Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.
Haruna Kakangi da Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Usman Minjibir, Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.
Haruna Kakangi da Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

Asalin hoton, Reuters
Rundunar ƴansandan Brazil ta tuhumi tsohon shugaban ƙasar, Jayir Bolsonaro da laifin aikata zamba dangane da bayanan riga-kafinsa na cutar korona.
Ma'aikatar lafiya na da bayanan cewa ya yi allurar riga-kafin Korona a ranar 19 ga watan Yulin shekara ta 2021 a São Paulo, amma bincike ya gano cewa yana babban birnin ƙasar Brasilia a wannan lokacin.
Mista Bolsonaro da kansa ya ce duniya ma ta san cewa bai yi riga-kafin ba.
Ɓarkewar cutar korona ta kashe 'yan ƙasar Brazil sama da 700,000 a lokacin mulkin Mista Bolsonaro, wanda shi ne ɗaya daga cikin adadi mafi girma a duniya.

Asalin hoton, Reuters
Majalisar dokokin Hong Kong ta bi umarnin China na zartar da dokar tsaurara tsaro da ke bai wa hukumomin ƙasar karin karfin murkushe ‘yan adawa.
Sabuwar dokar ta tanadi hukunci mai tsauri kamar ɗaurin rai-da-rai kan laifuka kamar cin amanar kasa, kuma an kara faɗaɗa ta don ta shafi wasu sabbin laifuka kamar kutse cikin harkokin gwamnati da kuma tayar da kayar baya.
Babban jami'in gudanarwa na Hong Kong, John Lee, ya ce a cikin wannan makon dokar za ta fara aiki.
L"Yau wani lokaci ne mai cike da tarihi ga Hong Kong, lokaci ne da Hong Kong ta kwashe sama da shekara 26 tana jira amma yanzu wannan muhimmiyar dokar ta tsaron ƙasa za ta fara aiki a hukumance a ranar 23 ga Maris," in ji Lee.
A yau cikin shirin Girke-girken Ramadan 2024, Naja'atu Ibrahim wadda aka fi sani Yakudima ta nuna mana yadda ake haɗa Dashishin Alkama da farfesun rago.

Asalin hoton, Nigerian Senate/X
Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ta kafa kwamitin gaggawa da zai gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa sojojin ƙasar 17 a jihar Delta.
Majalisar ta bayyana hakan lokacin da aka gabatar da kudurin da yake neman a yi bincike kan kisan sojojin, tana cewa ba za ta zuba ido lamarin ya tafi a haka ba, don guje wa ɗauki matakin ramuwar gayya daga sojojin.
Sanata Muhammad Adamu Aleru, mamba a kwamitin sojin ƙasa na majalisar dattawan, ya bayyana wa BBC cewa abin da aikata wa sojojin yana da munin gaske.
"Mun nuna rashin daɗin mu kan abin da ya faru, wannan abin bai kamata ba kan mutanen da suka fito su are rayukan ƴan ƙasa," in ji Aleru.
Ya ce ba wata ƙasa a duniya da za ta lamunci irin haka.
Sanata Aleru ya ce kwamitocin sojin ƙasa da sojin sama da kuma na ruwa za su tattauna da manyan hafsoshin tsaron ƙasar wajen ganin an zaƙulo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da hukunta su don haka ya zama darasi ga na baya.
Majalisar dattawan ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta biya diyya ga iyalan sojojin 17 da aka kashe.

Asalin hoton, Getty Images
Tunisiya da Libya sun rufe wata babbar mashigar kan iyaka bayan hare-haren da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai suka kai.
Ministan harkokin cikin gidan gwamnatin Libya mai hedkwata a birnin Tripoli ya bayyana cewa ‘yan ta’adda sun kai hari kan iyakar Ras Jdir inda ta nan ne ‘yan ƙasar Libya da dama ke shiga ƙasar Tunisiya, yayin da manyan motocin da ke ɗauke da kaya ke shige da fice.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Libiya ta ce tuni aka tura dakaru zuwa yankin domin yaki da fasa-kwauri da kuma tunkarar matsalar rashin tsaro.
Wasu ƙungiyoyi masu harkar kasuwancin man fetur a Najeriya sun ce abu ne mai wuya a samu saukin farashin man fetur idan matatar man fetur ta Fatakwal ta soma aiki nan da makoni biyu.
Ƙungiyoyin sun mayar da martani akan hasashen da ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa ta yi akan cewa za a samu raguwa a farashin man fetur nan ba da jimawa ba.
Bashir Ahmad Dan malam wanda shi ne shugaban ƙungiyar Arewa oil and gas marketers Association watau ARO-GOMA, ya ce saukin ya danganta ne a kan wasu dalilai.
Ga ƙarin bayanin da ya yi wa Raliya Zubairu.

Asalin hoton, Getty Images
Bangladesh da Pakistan da Indiya sun kasance kan gaba a jerin ƙasashen da suka fi fuskantar gurɓacewar iska a shekara ta 2023.
Rahoton hukumar da ke sa ido kan ingancin iska a duniya IQAir ta fitar, ya bayyana cewa ƙasashe bakwai ne kawai suka cika ka'idojin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta gindaya na samar da iska mai tsafta.
An gano cewa ƙasar Bangladesh tana da adadin gurɓatacciyar iska da motoci da masana'antu ke haifarwa har sau 16, wanda hakan kan iya lalata huhu da kuma haddasa mutuwa kwatsam.
Chadi, Iran da Pakistan na daga cikin ƙasashe uku na farko a shekarar 2022.
Daga cikin birane 100 da suka fi gurɓata muhalli a duniya a bara, 83 daga cikinsu suna Indiya.
Shugaban ƙasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Deby, ya kai ziyara kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen yada labarai dangane da makasudin ziyarar tasa, musamman dangane da rikicin kasar Sudan.
Rahotanni daga shafin yada labarai na TchadOne masu goyon bayan ‘yan adawa sun bayyana cewa, ziyarar ta zo daidai da matsin lamba da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi kan Mahamat domin kara kaimi ga kasar Chadi a rikicin ƙasar Sudan, musamman bayan koma bayan da dakarun RSF suka fuskanta a Khartoum da Omdurman.
A tarihi dai Hadaddiyar Daular Larabawa ta kasance kawa ce ga dakarun RSF, inda ta samar da mayaka ga yakin da Saudiyya ke jagoranta, da ke samun goyon bayan Hadaddiyar Daular Larabawa a Yaman.
Majiyoyi da TchadOne ya ruwaito sun nuna cewa Masarautar tana neman Chadi ta shiga tsakani kai tsaye a rikicin Sudan don tallafawa Hemedti, shugaban RSF.
Shirin da aka gabatar ya kunshi tura dakaru masu yawa, dauke da makamai da kuma tallafin da Hadaddiyar Daular Larabawa za ta ba su, domin ƙaddamar da ayyuka a Khartoum da Port Sudan.
Hukumomin kasar Chadi sun karyata ikirarin da gwamnatin sojan kasar ta Port Sudan ta yi, inda ta yi zargin cewa kasar Chadi ta ɗauki nauyin shigar da tallafin sojan da Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi ga kungiyar RSF.
A halin yanzu, ƙasar Chadi tana karbar bakuncin 'yan gudun hijirar Sudan sama da 500,000, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Ana ci gaba da kokarin hada kai agajin jin kai daga kasar Chadi zuwa Sudan domin magance matsalolin da ke tasowa sakamakon rikicin da ake fama da shi a makwabciyar kasar.
A yankin Ouham da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya (CAR), kusan fararen hula 60 ne aka kashe a wani hari da aka ce sojojin hayar Wagner na Rasha suka kai.
Lamarin ya faru ne a kusa da garin Kouki a wuraren haƙo ma'adanai na Kotabara da Zaranga a ranar 9 ga watan Maris, kamar yadda shafin yaɗa labarai na 'yan adawa Corbeau News Centrafrique ya ruwaito.
A cewar shaidu, an yi wa fararen hula da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara kisan gilla ta hanyar da ba ta dace ba.
Rahotanni sun nuna cewa sojojin hayar sun nufi wuraren da ake haƙar ma'adinan ne domin sace zinare.
Wannan harin ya ƙara tabbatar da hare-haren da sojojin hayar ke kai wa wuraren haƙar ma'adinai, wanda ake zargin suna amfani da shi wajen samar da ayyukan tsaro ga gwamnatin CAR.

Jagoran ƙungiyar ƴan awaren Biyafara masu neman ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu ya koka kan halin da yake ciki a hannun jami'an hukumar tsaro ta farin kaya - DSS.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana gaban babbar kotu a ranar Talata domin ci gaba da sauraron ƙararsa kan tuhumar cin amanar ƙasa da ta'addanci.
Ana yi masa tuhume-tuhumen ne da suka shafi tayar da husuma da kuma cin amanar ƙasa sanadiyyar gwagwarmayar da ƙungiyarsa ke yi a gabashin Najeriya na ganin ta zama ƙasa mai cin gashin kanta.
A harabar kotun, Kanu ya ɗage rigarsa domin nuna cewa ba a bashi kulawar da ta kamata inda ya yi iƙirarin cewa "zan mutu a hannun DSS."
Shugaban na Ipob ya nuna wani ɓangare na jikinsa da ke da tabo bayan da kotu ta ba shi damar magana game da buƙatarsa ta neman beli da kotun ta yi watsi da ita.
Kanu ya ce ya na fama da matsalar ciwon zuciya sai dai magugunan da ake ba shi a hannun DSS "ba su da amfani".
Ya ƙara da cewa DSS ba ta ba shi damar ganin likitan da yake so ba.
"Zan mutu a hannun DSS kuma suna ba ni magani mara tasiri. Suna duba ni game da matsalar zuciya amma maganin da suke ba ni ba shi da amfani. Suna son na mutu a tsare," in ji Nnamdi Kanu.
Jagoran na Ipob ya buƙaci kotun ta mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje sai dai mai shari'a Nyako ta ce tana da ikon ajiye Kanu duk inda ta ga babu barazanar tsaro.
Mai shari'a Nyako ta nemi a ci gaba da tsare Kanu a hannun DSS.

Asalin hoton, CHIDI OKEKE TV
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda ke nuna wani fitaccen jarumin fina-finan Nollywood Amaechi Muonagor cikin yanayi na rashin lafiya yana neman tallafin kuɗi, ya jefa ƴan Najeriya da dama cikin kaɗuwa.
A bidiyon, an gan shi kwance kan gado da bandeji a ƙirjinsa, yana magana da kyar.
Wani ɗan fim ɗin zaune kus da shi yana bayani cewa Muonagor yana buƙatar kuɗi domin a yi masa aikin dashen ƙoda.
Labarin ya bazu ne yayin da ƴan Najeriya suke cikin jimamin mutuwar shahararren ɗan fim ɗin Nollywood, John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu da shi ma ya buƙaci agaji.
A bidiyon da aka fitar ranar Litinin, Muonagor cikin damuwa, yana magana a harshen Igbo inda yke cewa: "Al'ummar Igbo, ina gaishe ku baki ɗaya."
Bai iya ƙarasa magana ba, sai jarumi Kingsley Orji ya ci gaba da bayani yana cewa jarumin yana fama da matsalar ƙoda.
"Babu sauƙi. Ya shafe watanni yana cikin wannan yanayin. Yana son a yi masa dashen ƙoda," in ji Orji.
"Bai daɗe da dawowa daga sashen masu fama da ciwo mai tsanani ba...kwanakin baya. Yana samun sauƙi amma ba sosai ba.
"Mun yanke shawarar mu mayar da shi gida saboda babu kuɗi amma hakan ba shi ne ya fi dacewa ba. Da ƙyar yake iya magana. Don Allah yana buƙatar taimakonku," ya ƙara da cewa.
Mutane da dama sun yi ta bayyana rashin jin daɗinsu bayan ganin bidiyon inda suka ce suna yi wa jarumin addu'ar samun sauƙi da kuɗi.
Muonagor ya yi fina-finai da dama har da Aki da Pw Paw, ɗaya cikin fim ɗin da ya taka rawa sosai inda ya fito a matsayin mahaifin matasan masu jini a jika.

Mai sharia'a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata, ta ki amincewa da belin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.
Sai dai kotun ta bayar da umarnin a gaggauta sauraron shari’ar Kanu wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi cin amanar kasa.
Kanu, wanda aka gabatar da shi gaban kotu a ranar Talata, yana tsare ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun bayan kama shi a watan Yunin 2021 domin yanke hukunci kan neman belin sa.
Nyako ta ce kotun za ta bayar da damar ci gaba da sauraron shari’ar ne kawai, sannan ta umarci masu gabatar da kara da su gabatar da shaida na farko.
Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya nuna rashin jin dadinsa da hukuncin.
Ya ce ƙungiyar lauyoyin Kanu ba za ta iya ci gaba da shari’ar ba idan ba a ba su damar yin magana da wanda suke karewa ba.
Ejimakor ya kara da cewa ganawa da Kanu a hannun DSS abu ne mai matuƙra wahala, domin kullum ana sa ido a kan hirar su, kuma Kanu na sanye da irin kayan da kotu ta ce a canza masa.
Ya yi zargin an yi wa Kanu rashin adalci, wanda a cewarsa ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya nuna rashin gamsuwar tawagar lauyoyin Kanu, sannan ya bukaci a dakatar da shari’ar don ba su damar tuntubar wanda yake karewa, wanda kotu ta amince.
Kanu ya nemi ya yi magana a kotu kuma an amince da bukatarsa.
Ya shaida wa kotun cewa yana fama da ciwon zuciya kuma ba ya samun kyakkyawar kulawa a hannun hukumar DSS.
Ya nemi a kai shi gidan yarin Kuje ko kuma a ɗaure shi a gida amma mai shari’a Nyako ta ƙi amincewa da rokonsa wanda daga bisani ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 17 ga Afrilu, 2024 don fara shari’a.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka da za ta bukaci 'yan kasar su biya harajin kashi 1.5 cikin 100 na wata-wata domin samar da kudaden gina gidaje masu rahusa.
Dokar gidaje masu araha ta 2024 ta sake dawo da wani harajin tilas wanda gwamnati ta fara cirewa a watan Yulin da ya gabata daga ma'aikata da waɗanda ke ɗaukansu aiki.
Kotuna dai sun ayyana harajin gidaje a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulki saboda babu wani tsarin doka da zai goyi bayan hakan.
Sun kuma yanke hukuncin cewa harajin ya shafi 'yan kasar Kenya da ke aiki a fannin na yau da kullun wanda wi hakan ya nuna rashin adalcin.
Sabuwar dokar da majalisar dokokin ƙasar ta amince da ita a makon da ya gabata, ta yi kokarin magance batutuwan da kotuna ta gabatar.
An saka 'yan kasuwa a cikin tsarin kuma ana buƙatar ba da gudummawar kashi 1.5 cikin 100 na yawan kuɗin da suke samu a kowane wata.
Sabon harajin zai fara aiki ne a karshen wannan wata kuma ba za'a mayar da shi baya ba.
Shugaba Ruto ya bayyana cewa asusun samar da gidaje ya tanadi gina gidaje kusan 200,000 a duk shekara wanda ya ce zai samar da ayyukan yi akalla 500,000 a kowace shekara.
Wannan harajin dai ya janyo ce-ce-ku-ce daga ɓangaren 'yan adawa da kuma wani ɓangare mai yawa na 'yan kasar Kenya, waɗanda ke jin nauyi na harajin da aka bullo da shi a karkashin mulkin shugaba William Ruto.
Masu sukar lamirin sun yi nuni da cewa kudirin ba zai iya magance musabbabin rikicin gidaje ba kuma zai buɗe hanyar yin cin hanci da rashawa.
Shugaba William Ruto ya ce aikin na ɗaya daga cikin kokarin gwamnati na inganta gidaje masu saukin kudi a kasar.

Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce ɗaukacin mutanen Gaza miliyan biyu na fuskantar matsanancin karancin abinci.
Wannan shi ne karon farko da aka ware ɗaukacin al'ummar kasar, in ji shi lokacin da BBC ta yi masa tambayoyi game da yanayin yankin.
Blinken ya yi kira ga Isra'ila da ta ba da fifiko wajen samar da mabukata da abinci.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun ce arewacin Gaza na iya fuskantar yunwa nan da watan Mayu ba tare da dakatawa ba a fadan da kuma karuwar buƙatar agaji.
Gargadin na Blinken ya zo ne a wata ziyarar da ya kai kasar Philippines, yayin da jami'an Amurka suka sanar da cewa zai je yankin Gabas ta Tsakiya, ziyararsa ta shida a yankin tun cikin watan Oktoba, yayin da ake ci gaba da kokarin tsagaita bude wuta.
A yau talata ne masu shawarwarin Isra'ila zasu fara tattaunawa a Qatar a wani sabon yunƙuri na cimma yarjejeniya da Hamas don dakatar da faɗan da shigar da kayan agaji da kuma fitar da mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su.
Kalaman na Blinken na daga cikin mafi karfinsa wajen bayyana girman matsalar jin kai a Gaza.
Ya sake yin kira ga Hamas da ta ajiye makamai amma ya ce ya zama wajibi Isra'ila ta ba da fifiko wajen samar da kayan agaji ga wadanda ke tsananin bukatar agaji.

Kotun ɗaukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da Felix Okonkwo lauyan da ke kare Nnamdi Kanu, jagoran masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) da ake tsare da shi ya shigar kan zargin kama shi da tsare shi da ‘yan sanda da jami'an tsaron farin kaya suka yi ba bisa ka’ida ba.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Okon Abang ya yi watsi da ɗaukaka karar, inda ya bayyana cewa ba shi da inganci.
Ya yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da karar ya kasa nuna rashin adalci a hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan lamarin.
Abang ya jaddada cewa, hujjojin bidiyon da masu karar suka gabatar a lokacin shari’ar ba su nuna wani hannun jami’an DSS ba a wurin da aka kama su a gidan Ifeanyi Ejiofor a jihar Anambra.
Dangane da diyyar naira miliyan biyu da aka ce ƴandan da DSS su bayar, mai shari’a Abang ya ki amincewa da hujjar wadanda suka shigar da kara na cewa adadin kuɗin bai wadatar ba, inda ya ce hurumin tantance diyya ya rataya a wuyan alkali ne kawai.
Bugu da kari, Mai shari’a Abang ya lura cewa wadanda suka shigar da ƙarar sun kasa bayar da bayanan da suka dace kamar matsayinsu a al’umma da kuma asarar da suka yi a lokacin da ake tsare da su.
Wadanda suka shigar da karar da suka hada da Felix Okonkwo da Ikenna Chibuike, da Okafor Ugochukwu, sun shigar da karar ne a gaban babbar kotu kan jami’an ‘yan sandan Najeriya da kuma hukumar DSS, inda suke zargin su da take hakkinsu.
Sun zargi jami’an tsaro da kama su da tsare su ba bisa ka’ida ba a watan Satumban 2021, inda suka yi iƙirarin cewa ana azabtar da su da cin zarafinsu da kuma tursasa musu.
A wani hukunci da ya yanke a ranar 24 ga Maris, 2022, Mai shari’a Samaila Bature ya samu ‘yan sanda da laifin kamasu da tsare su ba bisa ka’ida ba tare da ci musu tarar Naira miliyan biyu a kansu.
Sai dai babu wani mataki da aka ɗauka a kan hukumar ta DSS domin wadanda suka shigar da karar ba su gano dalilin daukar matakin a kansu ba.

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a jihar Gedaref da ke gabashin Sudan ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani dan dakarun RSF a wani mataki na murkushe sojojin da ke yaki da sojojin ƙasar tun tsakiyar watan Afrilun 2023, in ji kamfanin dillancin labarai na Sudan.
Wannan shi ne karo na farko da gwamnatin mulkin sojan Sudan ta yanke hukuncin kisa a lokacin rikicin.
A ranar 15 ga Maris, Kotun hukunta manyan laifuka ta Gedaref ta Gabas ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu da ake zargin mambobin dakarun RSF da masu goyon bayansu, yayin da wasu kuma aka daure su na tsawon shekaru bakwai.
A watan Agustan 2023, gwamnatin soja ta kafa kwamitin kan laifuffukan yaƙi da cin zarafi don bincikar take haƙƙin ɗan adam da sauran laifukan da RSF ta aikata.
A gefe guda kuma, an kashe ko jikkata “yawan fararen hula” a rana ta uku a jere ana gwabza fada tsakanin sojoji da RSF a garin Babanusa da ke yammacin jihar Kordofan, kamar yadda shafin intanet na Sudan Tribune mai zaman kansa ya ruwaito jiya.
Yaƙin da ake gwabzawa ya yi ɓarna sosai a sassan Babanusa tare da raba sama da fararen hula 50,000 da muhallansu yayin da RSF ke yunkurin kwace wasu sansanonin sojoji biyu a jihar.