Kwamatin Tsaro na MDD ya yi kira a tsagaita wuta a Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Mukhtari Adamu Bawa and Umar Mikail

  1. Gwamnati ta maka kamfanin Binance a kotu kan zargin ƙin biyan haraji

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙara kan kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

    Hukumar tara haraji ta Najeriya, FIRS ce ta sanar da matakin, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

    Gwamnatin dai na tuhumar kamfanin na Binance da aikata laifuka huɗu da ke da alaƙa da ƙin biyan haraji.

    Cikin waɗanda ake ƙarar akwai Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, dukkansu manyan shugabannin Binance da yanzu haka ke tsare a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa.

    Tuhume-tuhumen da ake yi wa Binance sun haɗa da zargin ƙin biyan harajin VAT kan kayayyakin more rayuwa da harajin da kamfanoni ke biya na kuɗin shigar da suke samu da ƙin biyan kuɗaɗen harajin da suka karɓa da kuma haɗa baki da abokanan hulɗarsu wajen kaucewa biyan haraji ta shafinta.

    A cewar gidan Talabijin na Channels, gwamnatin Najeriya tana zargin Binance da ƙin yin rajista da hukumar FIRS saboda dalilai na haraji da kuma saɓawa dokokin biyan haraji a ƙasar.

    Ɗaya daga cikin tuhumar da ake yi ta shafi gazawar Binance na karɓa da kuma biyan nau'ikan haraji ga gwamnati kamar yadda yake a sashe na 40 na dokar FIRS ta 2007 da aka yi wa gyaran fuska.

    Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan ƙudurinta na tabbatar da cewa kamfanonin kirifto suna mutunta dokokinta na haraji tare da magance almundahana a tsakanin irin kamfanonin.

    • 'Muna tsare da shugabannin Binance a Najeriya'
    • Mene ne shafin hada-hadar kudi na Binance?
  2. Isra'ila ta hana shigar da kayan agaji a arewacin Gaza - Majalisar Dinkin Duniya

    Falasdinawa

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza ta ce Isra'ila ta hana ta shigar da kayan agaji a arewacin Gaza inda ake fama da ƙarancin abinci.

    Shugaban hukumar Philippe Lazzarini, ya bayyana matakin da rashin tausayi.

    Mista Lazzirini, ya ce wannan yunƙurin na Isra'ila na nufin mutane da dama za su iya rasa ransu saboda yunwa da ƙishirwa da kuma rashin matsugunni.

    Isra'ila dai ba ta mayar da martani a kan batun ba.

  3. Fitaccen jarumin Nollywood Amaechi Muonagor ya mutu

    ..

    Asalin hoton, Amaechi Muonagor/Instagram

    Fitaccen jarumin Nollywood, Amaechi Muonagor ya mutu yana da shekara 62 a duniya, kamar yadda wani ɗan'uwansa ya shaida wa BBC.

    Ya mutu ne ranar Lahadi bayan ya yi fama da ciwon ƙoda da ya sa ake yi masa wankin ƙodar, in ji rahotanni daga kafafen yaɗa labarai.

    Ɗan'uwan jarumin Tony Muonagor da aka fi sani da Tony Oneweek, ya tabbatar wa BBC mutuwar ɗanfim ɗin ga BBC Pidgin.

    Mutuwar tasa na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da ya nemi tallafin kuɗi domin yi masa dashen ƙoda a Indiya.

    Da yawa cikin masu son fina-finansa sun yi ta jimamin rasuwarsa a shafukan sada zumunta.

    Muonagor ya yi fina-finai da dama ciki har da shahararren fim ɗin nan na Aki da Paw Paw, ɗaya daga cikin fitattun fina-finan da ya taka rawa a matsayin mahaifin yaran.

    Mutuwarsa ta zo ƴan makonni bayan da Najeriya ta yi rashin wani jarumin Nollywood John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu wanda shi ma ya buƙaci tallafin kuɗi domin neman magani.

  4. Daliban jihar Kebbi da ke karatu a India da Masar na fuskantar barazanar kora

    Daliban Najeriya ƴan asalin jihar Kebbi da ke karatu a ƙasashen India da Masar na fuskantar barazanar kora daga makarantun da suke.

    Rashin biyan kuɗin makarantun da su ke daga gwamnatin jihar shi ne abin da ya janyo lamarin.

    Ga karin bayani a rahoton Abdou Halilou.

    Bayanan sautiDaliban Kebbi da ke karatu a India da Masar
  5. Salam Alaikum!

    Jama'a barka da wannan lokaci. Da fatan mun wayi gari lafiya.

    Kamar kodayaushe, a yau ma za mu kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki.