Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, A'isha Babangida, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Mamakon ruwan sama ta haddasa ambaliya a wurare da dama a Kenya ciki har da Nairobi, babban birnin ƙasar.
Aƙalla mutum 11 ne sun rasa ransu, yayin da wasu fiye da 17,000 kuma suka rasa muhallansu.
Daminar bana wadda ta sauka a tsakiyar watan Maris ta lalata gidaje da kuma gonaki da dama.
Waɗanda ambaliyar ta shafa sun buƙaci gwamnati da ta taimaka musu yayin da suke fuskantar barazanar yunwa da kuma kamuwa da cutuka.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross a Kenya na taimaka wa waɗanda ambaliya ta tursasawa barin muhallansu.
Gwamnatin jihar Nasarawa ta haramta ayyukan ƙungiyoyin ƴan sa-kai na kabilu da ke aiki a faɗin kananan hukumomi 13 da ke jihar.
Hakan ya biyo bayan wani taron gaggawa ne da gwamna Abdullahi Sule ya jagoranta .
Haka-zalika gwamnatin jihar ta ba da wa’adin makonni biyu ga ɗukkan ƙungiyoyin ƴan sai kai da umarnin ya shafa da su miƙa kayan sarki, wato inifam da kuma makamansu ga kwamishinan ‘yan sandan jihar.
kwamishinan Shari’a na jihar ta Nasarawa, Barrister Magaji Labaran, ya faɗa wa BBC cewa an ɗauki matakin ne saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu yankuna na jihar.
"Cikin abubuwan da suka sa aka haramta ƙungiyoyin ƴan sa kai shi ne ganin cewa duk wata kabila idan ta tashi sai ta kirkiro da ƴan sa kai. An yi duba an ga cewa waɗannan ƙungiyoyi za su kawo barazana ga zaman lafiya a jihar," in ji shi.
Ya ce duk wata ƙungiya ta ƴan sa kai da za a kafa nan gaba, ya kasance ba ta da ɗauki wani ɓangare guda ba.
Isra'ila ta tabbatar da cewa ta kashe wani kwamandan ƙungiyar Hezbollah a wani hari ta sama da ta kai kudancin Lebanon.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe Isma'il Yusaf Baz, wanda shi ne jagoran wata ƙungiya a yankin Ain Ebel.
Sanarwar ta bayyana shi a matsayin babban jami'i wanda ya rike mukamai a ƙungiyar.
Ta ce yana cikin waɗanda suka harba roka da makamai masu linzami cikin Isra'ila daga gaɓar ruwan Lebanon.
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka kashe bashin dala miliyan 350 na bankin duniya da tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i ya ciyo, da kuma wasu kuɗaɗe da aka kashe da kuma watsi da wasu ayyuka da gwamnatin da ta shuɗe ta fara su tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
Rahotanni daga kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito cewa kakakin majalisar, Yusuf Liman ne ya kaddamar da kwamitin mai mambobi 13 a zaman majalisar a ranar Talata.
Kafa kwamitin ya biyo bayan kudirin da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kauru, Mugu Yusuf ya gabatar na neman majalisar ta binciki dukkan basussukan da gwamnatin El-Rufai ta karɓa.
“Na sha wahala sosai don kada in ba da izinin karɓar bashin, hatta mataimakin shugaban majalisar a wancan lokacin Isaac Auta Zankhai na adawa da ni saboda rashin amincewa da rancen da za a karɓa. Na faɗa gwamna El-Rufai a lokacin cewa ya duba adadin rancen da muke da shi a hannu, amma ya ki saurara ta,” in ji shi.
A jawabansu daban-daban, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Jaba, Henry Marah da takwaransa na mazaɓar Zangon Kataf Samuel Kambai, sun dage cewa ‘yan majalisar suna da hakki da tsarin mulki ya ba su na ba da izini kafin gwamna ya ci bashi, amma ya koka da cewa lamarin Kaduna daban yake.
Don haka suka buƙaci kwamitin da ya gayyaci shugabannin majalisa na takwas da na tara tare da wasu ’yan majalisa na yanzu, domin zuwa su yi bayanin yadda aka karɓo rancen da kuma kashe su.
Kakakin majalisar ya kuma tabbatar wa majalisar cewa za a duba lamarin yadda ya kamata, yana mai cewa za su bai wa kowa ‘yanci don faɗar gaskiya.
A watan Maris ne, gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa ya gaji bashin da ya kai dala miliyan 587 da kuma bashin kwangila 115 daga gwamnatin El-Rufai da ta shuɗe, inda ya koka da yadda bashin ya ke kawo nakasu a cikin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa jihar.
Birtaniya da Canada sun ƙaƙaba takunkumi kan 'yan kasuwa da mutanen da ke da alaƙa da tallafa wa Sudan kamar yadda gidan radiyon Tamazuj da ke Amsterdam ya ruwaito.
Birtaniya ta sanya takunkumi kan Bankin Alkhaleej wanda ake zargin ya ba da kuɗaɗe don ayyukan dakarun RSF da kuma Al-Fakher Advanced Works, wani kamfani da dakarun ke amfani da shi wajen fitar da zinare.
Har ila yau, ta kakaba takunkumi kan kamfanin hakar ma'adinai na Red Rock, wanda ke ba da kuɗade ga sojojin Sudan.
An sanya irin wannan takunkumi kan kamfanoni shida a watan Yulin bara.
Canada ta kuma sanar da ƙaƙaba takunkumi kan mataimakin kwamandan RSF Abdelrahim Hamdan Dagalo, da kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar Ali Karti, wanda ke jagorantar RSF masu iƙirarin jihadi da ake zargi da ci gaba da yaƙin Sudan.
Haka kuma ta sanya takunkumi ga kamfanoni huɗu da ake zargi da tallafa wa RSF da sojoji.
A halin da ake ciki, a ranar Litinin ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa ƙasarsa da kawayenta sun yi alkawarin bayar da sama da yuro biliyan biyu don taimakawa wajen rage matsalar jin kai a Sudan.
Ƙasa da mako ɗaya bayan da Mozambique ta gamu da haɗarin ruwa mafi muni, ƙasar ta sake fuskantar wani haɗarin jirgin ruwa da ya halaka mutane da dama.
Wani iyali na mutum 12 suna cikin kwale-kwale a lardin Caia lokacin da jirginsu ya nutse. Takwas daga cikinsu sun mutu sai biyu da har yanzu ba a san inda suke ba.
Akasarin waɗanda suka mutu yara ne, kamar yadda rahotanni daga AFP suka bayyana.
Suna kan hanyar zuwa wani tsibiri da ke kusa ne domin shaƙatawa. Biyu daga cikin fasinjojin sun tsira da ransu.
An dakatar da aikin ceto saboda rashin kyawun yanayi, amma an ci gaba da kai agaji tun safiyar yau Talata, kamar yadda jami'i a lardin Caia Nobre dos Santos ya ce.
Hatsarin ya faru ne ranar Litinin a kogin Zambezi in ji kafar yaɗa labaran ƙasar.
A makon da ya gabata ne gwamnati ta ƙaddamar da bincike kan haɗarin jirgin ruwa da ya kashe fasinjohi da dama.
Sama da mata 10,000 ne aka kashe a Gaza tun bayan fara yaƙi a Gaza, a cewar wani sabon rahoto na ƙungiyar mata na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙungiyar ta ce a daidai lokacin da yaƙin ke cika watanni shida da fara wa, "ya ci gaba da zama yaƙi a kan mata".
Cikin matan 10,000 da aka kashe, ƙungiyar ta agaji ta ce mata 6,000 sun bar yara marayu 19,000 a baya.
Yaƙin ya ɗaiɗaita waɗanda suka tsira, ya mayar da wasu kuma zawara da kuma faɗa wa yunwa, in ji rahoton.
Ya ƙara da cewa sama da mata da 'yan mata miliyan ɗaya ba su da abinci, ruwan sha, wuraren bahaya ko kuma auduga, inda cutuka ke ci gaba da yaɗuwa a cikin yanayin da suke rayuwa.
Ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas a Gaza, ta ce sama da Falasɗinawa 33,843 ne aka kashe tun watan Oktoba.
Hukumar ƙatin ɗan ƙasa (NIMC) ta bayyana cewa har yanzu ‘yan Najeriya miliyan 95 na buƙatar yin rajistar katin shaidar ɗan kasa (NIN) domin cimma burinta na yiwa ‘yan ƙasar miliyan 200 rajista nan da shekarar 2025.
Shugaban Sadarwa na hukumar, Kayode Adegoke ne ya sanar da hakan a shafin sada zumunta na X a ƙarshen mako.
A cewar Adegoke, an bayar da sama da lambar NIN miliyan 105 ya zuwa yanzu, tare da kokarin yi wa sauran al’umma rijistar katin shaidar ƙasa a cikin shekara ɗaya ko biyu masu zuwa.
Adegoke ya bayyana mahimmancin NIN a matsayin wata alama ta musamman mai mahimmanci ga shirye-shiryen gwamnati daban-daban da aka mayar da hankali kan inganta tsaro da shugabanci da samar da ayyukan yi.
Ya kuma tabbatar da aniyar hukumar na ganin an samu yi wa dukkan ƴan Najeriya a faɗin duniya rajistar nan da shekarar 2025.
Adegoke ya lura da cewa bayan naɗin Abisoye Coker a matsayin darakta-janar na hukumar, ta gano cewa akwai buƙatar a daidaita tsarin gyare-gyare da rajista.
Ya ƙara da cewa, an samar da wani dandali na dogaro da kai, wanda zai bai wa ‘yan Najeriya na gida da waje damar yin gyare-gyaren da ya kamata, kamar canza suna da ranar haihuwa da adireshin Imel, da lambobin waya daga gidajensu ko ofisoshinsu, ta hanyar amfani da wayoyi daban-daban.
Adegoke ya jaddada cewa za a saukaka wannan dandali na dogaro da kai, inda ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan sabuwar dabarar.
Ya yi nuni da yadda tsarin ke faruwa, inda ya ce a baya, masu son a yi musu gyara sai sun ziyarci ofisoshin NIMC domin gyara bayanansu.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kai samame kan maɓoyar ƴan fashin daji a ƙaramar hukumar Maru da ke jihar Zamfara, inda dakarunta suka halaka 12 daga cikinsu.
Cikin saƙon da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na X, sojojin sun lalata sansanin ƴan bindigar tare da kashe wasu daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka tsere.
A cewar daraktan yaɗa labarai na runduanr, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, dakarun sun kuma gano bindiga ƙirar AK47, da kunshin alburusai, da wasu bindigogi ƙirar gida.
Kazalika, sun gano wasu babura 10 da ƴan bindigar ke amfani da su wajen gudanar da harkokinsu, sannan sun ƙwato shanu 18 da aka sace, in ji ta.
"Nasarar ta nuna jajircewar sojojin Najeriya wajen yaƙar ayyukan ta'addanci," in ji sanarwar.
Ministan harkokin wajen Isra'ila ya ce yana jagorantar wani shiri na neman ɗaukar mataki kan Iran a difilomasiyyance bayan harin da ta kai mata.
Ya fadi haka ne yayin da gwamnatin ƙasar ke duba yiwuwar mayar da martani kan harin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ta kai mata ranar Lahadi.
Isreal Katz ya aika takarda ga ƙasashe da dama, inda yake neman su ƙaƙaba takunkumi kan shirin ƙera makamai masu linzami na Iran.
"Da safiyar yau, na aika wasiƙa ga ƙasashe 32, kuma na yi magana da ministocin ƙasashen waje na ƙasashe da dama da manyan mutane a duniya, inda na buƙaci a sanya takunkumi kan shirin ƙera makamai masu linzami na Iran," in ji Katz a shafin X.
Ya kuma yi kira da a ayyana dakarun juyin juya halin Iran a matsayin ƙungiyar ta'addanci, "a matsayin wata hanya ta yaƙi da kuma rage wa Iran ƙarfi".
Ya ƙara da cewa: "Dole ne a dakatar da Iran yanzu - kafin lamari ya ɓaci."
Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin ƙasar ta rufe wasu gidajen mai da ake zargi da hannu wajen sayar da man ga ‘yan fashin daji.
Hakan ya zo sakamakon wani samame da kwamitin aiki da cikawa mai sa ido kan hauhawar farashi da zirga-zirga ya kai gidajen man, inda har aka kama mutum 10.
Katsina ta jima tana fama da hare-haren ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Habiba Adamu:
Ƴan kasuwa da dama da ke Kampala a Uganda sun rufe shagunansu a ranar Talata a wani ɓangare na nuna adawa da sanya tsarin haraji da ya janyo cece-kuce, kamar yadda rahotanni daga kafafen yaɗa labaran ƙasar suka bayyana.
Ƴan kasuwa da dama suna ganin sabon tsarin zai dagula harkokinsu sannan kuma ya sa su biyan haraji da yawa. Sun kuma ce manhajar tana da tsada sosai.
An ƙaddamar da tsarin biyan haraji na zamani a watan Janairun 2021 domin bibiyar ciniki da kuma harajin da ake biya.
A baya-bayan nan ne kawai aka aiwatar da tsarin tsakanin ƙananan ƴan kasuwa lamarin da ya janyo zanga-zanga.
A makon da ya gabata, ƴan kasuwa a Kampala da sauran manyan birane sun gudanar da zanga-zangar yini biyu domin nuna adawa da tsarin biyan harajin.
Hukumar tattara haraji ta Uganda ta aiwatar da tsarin duk da damuwar da ƴan kasuwar suka nuna inda ta ce amfani da tsarin zai magance ƙin biyan haraji sannan ya sauƙaƙawa ƴan kasuwa wajen bayar da bayanan harajinsu.
Wata ɗaliba musulma a wata makaranta a birnin Landan ta yi rashin nasara a wata babbar kotu kan ƙarar da aka shigar ta haramta yin sallah.
Yarinyar dai ta shigar da ƙarar makarantar Michaela da ke Brent a gaban kuliya saboda hana sallah wani mataki da ake ganin wariya ne.
A baya, makarantar wadda ba ta addini ba ce ta shaida wa kotun cewa ba da damar a yi sallah zai "gurgunta tsarin tafiya da kowa" tsakanin ɗalibai.
Mamallakin makarantar da babban malama, Katharine Birbalsingh ta ce hukuncin "nasara ce ga dukkan makarantu".
A hukuncin mai shafi 83 da ya kori ƙarar ɗalibar, alƙali Linden ya ce: "shiga makarantar, kamar yarda da tsarin ne cewa za ta fuskanci wasu dokoki game da yin ibadunta."
Kimanin rabin ɗaliban makarantar kusan 700 musulmi ne, kamar yadda aka faɗa wa kotun. A Maris ɗin 2023, kusan ɗalibai 30 sun fara sallah a harabar makaranta inda suke amfani da rigarsu a matsayin darduma, kamar yadda aka shaida wa kotu.
Makarantar ta bijiro da haramcin a irin watan saboda damuwar da aka nuna wajen nuna wariya tsakanin mabiya addinai, kamar yadda aka sanar da kotun.
Sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun kama wasu sojoji da jami'an 'yan sanda da ake zargi da aikata laifin cin amanar kasa, in ji shafin intanet na Actualite.
Babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar Janar Christian Tshiwewe Songesha ya fada ranar Litinin cewa an kama mutanen a Lubumbashi da Kinshasa amma bai yi ƙarin bayani ba.
Songesha ya sake nanata cewa “sakamakon cin amanar kasa” da doka ta tanada tare da bayyana irin azabar da sojoji ke fuskanta na rashin bayar da rahoton irin waɗannan ayyukan, in ji Actualite.
Ya ƙara da cewa shawarar da aka yanke na farfado da hukuncin kisa ga sojojin da ake zargi da cin amanar kasa ya kasance " martani kai tsaye ga ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta".
Gargadin na Janar Songesha ya biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu ‘yan jam’iyyar tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila sun shiga sabuwar kawancen kungiyoyi masu dauke da makamai.
An kafa kungiyar Congo River Alliance, wadda ta haɗa da ƙungiyar ‘yan tawayen 23 a shekarar 2023 domin hamɓarar da gwamnatin shugaba Felix Tshisekedi.
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce aƙalla Falasɗinawa 33,843 aka kashe a Gaza tun watan Oktoba.
Adadin ya haɗa da mutuwar mutum 46 cikin fiye da sa'a 23, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana cikin wata sanarwa.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa mutum 76,575 aka raunata a zirin Gaza.
Ƙasar Kenya na gudanar da wani taro na yanki kan bunƙasa ilimin yara mata a gabashin Afirka.
Manufar su ita ce ƙalubalantar ƙa'idodin al'umma waɗanda ke cire wasu 'yan mata daga neman ilimin ta hanyar amfani da hanyoyi na al'adu.
Sama da masu ruwa da tsaki 100 daga ƙasashen Uganda da Tanzania da Kenya ne za su halarci taron na kwanaki uku, wanda za a fara a Nairobi ranar Talata.
Wani muhimmin abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne haɓaka tsarin tallafi ga 'yan mata masu rauni - ciki har da 'yan mata masu juna biyu da iyaye mata matasa da 'yan mata masu nakasa.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Najeriya na ci gaba da biyan tallafin mai wani abu da ya ce ƴan Najeriya da dama ba su sani ba.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, El Rufai ya ce a yanzu gwamnati na biyan fiye da abin da take biya a matsayin tallafin mai a baya.
Ya bayyana cewa matakai da dama da aka tanada na rage raɗaɗin janye tallafin mai ba sa tasiri abin da a cewarsa ya sa aka maido da tsarin.
A jawabin da ya yi lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki, shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin mai.
Sai dai El Rufai wanda a lokacin ya nuna goyon baya ga tsarin, ya ce dole ta sa gwamnatin yin gyare-gyare.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito El Rufai na cewa wurin aiwatar da tsarin, kamar yadda ake gani, gwamnatin a yanzu ta gano cewa dole a ci gaba da biyan tallafin, muna biyan kuɗi mai yawa kan tallafi fiye da yadda take biya a baya.
"Dalilin shi ne saboda an ga tasirin hakan sannan tsare-tsaren da aka shirya domin rage tasirin cire tallafin ba su yi wani tasiri ba, a don haka gwamnatin tarayya ta koma biyan tallafin mai."
Ya ce mutane da dama ba su san cewa gwamnati tana ci gaba da biyan tallafin mai ba, "amma idan suna son su san ko ana biya ko a a, su duba farashin mai da dizel saboda kamata ya yi mai ya fi tsada a kan dizel amma farashin dizel ya haura naira dubu ɗaya yayin da man fetur yake kan naira 600 duk lita guda.
"Don haka, har yanzu muna biyan tallafin mai saboda gwamnati ta gane cewa yadda ta aiwatar da tsarin biyan tallafin tun farko na buƙatar a sake nazari a kai. " in ji shi.
Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce shari'ar da ake yi masa rashin adalci ne da bita da ƙullin siyasa, bayan da ya kasance tsohon shugaban ƙasar na farko da ya fuskanci tuhuma ta wani mugun laifi a gaban kotu.
Wannan shari'ar dai ta fara ne da, ƙalubale na zaɓar masu taimaka wa alƙali yanke hukunci, inda aka riƙa sallamar wadanda suka bayyana cewa abu ne mawuyaci su iya zama ƴan baruwanmu wato ba tare da nuna son-kai ba a shari'ar.
Hakan dai ya sa alƙali ya riƙa sallamar su ɗaya bayan ɗaya har ta kai ga zaɓar waɗanda za su yi aikinsu kusan 32, waɗanda su ma aka riƙa yi musu tambayoyi na kwakwa ɗaya bayan ɗaya.
A yayin zaman shari'ar Mista Trump ya kasance shiru a kotun, in ban da magana da yakan yi da lauyoyinsa, jifa-jifa fuskarsa murtuke, inda duk tsawon zaman kalma uku kawai ya furta.
Ga alƙalin kotun Kolin ta New York, Mai Sharia Juan Merchan - a lokacin da ya tambaye shi game da yadda ake buƙatar mutum ya kasance a kotu – kalmar kuwa duka ita ce, yes- wato Eh.
To amma kuma a wajen kotun Mista Trump tun da farko ya bayyana wa manema labarai cewa shari'ar, shirme ce kawai, kuma wani hari ne a kan Amurka.
Kuma waɗannan kalamai sun ɗauki ɗan lokaci ana muhawara a kotun yayin zaman.
A shari'ar dai ofishin babban mai gabatar da ƙara na gundumar Manhattan na zargin Mista Trump da cewa ya umarci tsohon lauyansa Micheal Cohen ya biya wata mata Ms Daniels dala dubu 130.
Domin rufe bakinta a kan wata baɗala ta lalata da ake zargin sa da aikatawa wadda ya musanta an yi.
Masu gabatar da ƙara sun ce ya yi hakan ne domin zaɓen 2016.
Ana tunanin shari'ar za ta ɗauki tsawon watanni ana fafatawa inda ake buƙatar mista Trump ya kasance a cikin kotun tsawon zaman shari'ar.
Editan BBC a Arewacin Amurka ya ce shari'ar da kuma lokacin da za a ɓata ana yin ta, na iya yin babban tasiri a zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba.