Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Aisha Bappa and Umar Mikail

  1. Mahaukaciyar guguwa ta afka arewacin Madagascar

    ..

    Asalin hoton, Eumetstat

    Wata mahaukaciyar guguwa da ta afka arewacin Madagascar ta janyo mutuwra mutum aƙalla shida tare da raba 2,000 da gidajensu.

    Jaridun ƙasar sun ce ambaliyar ruwa ta yi gagarumar ɓarna da ta shafi tituna da gadoji.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito hukumar kula da annoba ta ƙasa data bayyana mutuwar mutum 11 sakamakon guguwar ta Gamane.

    Hukumar ta ce mutum shida sun nutse, sauran kuma sun mutu sakamakon bishiyoyi da suka faɗa musu da kuma gidaje da suka ruguje.

    "Ba kasafai ake ganin irin wannan guguwa ba," in ji Janar Elack Andriakaja, babban daraktan hukumar.

    • Mahaukaciyar guguwa da ta shafe fiye da wata ɗaya tana ɓarna
    • 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'
  2. Tinubu ya kafa kwamitin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kafa kwamitin karta-kwana da zai samar da hanyoyin daidaita tattalin arzikin ƙasar da ke ci gaba da fuskantar tasku.

    Farashin kayan abinci da mai ya yi tashin gwauron zabi kuma mutane da dama na fama kasancewar albashinsu bai wadatar ba wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum ba.

    Ƙalubalen tattalin arzikin ya janyo matsin rayuwa ga mutane da dama abin da kuma ke ƙara matsa lamba kan gwamnatin Tinubu.

    Wasu na ganin janye tallafin mai da faɗuwar darajar naira ne suka janyo matsalolin.

    Sai dai hukumomi sun ce yi wa tattalin arzikin ƙasar garambawul ya zama dole saboda makomar ƙasar.

    Shugaban ya umarci kwamitin ya gabatar da cikakken tsarin farfaɗo da tattalin arziki cikin mako biyu wanda za a aiwatar cikin wata shida.

    Manyan jami'an gwamnati da kuma ƴan kasuwa ne mambobin kwamitin.

    Shugaban ya kuma kafa kwamitin shugaban ƙasa da zai kula da harkokin tattalin arziki, wanda kuma zai jagoranci sa ido kan sauye-sauyen tattalin arziki.

    • Ko sayar wa 'yan canji dala zai iya farfaɗo da darajar naira?
    • Abubuwa biyar da ke faruwa da tattalin arzikin China
  3. Shugaban Uganda ya ƙaddamar da bankin Musulunci na farko a ƙasar

    ..

    Asalin hoton, Ugandan presidency/X

    Shugaban Uganda ya ƙaddamar da bankin Musulunci maras tsarin ƙarbar kuɗin ruwa irinsa na farko a ƙasar.

    Bankin Salaam wanda reshe ne na wani banki da ke Djibouti, shi ne na farko da ya fara ba da bashi kan tsarin Musulunci a ƙasar.

    Mista Museveni ya ce bankin na da ƙarfin ba da gudunmawa ga cigaban harkokin kuɗi na ƙasar da kuma jawo hankalin Musulmai masu saka hannun jari.

    "Ina ƙarfafa muku gwiwa kan yaƙar talauci da samar da arziki", a cewar shugaban ƙasar jim kaɗan bayan ƙaddamar da bankin a ranar Laraba a Kampala, babban birnin ƙasar.

    A Satumbar shekarar da ta gabata ne bankin Salaam ya samu lasisin fara aiki bayan da majalisar dokokin Uganda ta amince da tsarin bankin Musulunci, wanda Mista Museveni ya sa hannu a matsayin doka.

    Ba a yarda da biya da kuma karɓar kudin ruwa a tsarin bankin Musulunci ba amma ana gudanar da tsarin ne a kan raba riba da kuma asara.

  4. Sojojin Najeriya sun kashe 'ƙasurgumin ɗan fashi' Junaidu Fasagora

    Makamai

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Dakarun sojin Najeriya da aka tura jihar Zamfara domin yaƙar ta'addanci sun kashe shahararren jagoran ƴan bindiga mai suna Junaidu Fasagora tare da wasu mayaƙansa, a cewar rundunar.

    Wata sanarwa da ta wallafa a intanet ta ce sun yi nasarar ce bayan fafatawa da kuma musayar wuta mai zafi a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

    "Junaidu Fasagora tare da sauran ƴan bindiga abokansa sun dade suna garkuwa da mutane tare da aikata wasu ayyukan ta'addanci ga al'ummar jihohi da dama na yankin arewa maso yammacin kasar," in ji sanarwar.

    Ta ƙara da cewa kawar da su "wata gagarumar nasara ce a yaƙin da ake yi da ta'addanci da kuma rashin tsaro".

    Mutuwar Fasagora na zuwa ne yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin mutuwar shahararren ɗan fashin daji Dogo Gide, wanda har yanzu BBC ba ta kai ga tabbatar da mutuwarsa ba.

  5. Bassirou Faye ya ci zaɓen Senegal a hukumance

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗantakarar hamayya a zaɓen shugaban Senegal ya lashe zaɓe bayan samun kashi 54.28 na gaba ɗaya ƙuri'un da aka kaɗa, a cewar sakamakon da hukumar zaɓe ta ƙasar ta fitar a ranar Laraba.

    An bai wa ƴan takarar shugaban ƙasar nan da Alhamis da su shigar da ƙorafe-ƙorafen ƙalubalantar nasarar Mista Faye wanda bayan haka ne majalisar tsarin mulkin ƙasar za ta tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓan shugaban ƙasa.

    Babban abokin hamayyar Mista Faye wanda ya kasance tsohon firaiministan ƙasar Amadou Ba ya samu kashi 35.79 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Kashi 61 cikin 100 na masu kaɗa ƙuri'a ne suka fita yin zaɓe.

    Mista Ba tare da sauran ƴan takarar shugaban ƙasa 15 tuni suka amince da shan kaye tare da taya Mista Faye murna. Ana ganin zai yi wuya su ƙalubalanci sakamakon zaɓen.

    Shugaban ƙasa mai barin gado ya yi ƙoƙarin jinkirta zaɓen da a farko aka tsara yi a watan Fabarairu wanda hakan ya yi sanadiyyar zanga-zanga da kuma mutuwar mutum uku.

    Mista Faye ya ce zai yi mulki cikin ƙas-ƙasa da kai da kuma yaƙar cin hanci da rashawa.

    Kuma ya yi alƙawarin daukan matakan da za su magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa da kuma tsadar rayuwa.

    Mutane na tsammanin abubuwa da dama daga gare shi kasancewarsa shugaba mafi ƙarancin shekaru tsakanin shugabannin ƙasashen Afrika.

    • Daga kurkuku ya zamo shugaba mafi ƙarancin shekaru a Afirka
  6. 'Yan sanda sun tarwatsa taron 'yan adawa a Togo

    'Yan sanda a tsaye

    Asalin hoton, AFP

    'Yan sanda a Togo sun tarwatsa wani taron manema labarai da 'yan adawar kasar suka kira domin bayani a kan batun garanbawul din da za a yi wa kundin tsarin mulkin kasar lamarin da ya janyo ce-ce-kuce.

    A ranar Litinin ne, majalisar dokokin kasar ta kada kuri'a a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda ya kunshi batun sauye- sauye daga tsarin mulkin shugaban kasa zuwa tsarin mulkin firaiminista.

    To amma tun kafin majalisar dokokin kasar ta kada kuri'a a kan wannan tsari,'yan adawa ke nu na fargaba a kan cewa sauyin zai bayar da dama ga shugaban kasar mai ci yanzu, Faure Gnassingbe,ya kasance a kan mulki har sai da yadda hali ya yi.

    Kusan 'yan sanda 30 ne suka tarwatsa taron wanda 'yan adawa da kungiyoyin al'umma suka kira a ranar Laraba.

    'Yan sandan sun ce taron wanda aka yi a Lome, babban birnin kasar ta Togo ya sabawa ka'ida.

    Nathaniel Olympio, wanda ya shirya taron ya kira sabon yunkurin a matsayin juyin mulki, wanda ke bukatar al'ummar kasar ta Togo su tashi tsaye don kwatar 'yancinsu.

    Ba a san ko zuwa yaushe sauye-sauyen za su fara aiki ba.

  7. Ana neman mutum takwas da ake zargi da kisan sojin Najeriya 17

    ..

    Asalin hoton, Army/X

    Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce tana neman wasu mutum takwas ruwa a jallo saboda zargin su da hannu a kisan sojoji 17 a yankin Okuama da ke jihar Delta.

    Daraktan yaɗa labaran tsaro Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka yi a hedikwatar tsaron da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

    Hedikwatar tsaron ta fitar da sunayen mutanen takwas ranar Alhamis da suka haɗa da farfesa Ekpekpo Arthur da Andaowei Dennis Bakriri da Akevwru Daniel Omotegbo sai Akata Malawa David da Sinclear Oliki da Clement Ikolo Ogenerukeywe da Reuben Baru sai kuma Igoli Ebi.

    Buba ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya a faɗin Najeriya musamman a yankin Neja Delta su taimaka wa sojoji wajen zaƙulo waɗanda aka ayyana ana neman ruwa a jallo.

    A ranar 14 ga watan Maris ne wasu ɓata-gari suka afka wa sojojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya tsakanin al'umomin yankunan Okuoma da Okoloba inda suka kashe su.

    A ranar Laraba ne kuma aka yi jana'izar sojojin a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja inda shugaba Bola Tinubu ya halarta tare da wasu manyan jami'an gwamnati.

    • Lokuta biyar da mutanen gari suka yi wa jami'an tsaro kisan gilla a Najeriya
    • Abin da ya sa nake cinikin kuɗin fansa tsakanin ƴanbindiga da iyalai
  8. Barka da Hantsi!

    Muna yi muka barka da wannan lokaci. Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma wasu sassan duniya.

    Za ku iya zuwa shafukanmu na intanet domin karanta ƙarin labarai.