Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and Aisha Bappa

  1. Ana tunanin waɗanda suka ɓace bayan karyewar gadar Baltimore sun mutu

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Masu gadin teku a Amurka sun ce ta yiwu mutane shidan nan da har yanzu ba a gano su ba lokacin da jirgin ruwan dakon kaya ya daki gadar birnin Baltimore sun rasu.

    Da yake jawabi ga manema labarai, Rear Admiral Shannon Gilreath, ya ce ba lallai mutanen su kasance a raye ba saboda tsawon lokacin da suka ɓata da kuma rashin kyawun yanayin ruwan.

    Wakilin BBC ya ce hukumomi na ta aiki ba kaƙƙautawa, da jirage masu saukar ungulu da kwale-kwale da masu ninkaya, jami'ai sun bayyana yadda suke aiki cikin wahala saboda zurfin ruwan.

    A ɓangare guda kuma hukumomin tashar ruwan Singapore da jirgin da ya taso daga can, sun ce a bara sau biyu ana duba lafiyarsa.

  2. Yadda rashin haihuwa a Japan ya sa kamfanoni suka koma yi wa manya nafkin

    Jariri na kuka

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani kamfanin da ke samar da nafkin a Japan ya sanar da cewa zai daina samar da nafkin din yara a ƙasar, a maimakon haka zai mayar da kai wajen samar da nafkin din manya.

    Kamfanin Oji Holdings, shi ne kamfani na baya bayannan da ya yi wannan sanarwa a ƙasar da tsofaffi suka fi yawa saboda rashin haihuwa.

    Cinikin da ake a kan nafkin din manya ya fi na yara a ƙasar tsawon shekaru fiye da goma.

    Adadin jariran da aka haifa a 2023 a Japan da suka kai 758,631, ya yi ƙasa da kashi 5.1 idan aka kwatanta da shekarun baya.

    Kuma a shekarar barar ne aka samu raguwar haihuwa sosai a ƙasar tun ƙarni na 19.

    Cikin wata sanarwar, kamfanin Oji Holdings, ya ce yanayin cinikin da ya ke samu a kan nafkin din yara na raguwa tun shekarar 2001.

    A 2001 ne, babban kamfanin da ke samar da nafkin a Japan Unicharm, ya ce cinikin da ya ke samu a nafkin din manya ya fi na yara sosai.

    A yanzu haka Japan na cikin ƙasashen da suka fi yawan tsofaffi a duniya inda kashi 30 cikin 100 na tsofaffin na tsakanin shekarun 65 zuwa sama.

    Kamfanin Oji Holdings, ya ce yanzu zai mayar da hankali wajen samar wa ƙasashen Malaysia da Indonesia nafkin din yara domin a nan ne aka yawan buƙatarta saboda ana haihuwar jarirai akai-akai.

    Rashin haihuwa a Japan ya zamo babban abin damuwa a Japan, wadda tana ɗaya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.

    To amma ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ke yi wajen ganin an shawo kan matsalar a yanzu ana samun nasara.

    ƙwararru sun ce dalilan da suka janyo rashin haihuwa a ƙasar na da dama ciki har da rashin aure sannan kuma mata da dama sun shiga aikin ɗamara.

    • Yadda ƙasashen Asiya ke kashe maƙudan kuɗi don bunƙasa haihuwa
    • Halin da jaririyar da ta zama mutum na biliyan ɗaya a Indiya ke ciki
  3. Hotunan babbar gadar Baltimore bayan da ta karye

    Da safiyar ranar Talata ne babbar gadar Baltimore mai suna Francis Scott ta karye inda ta faɗa kofin Patapsco.

    Sai da gari ya waye sosai aka fi ganin girman ɓarnar da lamarin ya haifar wanda ya nuna ragowar gadar da ake iya gani a saman ruwa.

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, ReutersThe Francis Scott Key Bridge in Baltimore collapse

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, Maxar

  4. Dole a riƙa ɗaukan ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda – Tinubu

    ..

    Asalin hoton, @DOlusegun/X

    Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya bayyana cewa ya zama dole a riƙa ɗaukan mutanen da ke da hannu a aikata miyagun laifuka a matsayin ƴan ta'adda.

    Shugaban ya bayyana haka ne ranar Talata a taron buɗe-baki tare da ma'aikatan shari'a na gwamnatin tarayya bisa jagorancin alƙalin alƙalai na ƙasa, mai shari'a Olukayode Ariwoola.

    Da yake nanata ƙudirin gwamnati na murƙushe ƴan bindiga, shugaba Tinubu ya ce waɗanda suke sace yara matsorata ne da ba za su iya gaba da gaba da sojojin Najeriya ba.

    "Dole ne mu ayyana masu garkuwa a matsayin ƴan ta'adda," in ji shugaban ƙasar, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ta ruwaito.

    Najeriya dai tana fama da ƙaruwar matsalolin tsaro. Yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas sun yi fama da ƙaruwar sace-sacen mutane da hare-haren ƴan bindiga a shekaru 10 da suka gabata.

    Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa ba za ta tattauna da ƴan bindiga ba duk da yadda suka mayar da sace mutane don kuɗin fansa a matsayin wata hanyar samun kuɗi inda suke garkuwa da ɗalibai da jama'a - hari na baya-bayan nan shi ne sace ɗalibai 137 daga Kuriga a jihar Kaduna.

    • Maris: Watan da aka sace daruruwan mutane a Najeriya
    • Me ake nufi idan sunanka ya fito a jerin masu tallafa wa ta'addanci?
  5. Barka da Hantsi!

    Masu bibiyar mu ta wannan kafa, assalamu alaikum. Da fatan muna cikin ƙoshin lafiya.

    A yau ma, za mu kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke wakana a duniya musamman Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Sai ku kasance tare da mu.