Wani ɗan Najeriya da ya ƙware a wasan dara, Tunde Onakoya na ƙoƙarin kafa tarihi na nuna bajinta a wasan dara.
Ya ƙuduri aniyar shafe sa'a 58 yana wasan tare kuma da amfani da damar wajen tara dala miliyan ɗaya da zai bayar ga mabuƙata.
Kuɗin, a cewarsa, zai taimaka wa ilimin wasan dara ga miliyoyin yara.
Ɗaruruwan magoya baya sun yi dafifi a dandalin Times Square da ke New York a Amurka domin nuna masa goyon baya ciki har da fitaccen mawaƙin Najeriya, Davido.
Ƴan Najeriya da ke New York sun kasance tare da Onakoya inda suke ƙara masa ƙwarin gwiwa ta hanyar saka kiɗe-kiɗe da kuma rarraba abincin gargajiya na Najeriya har da shinkafa dafa-duka.
A Najeriya ma, mutane na nuna goyon bayansu ga Onakoya yayin da suke kallon yadda yake nuna bajinta a ƙoƙarin kafa tarihi ta manhajar Twitch.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya wallafa saƙon goyon baya ga Mista Onakoya a shafinsa na intanet inda ya ƙara ƙarfafa masa gwiwa da neman ya ƙara fito da Najeriya a idon duniya.
Shi ma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya faɗa wa Onakoya cewa yunƙurin da yake "babbar manuniya ce cewa ɗaukaka na iya zuwa daga ko ina."
Zuwa ƙarfe 3:00 agogon New York ne Mista Onakoya ya shafe sa'a 39 yana wasan na dara kuma ya tara fiye da dala dubu 42.
Waɗanda ke riƙe da kambun, Hallvard Haug Flatebo da Sjur y Ferkinstad sun shafe sa'a 56 da minti tara da sakanni 37 suna wasan dara a 2018.
-
Me ya sa ƴan Najeriya ke rige-rigen shiga Kundin Bajinta na Guiness?