Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Aisha Shariff Bappa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. China ta ba da gudummawar kayan aikin soji ga Burkina Faso

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    China ta ba da gudummawar kayayyakin aikin soja ga ƙasar Burkina Faso, domin tallafawa yaƙi da ta'addanci kamar yadda Tashar talabijin ta RTB ta ƙasar ta bayyana.

    Ƙasar ta ba da gudummawar motoci guda 81 da suka hada da motocin ɗauka kaya na Maxus 58, da tankunan man fetur guda hudu, da tankunan ruwa guda hudu, da manyan motocin daukar kaya guda uku, da manyan motoci guda 9, da manyan motoci guda uku, da wayoyin tauraron dan Adam guda shida.

    Ministan tsaron Burkina Faso, kanar Maj Kassoum Coulibaly, ya gode wa kasar China da wannan gudummawar, ya kuma ce hakan zai taimaka a kokarin "kwarewa da kuma daidaita kasarmu".

    Wenzhang Wang, jami'in hulda da jama'a na ofishin jakadancin China dake Burkina Faso, ya ce wannan gudummawar tana tabbatar da kyakkyawar alaƙa a tsakanin kasashen biyu.

    Burkina Faso dai ta koma wurin China da sauran ƙawayenta ciki har da Rasha, wajen neman taimakon soji, bayan takun saka tsakaninta da Faransa da sauran ƙasashen yammacin duniya.

    • Dakarun Rasha da na China da na Mongolia na rawar daji
    • Ƴanbindiga sun sake sace mutum 61 a Kaduna
  2. Kada wata masarauta ta ɓoye makasan sojoji 17 – Gwamnan Delta

    ..

    Asalin hoton, @DSGovernment/X

    Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya gargaɗi sarakunan gargajiya da ke jihar kan bai wa waɗanda ake zargi da kisan sojojin Najeriya 17 mafaka.

    Ya bayyana haka ne ranar Alhamis, mako ɗaya da faruwar mummunan lamarin.

    An kashe sojojin ne yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'umomin yankin Okuama da ba sa ga maciji da juna a ƙaramar hukumar Ughelli da ke jihar ta Delta.

    Gwamnan ya bayyana buƙatarsa ta son sarakunan gargajiya su bai wa hukumomi haɗin kai a aikin da suke na gano waɗanda suka kashe dakarun.

    Da yake yi wa sarakunan gargajiyar bayani a birnin Asaba, gwamna Oborevwori ya ce Delta tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin doka inda ya nanata cewa bai kamata wata masarauta ta bai wa mutanen da suka yi taɓargazar kariya ba.

    Gwamnan ya ƙara da cewa shugaba Bola Tinubu da sojoji sun ba shi tabbaci cewa ba za a muzgunawa farar hular da ba su ji ba su gani ba yayin binciken.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Shugaban Aljeriya ya sanar da gudanar da zaɓen shugaban kasar da wuri

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya gabatar da ranar gudanar da zaben shugaban kasar da watanni uku.

    A ranar Alhamis ne fadar shugaban kasar ta sanar da cewa Tebboune ya shirya gudanar da zaɓen a ranar 7 ga watan Satumba

    A baya dai ana sa ran gudanar da zaɓen a watan Disamba.

    Fadar shugaban ƙasar dai ba ta bayar da bayanin gudanar da zaɓen ba tun da farko.

    Tebboune, mai shekaru 78, har yanzu bai bayyana ko zai tsaya takara a zaɓen ba.

    A watan Disamba ne wa’adinsa zai kare. Ya lashe kashi 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada don tabbatar da wa'adinsa na farko a watan Disambar 2019.

    • Algeria: Tsohon shugaban ƙasar Abdelaziz Bouteflika ya rasu
    • Ra’ayi: Salon dora alhakin da kasar Algeria ke yi ya bankado gagarumin rikicin siyasa
  4. Dole ne a hukunta waɗanɗa suka kashe mana sojoji 17 - Tinubu

    ...

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce waɗanda suka kashe sojoji a jihar Delta za su fuskanci hukunci, yana mai gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da kai hare-hare kan sojoji da ababen more rayuwa ba.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar dattawan kasar a yayin wani zaman cin abincin buɗe baki a fadar gwamnati a ranar Alhamis.

    Tinubu ya ce sojoji za su ci gaba da samun goyon bayan gwamnatinsa wajen kawar da barazanar tsaro a faɗin kasar.

    "Rundunar sojojinmu na aiki tukuru, kuma ba za mu bar maharan su lalata mutunci da ƙimar sojojinmu da kuma shugabancinta ba."

    "Za mu ci gaba da karfafawa da gwagwarmayar neman ƴancinmu da haƙƙinmu na zama daya, kuma za mu yi nasarar kawar da talauci daga kasarmu,’’ in ji Tinubu. Shugaba.

    Tinubu ya shaida wa shugabannin Majalisar Dattawan cewa, mutuncin Majalisar Dokoki dole ne ya ci gaba da wanzuwa, kuma a ko da yaushe gwamnatinsa za ta ƙarfafa hadin gwiwa don ci gaban kasa.

    "A kan matsalar tattalin arziki da muke fuskanta yanzu, muna ƙoƙarin gaske don ganin mun magance wannan matsalar, kudaden shigarmu sun inganta."

    "Abin da ya kamata mu yi shi ne mu kula da yadda muke kashe kuɗaɗe da kuma yadda za mu sarrafa kanmu da kyau."

    "Nan ba da jimawa ba za ku ga sauyi, murmushin 'yan Najeriya ya kusan dawowa," in ji shugaban.

    A nasa jawabin, shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya godewa shugaba Tinubu bisa karbar bakuncin ‘yan majalisar, inda ya bayyana cewa yin mu’amala akai-akai zai ƙara fahimtar juna da gudanar da shugabanci mai inganci.

    ...

    Asalin hoton, Presidency

    ...

    Asalin hoton, Presidency

    • Wace dabara ta rage wa Tinubu game da tsadar rayuwa a Najeriya?
    • Hanyoyi biyar da ƴan Najeriya ke bi wajen rage raɗaɗin tsadar rayuwa
  5. Blinken ya isa Isra'ila yayin da Amurka ke son a tsagaita wuta a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Isra'ila daga ƙasar Masar a ci gaba da ƙoƙarin da Amurka ke yi na tabbatar da tsagaita wuta a Gaza tare da kuma kuɓutar da mutanen da kungiyar Hamas ke garkuwa da su.

    Blinken zai gana da firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Amurka da Isra'ila.

    Wannan dai ita ce ziyararsa ta shida a yankin tun bayan da Hamas ta kai wa Isra'ila hari a ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda kuma sojojin Isra'ila suka fara yaƙinsu a Gaza a matsayin mayar da martani.

    A ranar laraba ne Blinken ya je Saudiyya kuma ya gana da jami'ai a Masar a ranar Alhamis kafin ya karkata hankalinsa ga Isra'ila a yau, Juma'a

    A yayin ziyarsa dai an ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da wasu ƙasashen larabawa domin ganin an tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin ƴan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su.

    Blinken ya ce tattaunawa tsakanin Amurka da Qatar da Masar ka iya cimma yarjejeniya inda ya ce ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi, kuma yana fatan nan ba da jimawa ba za a cimma nasara.

    Ana sa ran yarjejeniyar za ta ƙunshi tsagaita wuta na mako shida da kuma sako ƴanIsra'ila 40 da Hamas ta yi garkuwa da su, yayin da Isra'ila za ta sako ɗaruruwan Falasɗinawa da take tsare da su abin da Amurka ta kira "tsarin samar da zaman lafiya mai dorewa".

    • An samu ɓaraka tsakanin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amurka da Isra'ila
    • Jarirai na mutuwa a Gaza saboda tsananin yunwa
  6. An kashe ɗaya daga cikin jagororin ƴandabar da suka addabi Haiti

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴan sanda a Haiti sun ce sun kashe ɗaya daga cikin jagoran ƴandabar da suka addabi ƙasar.

    Ti Greg shi ne shugaban ƙungiyar Delmas 95 wadda ke da iko da wani ɓangare na babban birnin ƙasar Porto-Prince.

    Wakilin BBC ya ce ɗandabar ya tsere daga gidan yari ne a farkon watan nan, yayin wani farmaki da ƴanƙungiyarsa suka kai gidan yarin, inda suka saki kusan fursononi dubu huɗu.

    • Abubuwan tarihi biyar da suka janyo rikici a Haiti
    • Rikicin Sudan: Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici
  7. Rwanda ta karɓi 'yan gudun hijira da dama daga Libya

    ...

    Asalin hoton, Rwanda Ministry in charge of Emergency Management/X

    Ƙasar Rwanda ta karbi ‘yan gudun hijira 91 da masu neman mafaka daga kasar Libya a karkashin wani shiri da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Afrika da kuma Tarayyar Turai ke tallafawa.

    Ƴan gudun hijirar sun haɗa da 'yan Sudan 38 da 'yan Eritriya 33 da ƴan Somaliya 11 da ƴan Habasha bakwai da kuma 'yan Sudan ta Kudu biyu.

    An kwashe 'yan gudun hijirar da masu neman mafaka a karkashin shirin gaggawa na jigilar kayayyaki, wanda ya ga 'yan gudun hijira 2,150 da aka aika zuwa Rwanda daga Libya tun daga shekarar 2019.

    Daga cikin waɗannan, 1,600 sun yi ƙaura zuwa Amurka da ko'ina cikin Turai.

    "Rwanda ta ci gaba da jajircewa wajen ba da mafaka ga mabuƙata," in ji ma'aikatar ba da agajin gaggawa ta ƙasar a ranar Alhamis.

    Zuwan 'yan gudun hijirar da masu neman mafaka ya zo ne a daidai lokacin da Birtaniya ke ƙokarin samar da sabuwar dokar da za ta ba ta damar tura wasu masu neman mafaka zuwa Rwanda..

    A baya dai kotun ƙolin Burtaniya ta yi fatali da shirin, inda ta bayyana shi ba bisa ka'ida ba.

    • Me ya sa Pakistan ke korar ƴan Afghanistan daga ƙasarta?
    • Halin da matasa masu son zuwa Turai ke faɗawa a tsibirin Lampedusa
  8. 'Ba za mu bar Okuama ba har sai an zaƙulo waɗanda suka kashe sojojinmu 17'

    ..

    Asalin hoton, TAOREED LAGBAJA/TWITTER

    Rundunar sojojin ƙasa a Najeriya ta ce dakarunta ba za su fice daga jihar Delta ba har sai an zaƙulo waɗanda suka kashe sojoji 17 a baya-bayan nan.

    Kwamandan runduna ta shida da ke aiki ƙarƙashin rundunar ko ta kwana a yankin kudu maso kudancin Najeriya, Manjo Janar Jamal Abdussalam ya bai wa shugabannin yankin Neja Delta tabbacin cewa sojoji za su nuna ƙwarewa wajen nemo mutanen da ke da hannu a kisan gillar da aka yi wa sojojin.

    Ya bayyana haka ne lokacin da shugaban hukumar raya yankin Neja Delta Chif Samuel Ogbuku ya kai masa ziyara a hedikwatar rundunar da ke barikin sojoji a Patakwal.

    Rundunar sojin cikin sanarwar da ta fitar ranar Alhamis ta ruwaito manjo janar Abdussalam na cewa nauyin da aka ɗora wa sojojin shi ne su gano makaman da ɓata-garin suka ƙwace daga hannun sojojin da aka kashe tare da tabbatar da cewa an kama duka masu hannu a kisan gillar.

    Ya ƙara da cewa sojoji za su ci gaba da kasancewa a jihar har sai an cimma ƙudurin da aka sa gaba na binciko waɗanda suka tafka aika-aikar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    • Lokuta biyar da mutanen gari suka yi wa jami'an tsaro kisan gilla a Najeriya
    • Ba mu da isassun kayan aikin tunƙarar ƴan bindiga - Babban hafsan tsaron Najeriya
  9. Ƙasar Habasha na shirin ci gaba da dawo da ƴan ƙasarta daga Saudiyya

    ....

    Asalin hoton, AFP

    Ƙasar Habasha za ta fara mataki na uku na dawo da ‘yan kasarta 70,000 daga ƙasar Saudiyya.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasasr ta ce 'yan kasar "suna cikin tsaka mai wuya" a kasar ta Saudiyya.

    Nan da makonni biyu za a fara dawo da su gida.

    Saudiyya ta buƙaci ma'aikatan ƙasashen waje da ke zaune a ƙasar ba tare da izinin doka ba su fice ko kuma su fuskanci hukuncin ɗauri.

    Kasar dai na karbar baƙuncin ‘yan kasar Habasha kimanin 750,000, waɗanda fiye da rabinsu suna ƙasar ba bisa ka’ida ba, a cewar hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya IOM.

    Sun haɗa da ma'aikata, masu neman aikin yi da kuma 'yan gudun hijirar da ke tserewa rikici a kasar da ke yankin kahon Afirka.

    A baya dai ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bayyana cewa wasu ‘yan kasar Habasha na fuskantar cin zarafi a Saudiyya da suka hada da azabtarwa da kuma kisa.

    Saudiyya ta maido da ‘yan kasar Habasha sama da 350,000 tun daga shekarar 2017, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta IOM.

    • Anya tallafi na kaiwa ga 'yan Ethiopia kuwa?
    • Abin da ya sa yaƙin Ethiopia ya sake zama sabo a Tigray da Amhara
  10. Assalamu Alaikum!

    Masu bin mu a wannan kafa muna muku maraba da shigowa shafin kai-tsaye na BBC Hausa.

    Muna fatan za ku kasance da mu a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Sai ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Akwai ƙarin labarai da bidiyo da za ku iya dubawa a shafukan.