Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Usman Minjibir and Abdullahi Bello Diginza

  1. Za a yi jana'izar sarki Olubadan na 42 a yau Juma'a

    ..

    Asalin hoton, DELE OGUNSOLA

    Anjima a yau Juma'a ne za a yi jana'izar sarki Olubadan na 42 a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

    Sarki Olubadan na Ibadan, Oba Olalekan Balogun ya mutu ƴan kwanaki bayan ya yi bikin cikarsa shekara biyu kan karaga.

    Kakakin Sarkin, Dele Ogunsola ne ya tabbatar da mutuwarsa a ranar Alhamis.

    Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde shi ma ya tabbatar da mutuwar sarkin yana shekara 81 a wata sanarwa da ya fitar.

    Gwamna Makinde ya bayyana cewa sarkin wanda shi ne Olubadan na 42 ya mutu ne a asibitin koyarwa na jami'ar UCH da ke jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya.

    Gwamna Makinde ya bayyana sarkin a matsayin mutumin da ya cimma nasarori da dama da suka zama ci gaba ga Ibadanland cikin shekara biyun da ya yi yana mulki.

    "Babban bango ya faɗi; Sarki Dakta Balogun ya rasu," in ji gwamna Makinde.

    Kola Balogun, wanda ƙani ne ga sarkin ya ce za a yi jana'izar sarkin a gidansa da ke Aliiwo, kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

    Wane ne marigayi Sarki Olubadan na 42?

    Marigayi sarki Oba Olalekan Balogun ɗan siyasa ne, ɗan kasuwa kuma tsohon sanata.

    An haife shi a Balogun cikin watan Oktoban 1942.

    Balogun ya taɓa zama mamba a hukumar gudanarwar manyan kamfanoni da dama a Najeriya da ƙasashen waje, musamman a ɓangaren man fetur da noma da kasuwanci da shugabanci da yawon buɗe ido.

    Ya kuma taɓa riƙe muƙamai da dama a kamfanin mai na Shell.

    Ya yi karatu a jami'ar Columbus International da jami'ar Brunel da kuma jami'ar Manchester - dukkansu a Birtaniya.

    A fagen siyasa, Balogun tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne a Najeriya a ƙarƙashin jam'iyyar SDP.

    Ya kuma taɓa yi wa PDP takarar gwamna a jihar Oyo.

    Daga bisani, Balogun ya zama sanata a Najeriya.

  2. Sojojin Najeriya sun yi alƙawarin kuɓutar da ɗaliban Kuriga

    ..

    Asalin hoton, X/DEFENCE HQ

    Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin kuɓutar da fiye da ɗalibai 200 da ƴanbindiga suka sace a baya-bayan nan a jihar Kaduna.

    Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja game da ayyukan rundunar sojin a makonni biyu da suka gabata, Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ya ce sojojin a shirye suke su ceto ɗaliban ba tare da an rasa rai ba.

    Ya kuma ɗora laifin sace ƴangudun hijira a kwanakin da suka gabata daga Gamboru-Ngala a jihar Borno kan rashin mutunta umarni inda suka fita daga sansanin domin neman itacen girki ba tare da sanar da jami'ai ba.

    Tun dai bayan sace ɗaliban ne, shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su gano ƴanbindigar tare da kuɓutar da ɗaliban inda ya nanata cewa gwamnati ba za ta biya kuɗin fansa ba.

    Bayan taron majalisar zartaswa na ranar Laraba ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammad Idris ya bayyana hakan inda ya shaida wa ƴanjarida cewa shugaba Tinubu ya nanata umarnin tabbatar da kuɓuto ɗaliban da mayar da su ga iyalansu lami lafiya.

    • Abin da ya sa gwamnoni ba su da karfin iko kan jami’an tsaro
    • Ƙarin 'yan Najeriya sun shiga tashin hankali saboda ƙazancewar rashin tsaro
  3. An saki Ousmane Sonko daga gidan yari gabanin zaɓen Senegal

    ..

    Asalin hoton, AFP

    An saki Madugun ƴanhamayyar Senegal Usman Sanko daga gidan yari, gabanin babban zaɓen ƙasar.

    Lauyan mista Sanko ya bayar da tabbacin sakin nasa tare da ɗan takarar shugaban ƙasar da yake goyon baya, Bashiru Jomaye.

    An saki ƴanhamayyar ne a ƙarƙashin wani shiri na afuwa da Shugaba Macky Sall ya sanar a watan da ya gabata.

    Jagoran ƴanhamayyar na Senegal tare da ɗan takarar da yake mara wa baya, a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi, nan gaba a wannan wata sun samu kansu ne, daga garƙame su da aka yi, albarkacin shirin afuwa da Shugaban ƙasar Macky Sall ya yi bayan wata doka da majalisar dokokin ƙasar ta amince da ita, da nufin yayyafa wa wutar rikicin siyasar ƙasar ruwa.

    Rikicin da ya haddasa tarzoma saboda ɗage zaɓen shugaban ƙasar na watan fabarairu da Shugaba Sall ya yi.

    Lauyan Mista Sonko, Bamba Cisse, shi ne ya tabbatar da sakin jagororin hamayyar biyu.

    Wani hoton bidiyo da aka sanya a intanet ya nuna cincirundon mutane suna yabo da rera sunan Mista Sonko a titunan babban birnin ƙasar, Dakar

    Mutane da dama daman su zaƙu da sanin makomar ƴansiyasar biyu kafin babban zaɓen ƙasar ta yammacin Afirka

    Shi dai Mista Sonko an haramta masa shiga takara a zaɓen wanda a yanzu za a yi ranar 24 ga watan nan na Maris, saboda kotu ta same shi da laifin ɓata suna abin da ya ce siyasa ce kawai.

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Shi kuwa Bachirou Diomaye Faye mai shekara 44, wanda yana ɗaya daga cikin ƴantakara 19 a zaɓen, ana sa ran ya fara yaƙin neman zaɓensa daga yau Juma'a.

    Yacine Fall, mataimakin shugaban jam'iyyar PASTEF da aka rushe, wanda a yanzu yake goyon bayan Faye, ya ce sun yi matuƙar farin ciki da sakin mutanen biyu.

    Ya ce tun da farko ma bai kamata a ce sun je gidan yarin ba, amma yanzu tun da an sako Ousmane Sonko, da kuma ɗantakararsu Bachirou Diomaye Faye, za su iya ci gaba da yaƙin neman zaɓe, kuma ya ce suna da tabbacin samun nasara.

    Shi kuwa Sonko mai shekara 49 yana kan gaba ne wajen hamayya da Shugaba Sall, amma aka ɗaure shi a watan Yuli na 2023, a kan abin da ya ce, zargi ne da aka kitsa domin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasar.

    Duk da sauye-sauyen da aka yi na siyasa, har yanzu ba a sauya jerin sunayen ƴantakarar da ka ce sune suka cancanta tsayaw zaben ba, wanda hakan ke nufin Mista Sonko ba zai shiga takara ba.

    Ɗansiyasar na hamayya yana da farin jini musamman a tsakanin matasa marasa aikin yi ƴanƙasar ta Senegal, saboda alƙawarin da ya yi na gudanar da sauye-sauye masu tsauri.

    A farkon shekarar da ta wuce ne, 2023 ya kafa jam’iyyar Pastef-Les Patriotes, wadda gwamnati ta rushe

    A zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a 2019 ya zo na uku inda ya samu kashi 15 cikin ɗari na ƙuri’un da aka jefa.

    Zaɓen ƙasar na bana a da an tsara yin sa ne a ranar 25 ga watan Fabarairu, amma aka mayar da shi ranar 24 ga watan nan na Maris bayan hukuncin kotu.

    • Abin da ya kamata ku sani game da madugun adawa Ousmane Sonko
    • An sanar da ranar zaben shugaban kasar Senegal
  4. Barka da wannan lokaci!

    Barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a wannan hantsi na Juma'a - babbar rana.

    Nabeela Mukhtar Uba ke fatan kun tashi lafiya.

    Za mu kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu daga bisani kuma mu miƙa ragama ga sauran abokan aiki,

    Ku biyo mu.