Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, A'isha Babangida, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage
Ana jiran fara zaman sauraron shari'a kan tuhumar da ake yi wa Ganduje
Kamar yadda muka faɗa maku a baya, a yau ne ake sa ran kotu za ta soma sauraron ƙarar da gwamnatin Kano ta shigar kan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje game da tuhume-tuhumen da ake masa.
Wakilin BBC da ya isa harabar kotun ya ruwaito cewa ana zaman jiran soma sauraron ƙarar kasancewar i zuwa lokacin da ya turo rahoton, mai shari'ar bai isa kotun ba.
Zuwa yanzu dai babu tabbas ko wanda ake ƙara zai halarci zaman kotun kuma zuwa lokacin rahoton, ba a ga fuskokin lauyoyin Ganduje ba.
Za mu fara bai wa ɗalibai miliyan 1.2 bashin karatu - gwamnatin Najeriya
Asalin hoton, TINUBU FACEBOOK
Akalla matasa miliyan 1.2 ne za su fara cin gajiyar shirin bai wa ɗalibai bashin karatu da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɓullo da shi.
Ana sa ran tsarin shiga cikin shirin, wanda Shugaba Tinubu ya amince da shi a ranar 3 ga Afrilu, zai fara "nan ba da jimawa ba," kamar yadda Akintunde Sawyer, Manajan Darakta da kuma Babban Jami'in Gudanarwa na Asusun ba da bashi na Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana.
A ƙarkashin wannan shiri, kashi ɗaya cikin dari na kuɗaden shiga na shekara-shekara na Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) za ta ɗauki nauyin shirin.
Tare da shirin samun kudin shiga na Naira tiriliyan 19.4 da aka ware wa FIRS a bana, za a iya ware makudan Naira biliyan 194 a matsayin bashin da za a baiwa daliban da suka cancanta.
Sharuɗɗan biyan bashin sun nuna cewa za a fara biyan bashin shekaru biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC).
Sawyer ya zayyana tsarin rajistar, wanda ya nuna cewa wadanda za su ci gajiyar shirin za su bukaci bayar da lambar jarabawarsu ta JAMB, da Lambar Shaida ta Kasa (NIN), da Lambar Tabbatar da Banki (BVN) don neman rancen.
Bugu da ƙari, ɗaliban da suke neman rancen dole ne su ba da cikakkun bayanan karatun su.
"Ga wadanda suka yi nasara samun rancen, za mu biya cikakken adadin kuɗaɗen makarantarsu kai tsaye ga jami'o'in da suke karatu."
“Haka kuma za a biya daidaikun mutane alawus na amfanin yau da kullum don kula da kansu ta yadda za su iya yin abubuwan."
“Za su iya amfani da alawus ɗin don tabbatar da cewa akwai isassun dama a gare su don tsira daga wahalar da ɗalibai ke fuskanta."
Burin Shugaba Tinubu game da shirin ya kunshi kuma yana da nufin fadada hanyoyin ilimi ga ‘yan Najeriya da dama.
Kamar yadda Sawyer ya jaddada, an tsara shirin ne don samun damar shiga da kuma tabbatar da cewa ɗalibai daga sassa daban-daban za su iya cin gajiyar damar samun yin karatu.
Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
Ko bashin karatu na gwamnatin Najeriya zai magance matsalar ilimi?
Mun gabatar da tuhume-tuhume takwas kan Ganduje – Muhuyi Magaji
Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce sun suna yi wa tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje tuhume-tuhumen guda takwas.
A cewar Muhuyi tuhume-tuhumen sun haɗa da waɗnda suka danganci shigar kuɗi kimanin naira miliyan ɗari shida daga asusun gwamnatin Kano zuwa wani kamfani "wanda tsohon gwamna yake darakta a wajen sannan wanda yake tasarrafi da asusun mai ɗakinsa ce take yi"
Nan gaba a yau Laraba ne dai ake sa ran za a fara sauraron ƙarar da gwamnatin Kano ta shigar kan tsohon gwamnan jihar da iyalansa da wasu makusantansa bisa zargin cin hanci da rashawa da almundahana da dukiyar al’umma.
A na sa ran a gudanar da zaman fara sauraron shari'ar ne ƙarƙashin mai shari'a Usman Na'abba na babbar kotu mai lamba huɗu da ke jihar.
Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce akwai ƙari cikin waɗanda ake ƙara da suka haɗa da mutum huɗu da wasu kamfanoni.
A cewarsa, sun shirya gabatar da shaidu 15 da za su gabatar gaban kotu saboda "mun samo hujja da ta danganta tsohon gwamna da laifuffuka da dokar hukuma ta haramta."
Muhuyi Magaji ya ce akwai tuhume-tuhume takwas da suke yi kan tsohon gwamna Ganduje.
Sai dai wasu na ganin matakin gurfanar da tsohon gwamnan Kano da iyalinsa da hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano ke yi masu yunƙuri ne na ramuwar gayya kan dakatarwar da Ganduje ya yi wa shugabanta - Muhuyi Magaji, zargin da ya musanta.
Ya bayyana cewa "shi ne dalilin da ya sa aka dakatar da ni tun farko, abu ne da muka fara shi tun yana gwamnati kuma ƴan jarida sun faɗa muna bincike kan wasu abubuwa da iyalinsa suke, kuma su ba su ƙaryata ba, babu wanda ya fito daga gwamnati ya ƙaryata,"
"Kuma abin da aka ce an dakatar da ni a kan shi, ba a iya tabbatar da shi ba har kotu ta ce mu dawo." a cewar Muhuyi.
Ya ce akwai ƙarar da ke gabansu "wadda muka gano kuɗin ƙananan hukumomi, naira miliyan dubu 51 da miliyan 300."
Game da wannan zargi na Muhuyi Magaji, lauyan tsohon gwamna Ganduje, Barista Musa Lawan ya ce ba za su halarci zaman kotun ba saboda har izuwa lokacin da BBC ta tattauna da shi, ya ce ba su samu takardar gayyata ba.
Abu huɗu da Muhuyi zai binciki gwamnatin Ganduje a kai
Sakataren harkokin wajen Birtaniya ya isa Isra'ila don tattaunawa kan harin Iran
Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Lord Cameron, ya isa Isra'ila, domin tattaunawa kan martanin da ƙasar ta kai dangane da harin da Iran ta kai mata a baya-bayan nan da jiragen yaƙi mara matuki da makami mai linzami.
Ana sa ran zai gana da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ya yi alkawarin mayar da martani bayan harin.
Wannan ziyarar ta zo dai-dai da kokarin da Birtaniya da sauran ƙasashe ke yi na kawar da tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
Firaiministan Birtaniya, Rishi Sunak ya jaddada buƙatar kwantar da hankalula a tattaunawar da Netanyahu.
Harin na Iran ya haɗa da jiragen sama marasa matuka 300 da makamai masu linzami da aka nufa kan Isra'ila.
Harin dai martani ne kai tsaye ga harin da aka kai Syria a ranar 1 ga Afrilu, wanda ake dangantawa da Isra'ila, wanda ya yi sanadin mutuwar manyan sojojin Iran.
MDD za ta ƙaddamar da asusun neman taimako ga Falasɗinawa a Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ƙaddamar da asusun neman taimako na kusan dala biliyan uku, domin samar da kayan agaji ga al'ummar Falasɗinawa a Gaza da yankin Gaɓar Yamma da Isra'ila ta mamaye.
Shugaban hukumar jin-ƙai ta majalisar wadda ke kula da yankunan Falasɗinawa, ya ce, za a yi amfani da kashi 90 cikin ɗari na kuɗin a Gaza, yayin da ma'aikatan agaji ke ta faman kare faɗawar yankin cikin yanayi na yunwa, musamman ma a yankin arewaci.
Ya ce yayin da ake shigar da ƙarin manyan motoci maƙare da kayan abinci zuwa yankin, ya zama wajibi a sake gyara cibiyoyin samar da ruwa da na kula da lafiya da aka lalata sakamakon yaƙi da Isra'ila.
Tun farko, ofishin kula da haƙƙoƙin bil adama na MDD ya ce Isra'ila ta ci gaba da ƙaƙaba abin da ta kira takunkumai ba bisa ƙa'ida ba kan rarraba kayan jin ƙai a Gaza - wani abu da gwamnatin Isra'ila ta musanta.
Hankalin duniya ya karkata kan martanin da Isra'ila za ta mayar wa Iran
Barka da Hantsi!
Daga nan BBC Hausa muke yi muku barka da warhaka.
Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.
Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.