harin da Isra'ila ta kai da asubahin ranar Juma'a.
Sashen bin ƙwaƙwaf na BBC, ya yi nazarin hotunan waɗanda suka nuna yadda aka lalata wani sashe na sansanin sojin saman da ke filin jirgin saman Isfahan.
Jami'an Amurka sun ce Isra'ila ta ƙaddamar da harin makamai mai linzami, duk kuwa da cewa ita Isra'ila ba ta tabbatar da hakan ba.
Takun saƙa tsakanin ƙasashen biyu da ke gaba da juna na ci gaba a ruruwa a makonnin baya-bayan nan.
Tun da farko wani hari da ake zargin Isra'ila ce ta kai ofishin jakadancin Iran a Syria a farkon watan da muke ciki, ya sa Iran ta mayar da martani zuwa Isra'ila ranar 13 ga watan Afrilu.
Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fitar da gwanin gwamnan jihar Ondo na jam'iyyar APC, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kogi Alhaji Usman Ododo ya ce jam'iyyar za ta ci gaba da gudanar da zaɓen fitar da gwanin a ƙaramar hukumar Okitipupa a yau Lahadi.
A ranar Asabar ne dai jam'iyyar ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin gwamnan a faɗin jihar.
Cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar ya ce ya samu rahoton gudanar da zaɓen fitar da gwanin a mazaɓu 203 na ƙananna hukumomin jihar 18.
Sai dai gwamnan na Kogi ya ce bayan samun sahihan rahotonnin da ke nuna cewa ba a gudanar da zaɓen a ƙaramar hukumar Okitipupa ba, kwamitin ya ɗauki matakin gudanar da zaɓen a mazaɓu 13 na ƙaramar hukumar a yau Lahadi.
Usman Ododo ya ce za a gudanar da zaɓen a ƙaramar hukumar da tsakar ranar Lahadi, kafin a fara tattara sakamakon zaɓen.
Gwamnan ya kuma yaba da yadda aikin zaɓen fitar da gwanin ke gudana a faɗin jihar.
Hukumar zaɓen ƙasar INEC dai ta ce cikin watan Nuwamba mai zuwa ne za ta gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ondo.
Nan gaba a yau ne za ayi jana'izar babban hafsan sojin Kenya, Janar Francis Ogola, da ya mutu a hatsarin jirgin sama ranar 18 ga watan Afrilu.
Za a gudanar da jana'izar ne a mahaifarsa da ke yankin Siaya a yammacin ƙasar.
Janar Ogola ya mutu ne sakamakon hatsarin jirgin sama a yankin Kabem.
Tuni aka mayar da gawarsa yankin Ng'iya da ke mazaɓar Alego Usonga, inda kuma za a ajiye ta a harabar wata makaranta domin yin bankwana da ita.
Rundunar sojin saman ƙasar ce ta shirya jana'izar babban hafsan sojin, wanda ya kasance matuƙin jirgi a rundunar sojin saman ƙasar.