Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage
Isra'ilawa sun buƙaci a gaggauta sakin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su

Asalin hoton, Reuters
Dubban Isra'ilawa a birnin Tel Aviv sun buƙaci a gaggauta sakin 'waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su tare da buƙatar Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi murabus.
'Yan sanda sun kama mutum 16, tare da amfani da feshin ruwa domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Tun da fari cibiyar bayanan sirri ta Mossad, ta ce masu shiga tsakani na ta tuntuba kan yarjejeniyar tsagaita wuta, da sakin waɗanda akai garkuwa da su amma babu alamun cimma nasara.
Amurka da Sifaniya sun aike wa Falasɗinawa kayan tallafi

Asalin hoton, EPA
Rundunar sojin Amurka ta ce jirgin ruwa na dakon kaya ɗauke da kayan agaji da za a kai Gaza na kan hanyar tekun Mediterranean.
Jirgin irin sa na farko, na ɗauke da kayan aikin da za a haɗa gada a cikin ruwa da za a sauke kayan da jirgin ke ɗauke da shi.
A ɓangare guda kuma wani jirgin ruwan Sifaniya shi ma ɗauke da tan dubu 200 na kayan agaji, zai taso dada tashar ruwa ta Cyprus.
Kungiyoyin agaji dai sun yi gargaɗin Falasdinawa na fama da matsananciyar yunwa sakamakon yaki tsakanin Isra'ila da Hamas da ake cikin wata na biyar da barkewa.
Sallama
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun karshen mako.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.
Amma kamar kullum, za mu fi mayar da hankali ne kan Najeriya da makwabtan ƙasashe.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.
