Farashin man fetur da na zinare sun yi tashin gwauron zabi bayan da jami'an Amurka suka ce Isra'ila ta kai wa Iran hari da makami masu linzami inda danyen mai nau'in Brent ya haura dala 90 kan ganga guda kafin ya ja da baya yayin da Iran ta rage tasirin lamarin.
Farashin zinare kuma ya kai kusan dala 2,400 a kan kowane ma'auni guda ɗaya.
Akwai fargabar ɓarkewar rikici a Gabas ta Tsakiya na iya kawo cikas ga samar da mai.
Masu zuba jari suna zuba ido sosai kan matakin da Isra'ila ta ɗauka game da harin da Iran ta kai mata da jirage marasa matuka da makamai masu linzami a ƙarshen makon da ya gabata.
Farashin mai ya tashi da kusan kaso 3.5 da farko amma kuma ya faɗi daga baya zuwa dala 87 kan ganga guda daga dala 90 bayan da kafar yaɗa labaran Iran ta yi ikirarin cewa babu ɓarna a lardin Isfahan inda aka samu rahotannin fashewar abubuwa.
Ci gaban tashin farashin mai na haifar da hauhawar farashin kayayyaki.
Ƙasashe sun dogara kacokan kan kayayyakin da ake amfani da su wajen samar da mai kamar man fetur da dizal.
Farashin man fetur da makamashi sun kasance babban abin da ke haifar da tsadar rayuwa a duniya a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Randeep Somel, manajan asusu a M&G Investment Management a tattaunawarsa da BBC ya nuna damuwarsa game da hauhawar farashin kayayyaki, musamman yadda hauhawar farashin kayayyaki na Burtaniya ya kasance sama da abin da Bankin Ingila ke son cimma na kashi 2 cikin 100.
"A Burtaniya, hauhawar farashin kayayyaki har yanzu yana kusa da kaso 3.2 inda har yanzu ba a kai ga cimma burin ƙasar ba - kuma ya zama abin damuwa ga masu tsara manufofi," in ji Mista Somel
Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo zuwa dala 125 a cikin wannan lokacin, wanda ya haifar da tsawaita wahalhalun kudi ga masu sayen kayayyaki.