Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, A'isha Babangida, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Waɗanda suka dakatar da Ganduje ba ƴan APC ba ne – Abdullahi Abbas

    Jam'iyyar APC a jihar Kano ta ce za ta ɗauki mataki kan ɓangaren da ya sanar da dakatar da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa na riƙo, Abdullahi Umar Ganduje.

    A ranar Litinin ne wani reshen mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ya sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar ta kasa, daga bisani kuma shugaban jam'iyyar APC din a matakin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ya yi watsi da matakin.

    Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Abdullahi Abbas ya yi zargin cewa waɗanda suka dakatar da Ganduje makusanta ne ga wasu masu riƙe da muƙamai a gwamnatin jihar da NNPP ke mulki.

    Ya shaida cewa sun duba jerin sunayen ƴan jam'iyyar na mazaɓar Ganduje, "mutum 27 ne kowace mazaɓa, mun duba a cikin su gaba ɗaya babu ko ɗaya da yake a cikin shugabanni."

    A cewarsa, jami'in da aka ce ya sanar da dakatar da Gandujen, Haladu Gwanjo, ya ce zai je kotu ya nemi haƙƙinsa saboda an zalunce shi.

    Abdullahi Abbas ya bayyana cewa "wannan ba abin da ya haɗa shi da jam'iyyarmu, wannan tsari ne na gwamnatin jihar Kano da jam'iyyarsu ta kayan gwari suka shirya, ina tunanin wannan [ita ce] hanyar da za su ci mutuncin dakta Ganduje."

    Ga ƙarin bayanin da shugaban jam'iyyar ta Kano ya yi wa Khalifa Shehu Dokaji.

    • Ban taɓa wani abu don cutar da Ganduje ba, kuma ba zan yi ba - Kwankwaso
    • 'Kalamaina na 'ko da tsiya-tsiya' ba na tunzura rikici ba ne'
  2. Shugaban Somaliya ya tura sojoji domin yaƙar ƙungiyar al-Shabab

    Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya ziyarci sansanonin soji guda uku dake karbar sojojin dake shirye shiryen yaƙar mayakan al-Shabab da kuma rundunar kwamandojin da aka tura Turkiyya domin samun horo, kamar yadda gidan talabijin na kasar Somaliya ya bayyana.

    Mohamud ya ziyarci sansanin Turksom da Turkiyya ta gina, da kuma sansanin Janar Dhaga-badan da Janar Daud da ke Mogadishu babban birnin kasar a jiya.

    "Za mu iya kayar da al-Shabab saboda mun fi su yawa kuma muna da karfin gwiwa," in ji Mohamud ga sojojin.

    Sojojin Somaliya na shirin sake kai manyan hare-haren soji kan al-Shabab da aka dakatar a cikin watan azumin Ramadan a watan Maris da Afrilu.

    Tura sojojin na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar al-Shabab ta ƙara kai hare-hare a cikin watan Ramadan na bana, wanda ya ƙare a ranar 9 ga watan Afrilu.

  3. Barka da Safiya

    Barka da safiya da fatan mun wayi gari lafiya.

    Muna fatan kasancewa tare da ku a wannan safiya ta Talata.

    Za mu kawo muku labarai da rahotanni masu ƙayatarwa daga ko ina a sassan duniya musamman Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya duba ƙarin labarai da kallon bidiyo.