Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and A'isha Babangida

  1. Shaƙiyanci na neman kunno kai a siyasar Kano – Ganduje

    ..

    Asalin hoton, Ahmad Dahiru/Fb

    Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce har gobe shi ne shugaban jam'iyyar APC duk da hukuncin da alƙalin babbar kotun jihar Kano ya zartar na cewa ya daina bayyana kansa a matsayin mamba a jam’iyyar.

    Tsohon gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje ya ce sun rubuta takardar koke kan alƙalin da ya tabbatar da dakatarwar da aka yi masa tare da sanar da jami’an tsaron ƙasar cewa wanda ya bayar da sanarwar dakatar da shi cewa sojan gona ne.

    Ya shaida wa BBC cewa "abubuwan da suke faruwa abubuwa ne waɗanda dole sai mun tashi sosai da sosai domin sabon shaƙiyanci ne yake nema ya shiga dimokraɗiyya a Najeriya musamman a jihar Kano."

    Ga tattaunawar da wakilinmu Khalifa Shehu Dokaji ya yi da tsohon gwamnan Kano, Ganduje.

    Bayanan sautiDanna hoton domin sauraron tattaunawar
    • Ban taɓa wani abu don cutar da Ganduje ba, kuma ba zan yi ba - Kwankwaso
  2. Kotu ta tsare mutum 29 da ake zargi da fafutukar kafa ƙasar Yarabawa

    ..

    Kotun majistre ta Iyaganku da ke Ibadan ta bayar da umarnin a tsare mutum 29 da ake zargin masu fafutukar kafa ƙasar Yarabawa ne saboda yadda suka yi wa harabar sakatariyar jihar Oyo ƙawanya.

    A ranar Laraba ne aka gurfanar da mutanen saboda zargin su da hannu a harim da suka kai kan sakatariyar da kuma ofishin gwamna da bai yi nasara ba.

    A baya-bayan nan ne wasu mutane da suka rufe fuskarsu suka yi dirar mikiya a sakatariyar jihar inda suka kafa tutarsu kafin jami'an tsaro su tarwatsa su.

    A cewar jaridar Vanguard, mutanen waɗanda ke fuskantar tuhume-tuhume bakwai kan haɗa baki da cin amanar ƙasa da kuma shiga haramtacciyar ƙungiya da riƙe makami cikin jama'a da kuma aikata abin da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya da mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba.

    Mutanen da ake zargi, har da wata matashiya da manyan mata biyar, an tsare su a gidan gyaran hali da ke Ibadan bisa umarnin babban majistare, Olabisi Ogunkanmi.

    Daga bisani kuma mai shari'ar ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 1 ga watan Agusta.

    • Su wane ne masu fafutukar kafa ƙasar Yarabawa zalla a Najeriya?
  3. Assalamu Alaikum

    Muna yi maku barka da wannan lokaci.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma wasu sassan duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.