Mu kwana lafiya
Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.
Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.
Aisha Bappa da Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Usman Minjibir, Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Aisha Shariff Bappa and Ahmad Tijjani Bawage
Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.
Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.
Aisha Bappa da Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

Asalin hoton, Reuters
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Rasha ya ce an kashe mutane da dama tare da jikkata wasu a wani hari da aka kai wani zauren raye-raye da ke kusa da Moscow babban birnin ƙasar.
An kuma bayar da rahoton cewa rufin zauren na Crocus da ke Krasnogorsk yana ci da wuta yayin da mutane suka makale a ciki.
Hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna gawawwaki da dama a kofar zauren da kuma mutane suna guje-gujen neman hanyar ficewa daga ginin.
Ana iya jin karar harbe-harbe a bayan fage inda Rahotannin baya-bayan nan suka bayyana cewa wasu mutane uku sanye da kayan sojoji ne suka buɗe wuta a cikin zauren.

Asalin hoton, BBC Studios
A cikin 'yan sa'o'i da suka gabata, Gimbiyar Wales ta bayyana cewa tana jinyar cutar kansa.
Catherine wadda ke auren Magajin Sarautar Birtaniya – ta ɗan ja baya daga ayyukan sarauta lokacin da aka yi mata tiyata a cikin watan Janairu.
A cikin wani bidiyo da aka fitar, ta ce da farko ta yi tunanin cewa cutar da ke damunta ba kansa ba ce, amma daga baya gwaje-gwajen da aka yi sun gano cewa lamarin ba yadda ake tunani ba ne.
A halin yanzu dai Gimbiyar ta fara karɓan magani.
Hakan dai na zuwa ne bayan ce-ce-ku-cen da aka yi na tsawon makonni game da lafiyarta.

Asalin hoton, Reuters
Majalisar Dinkin Duniya na fargabar kimanin 'yan gudun hijirar Rohingya 75 sun mutu a lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a kusa da Indonesia.
Faisal Rahman, jami'i ne na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce jirgin a cike ya ke makil da ‘yan gudun hijira a lokacin da ya kife.
Ya ce " Bayanan da muka samu dai na nuni da cewa akwai mutane 151 a cikin kwale-kwalen, da ‘yan Rohingya 142 ke ciki, sauran kuma ma’aikatan jirgin ruwan ne.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Indonesia da ta ci gaba da neman wadanda suka tsira.

Jamhuriyar Nijar ta sake buɗe kan iyakarta da Najeriya a yankunan Diffa da Tahoua da Maradi da Dosso.
An rufe iyakar kasar da ke tsakanin makwabtan biyu biyo bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli da kuma takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata.
A wani sakon rediyo da aka watsa a shafukan sada zumunta, a ranar Alhamis, ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyar Nijar ta umurci gwamnonin waɗannan yankuna na kan iyaka da su ba da izinin sake bude aiki da karfe 12:00 na dare.
Ma'aikatar ta kuma umurci gwamnonin da abin ya shafa da su karfafa tsaro a kan iyakokin kasar.
An buɗe iyakokin Najeriya makonnin da suka gabata bayan ɗage takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa ƙasar a wani taro da aka yi a Abuja, amma Nijar ba ta mayar da martani ba nan take.
Sai dai kuma har yanzu kan iyakar Nijar da makwabciyarta Benin na nan a rufe a ɓangaren Nijar duk da gaggawar aiwatar da umarnin ECOWAS da hukumomin Benin suka yi.
Hukumomin rikon kwaryar Nijar sun bayar da dalilai na tsaro a matsayin dalilin rashin buɗe kan iyaka da makwabtanta da ke Kudu.

Asalin hoton, b
Majalisar Koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta bayyana damuwa a game da babbar barazanar da ke tattare da aikin Hajjin bana ga al'ummar Musulmi a Najeriya.
Binciken da majalisar ta gudanar kan shirye-shiryen aikin Hajjin na bana ya nuna akwai wagegen giɓi a game da shirye-shiryen.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta ce wa'adin da hukumomin Saudiyya suka ɗiba game da kammala duk wani shiri da ya kamata kama daga biyan kuɗin kujera zuwa sauran shirye shirye, akwai yiwuwar zai iya cika ba tare da maniyyatan bana sun san halin da suke ciki ba na ainihin kuɗin da ya kamata su cika kan kujerar.
Majalisar ta ce har kawo yanzu ba a biya kuɗin rabin kujerun da aka ba wa Najeriya ba.
"Babban abin damuwar shi ne mutanen da suka fara biyan wani daga cikin kuɗin kujerar aikin Hajjin na bana, har yanzu suna cikin rashin sanin inda suka dosa," in ji sanarwar.
Daga bisani majalisar ta ce tana sane da irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen samun sauki musamman kan batun canjin dala wanda shi ne musabbabin abin da ya janyo wannan matsala.
Ta kuma buƙaci 'yan siyasa da masu hannu da shuni da kuma masu ruwa da tsaki da su taimaka yadda ya kamata domin ganin ba a samu koma baya a aikin Hajjin bana ba ga maniyyatan Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyun siyasa a Senegal na ci gaba da neman magoya gabanin zaben kasar da za a gudanar ranar Lahadi.
Jam'iyyun sun gudanar da gangami a Dakar, babban birnin kasar a yau Juma'a gabanin cikan wa'adi.
An samu rudani sosai gabanin wannan lokaci bayan da shugaban kasar ya yi yunkurin dage lokacin yin zabe.

Amurka ta shigar da kara a gaban kotu kan kamfanin Apple, inda ta zargi katafaren kamfanin da mamaye kasuwar wayoyin zamani da kuma murƙushe gasa tsakanin kamfanonin wayoyi.
Shari'ar ta yi zargin cewa kamfanin Apple ya yi amfani da ikonsa na runbun sakko da manhajar wayoyinta don ƙulle abokan ciniki da masu haɓakawa, yana ɗaukar matakan da suka sabawa doka don hana fafatawa a gasa da sauran kamfononin wayoyi da kuma sanya samfuran sauran wayoyi a matsayin ba su da kyau.
Kamfanin Apple dai ya yi alkawarin kare kansa daga zarge-zargen, inda ya musanta aikata irin wannan laifin.
Koken, wanda aka shigar a kotun tarayya da ke New Jersey tare da manyan lauyoyi daga jihohi 16, na wakiltar babban kalubale ga kamfanin Apple, wanda ke fuskantar karin bincike kan ayyukansa a ‘yan shekarun nan.
Amurka ta yi zargin cewa Apple ya yi amfani da dabaru daban-daban don ci gaba da kasancewa da karfin ikonsa a kasuwannin wayoyi, wanda a karshe ya cutar da masu amfani da ƙirar wayoyin kamfani tare da dakile sabbin abubuwa don bunƙasa samunsa.
Babban Lauyan kasar Merrick Garland ya bayyana abin da Apple ya yi da cewa ya saba wa dokokin gwamnatin tarayya a yayin wani taron manema labarai da ke sanar da karar.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan sandan Sifaniya sun kama wasu gungun mutane da suka kware wajen safarar kwayoyi cikin dare da jirgin sama, bayan da suka yi yunkurin shiga Sifaniya daga Maroko.
Ƴan sandan sun ce sun kwashe wasu jirage masu saukar ungulu guda biyu da kuma ganyen wiwi mai nauyin kilogram 800, a wani samamen haɗin gwiwa da ƴan sandan Moroko.
Sun kuma kama mutum tara, inda suka ce biyu daga cikinsu sun kware wajen tuka jirgin sama da dare.
Aikin wanda aka yi a watan Janairu, ya kunshi samame kan wani wurin kiwon dabbobi kusa da birnin Cadiz bayan da masu bincike suka gano cewa wani jirgi mai saukar ungulu na kai da kawowa tsakanin Sifaniya da Moroko.
Ƴan sandan sun ce wani shugaban gungun masu safarar kwayoyin ya mutu a wani hatsarin mota lokacin da ya yi yunkurin tserewa daga wajen da lamarin ya faru.

Asalin hoton, Getty Images
Finland ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta ce za ta koma tallafa wa hukumar jin ƙai mafi girma a Gaza UNRWA.
A watan Janairu ne Isra'ila ta zargi ma'aikatan UNWRA 12 da hannu a hare-haren Hamas na ranar 7 ga watan oktoba.
Abin da ya sa ƙasashe da dama har da Amurka da Birtaniya suka dakatar da bayar da tallafi.
Lamarin ya zo sakamakon sanarwar da ƙasashe da dama kamar Austreliya da Kanada da Suwidin suka yi cewa za su koma bayar da tallafi ga hukumar.
Ministan cinikayya da ci gaba na ƙasar Finland Ville Tavio cikin wata sanarwa ya ce "hana rashin da'a da kuma fara sa ido sosai, zai ba mu isasshen tabbaci a wannan lokacin don ci gaba da tallafin."
UNRWA na binciken bayanan da Isra'ila ta bayar game da zargin da ake yiwa ma'aikatanta, inda ake sa ran samun rahoto na ƙarshe a watan Afrilu.

Asalin hoton, Office of Tanzania's vice-president/X
Mataimakin shugaban ƙasar Tanzaniya, Phillip Mpango ya yi barazanar sauka daga muƙaminsa saboda matsalar ƙarancin ruwan sha da aka daɗe ana fama da ita a lardin Mwanga da ke arewacin ƙasar.
Mista Mpango ya zargi ƴan kwangilar da ke kula da muhimmin aikin samar da ruwan sha a yankin na ɗaukan lokaci kafin kammala shi.
Shirin na sama da dala dubu 100 an soma shi ne kusan shekara 20 da ta gabata, a cewar Mista Mpango.
"Idan har aikin nan ba zai samar da ruwa ba ga mutanen yankin nan da watan Yuni, zan sauka. Ban san me zai zama makomar jami'an da ke kula da aikin ba da mataimakansa idan na yi murabus," kamar yadda Mista Mpango ya ce.
"Ba zan sake zuwa nan na faɗa wa jama'a su ƙara jiran ruwa ba, ruwa shi ne rayuwa," ya ce.
A cewar jami'an gwamnati da suka yi wa Mista Mpango rakiya zuwa Mwanga a ranar Alhamis, an yi kashi 90 cikin 100 na aikin samar da ruwan.

Asalin hoton, Reuters
A jiya ne hukumomin ƙasar Chadi suka kama mutum 175 sakamakon rikicin kabilanci da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 40 a kauyen Tileguey da ke kudu maso gabashin kasar , kamar yadda shafin intanet na Alwihda mai zaman kansa ya ruwaito.
A cewar rahoton, wasu mutane ɗauke da makamai ne suka ƙona wani yanki mai yawa na kauyen.
Tawagar ministocin da ta aike zuwa yankin karkashin jagorancin ministan tsaron jama'a da shige da fice Janar Mahamat Charfadine Margui ta sanar da kame mutanen, inda ya ƙara da cewa an kuma kama manyan makamai 152 da babura 13.
Ministan ya ce "dukkan waɗanda ke da hannu za a gurfanar da su a gaban kuliya" tare da sanar da gudanar da bincike don yin ƙarin haske kan "abubuwan da ba su dace ba".
Rikicin kabilanci ya zama ruwan dare a gabashi da kudancin Chadi, wanda yawanci yakan shafi makiyaya Larabawa da manoma 'yan asalin ƙasar.
Albarkacin Ranar Ruwa ta Duniya, Muhammad Mustafa, Shugaban Gidauniyar Water the Needy mai gina burtsatse kyauta a kauyuka ya bayyana mana yadda ya jagoranci gina burtsatse kusan 2,000.
Muhammad ya bayyana mana yadda suke gudanar da ayyukansu da kuma girman matsalar rashin ruwa a yankunan karkara a Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Daftarin kudurin Amurka na a tsaigata buɗe wuta a Gaza ya gaza.
Kuri'u 11 ne suka kaɗa kuri'ar amincewa da ƙudirin, uku kuma suka ƙi yayin da guda ɗaya kuma ba ya nan.
Ƙasashen Rasha da China su ma sun ƙi amincewa da kudurin tsagaita wuta nan take a Gaza da ke da alaƙa da sako mutanen da Hamas ke garkuwa da su.
Ita ma Aljeriya ta ki amincewa da kudurin na Amurka yayin da ita kuwa Guyana ta tsaya a tsakiya.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York na shirin kada kuri'a kan daftarin kudirin Amurka na neman tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza da ke da nasaba da sako mutanen da Hamas ke garkuwa da su.
Ƙasashen Rasha da China sun ki amincewa da kudurin na Amurka wanda ke son a gaggauta tsagaita wuta a Gaza domin a saki ƴan Isra'ila da Hamas take garkuwa da su.
Ita ma Aljeriya ta ki amincewa da kudurin yayin da ƙasar Guyana kuma ta tsaya a tsakiya.
Wakiliyar Amurka a Kwamitin Sulhu na MDD, Linda Thomas-Greenfield, ta ce Rasha da Amurka ba sa son kaɗa kuri'a kan daftarin da Amurkar ta gabatar saboda sun fi son su ga ta faɗi.
"Rasha ta sake saka siyasa a farko mamakon ci gaba."

Asalin hoton, AFP
Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya naɗa ɗansa Janar Muhoozi Kainerugaba a matsayin sabon babban hafsan tsaron ƙasar (CDF).
A baya dai Kainerugaba ya taɓa riƙe mukamin babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara, muƙamin da ya ɗauka bayan an sauke shi daga muƙamin kwamandan sojojin ƙasar a shekarar 2022 bisa wasu kalamai na ɓatanci.
Ya maye gurbin Janar Wilson Mbado, wanda aka naɗa a matsayin ministan kasuwanci da masana'antu.
Shafin intanet na The Monitor mai zaman kansa a jiya ya bayar da rahoton cewa naɗin Kainerugaba na zuwa ne kwanaki bayan Museveni ya sanya dukkan sassan rundunar tsaron Uganda ƙarƙashin jagorancin CDF a ranar 17 ga Fabrairu.
Laftanar Janar Samuel Okiding ne zai maye gurbin Kainerugaba.
Museveni ya sanar da naɗin dansa ne a lokacin da ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul.
Naɗin Kainerugaba zai iya tabbatar da zargin da aka daɗe ana yi cewa Museveni na shirya ɗansa a matsayin shugaban ƙasa da zarar ya yi ritaya.
Museveni bai nuna wata alama ta barin kujerar da ya daɗe yana rike da ita ba gabanin zaɓen da aka shirya yi a shekarar 2026 ba.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta hannun ma’aikatar kula da ma’adanai ta tabbatar da ayyukan dakarun tsaro 2,220 a karkashin sabon tsarin tsaro, inda ta kuma umarce su da su yi maganin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Haka kuma ta buƙaci sabbin dakarun da su dakile sata da duk wasu munanan ayyuka da suka shafi ma’adinan kasar domin bai wa al’umma damar cin gajiyar amfani da abubuwan da Allah ya hore musu.
Ministan ma’adinai, Dele Alake, ne ya bayar da wannan umarni a lokacin taron karɓar jami'an da aka horar na musamman da kuma aka zayyana zu daga hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya mai suna “Mining Marshal Corps” a hedikwatar ma’aikatar a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja.
Wannan sabon al’amari ya zo ne watanni biyu bayan da Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin ma’aikatu karkashin jagorancin ministan ma’adinai na kasa don yin shawarwari kan hanyoyin da za a bi wajen cimma wa’adinsa na samar da wani tsari na tabbatar da albarkatun kasa da suka hada da ma’adanai da dazuka da kuma tattalin arzikin ruwa.
A cewarsa, kafa dakarun a hukumance zai tabbatar da tsaro a wuraren da ake haƙar ma’adanai, da kawar da baragurbi, da tsaftace muhallin da ake haƙar ma’adanan a cikinsa da kuma safarar ma’adanai daga Najeriya.
Ya bayyana hakan a matsayin babban nasara a cikin ajandarsa guda bakwai.
Ministan ya kara da cewa jami’an hako ma’adinai da aka kirkira domin su zama jami’an tsaro a tsakanin hukumomin za su hada da jami’ai na musamman daga sauran hukumomin tsaro kamar ‘yan sandan Najeriya da sojoji da sauransu.
Da yake jawabi a yayin taron, Alake ya ce, “Rashin tsaro ya durkusar da bangaren tattalin arziƙin ma’adinai tare da hadewa da sauran abubuwan da za su iya haifar da karancin kudaden shiga na ƙasar. Don haka, yaƙi da rashin tsaro a wannan fanni yana da matukar muhimmanci idan za mu sami nasarar cimma wata nasara."
"Muna fata kuma mun yi imanin cewa ma’adinan za su zama hanyar ceton tattalin arzikin Najeriya.”
A nasa jawabin, kwamandan hukumar rundunar farin kaya ta NSCDC, Abubakar Audi, ya bayyana cewa sabbin jami’an hako ma’adanai za su bai wa hukumar hadin kai wajen kare kadarori da ababen more rayuwa na kasa da ma’adanai.
Audi ya bayyana cewa jami’an tsaron za su yi hulda da hukumar kula da ma’adanai a jihohi domin samun bayanan sirri kuma za su kasance a karkashin jagorancin ministan ma’adanai kai tsaye domin gudanar da aiki yadda ya kamata.

Asalin hoton, TELEGRAM
Manyan yankuna na Ukraine na fama da rashin wutar lantarki bayan da makamai masu linzami na Rasha suka fada kan wani rumbun kayayyakin makamashi.
Magajin garin ya ce an samu tashin bama-bamai 15 a birni na biyu mafi girma na Ukraine yayin da sama da gidaje 53,000 a Odesa suka tsinci kansu cikin duhu.
Ministan makamashi na Ukraine, Jamus Galushchenko, ya zargi Rasha da kokarin haifar da babbar gazawar tsarin makamashin kasar".
Ya kara da cewa an yanke layin wutar lantarki da ke samar da wuta ga tashar nukiliyar Zaporizhzhia.
Gwamnan yankin, Ivan Fedorov ya ce tashar wutar lantarkin na dab da faɗawa cikin duhu inda ya kara da cewa gine-gine bakwai a yankin sun ruguje kuma wasu 35 sun lalace.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ta harba makamai masu linzami sama da 90 tare da aika wasu bama-bamai 60 cikin ƙasar a hare-haren da aka kai cikin dare.
Akalla mutum biyu ne aka ruwaito sun mutu sannan wasu 14 suka jikkata.

Asalin hoton, nassarawa govt house
Akalla dalibai mata biyu na jami'an jihar Nassarawa da ke Keffi ne suka mutu sakamakon wani turmutsutsu da aka yi a wajen karbar kayan tallafi na gwamnati a dandalin taro na jami'ar da safiyar Juma'a.
Gwamnatin jihar Nassarawa dai ta yi amfani da dandalin taron da ke jami'ar ne wajen raba kayan tallafin wahalar rayuwa ga daliban jami'ar.
Wani dan jarida da ya shaida yadda al'amarin ya faru ya fada wa BBC daliban matan da suka rasu na daga cikin wadanda suka je neman tallafin.
Mataimakain gwamnan jihar ta Nassarawa, Emmanuel Akadeh wanda ya je jami'ar domin jajantawa dangane da faruwar al'amarin ya ce faruwar al'amarin na da takaici kuma "za mu kafa kwamitin da zai binciko hakikanin abin da ya faru.