Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge

  1. DR Kongo ta musanta ƙulla yarjejeniya da Rasha

    DR Congo

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ta musanta Ƙulla yarjejeniyar soji da Rasha.

    A farkon wannan mako ne kamfanin dillancin labarai na Rasha Tass ya bayar da rahoton cewa Moscow ta amince da daftarin yarjejeniyar haɗin gwiwa da DR Kongo da ta ƙunshi atisaye da horas da dakarun ƙasar.

    Batun yarjejeniyar haɗin gwiwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun takun saka tsakanin DR Kongo da makwabciyarta Rwanda.

    Gwamnatin Kinshasar na zargin Rwanda da mara wa 'yan tawayen gabashin ƙasar baya, zargin da Kigalin ta sha musantawa.

    • Isra'ila ta hana shigar da abinci Gaza - MDD
    • Yadda karancin maganin kashe radadi ke jefa mutane cikin mawuyacin hali a Gaza
  2. Shugaba Tinubu bai fahimci mulkin Najeriya ba - Ningi

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, fb/Bola Tinubu

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

    Wasu ƴan Majalisar Dattijan Najeriya a ɓangaren jam'iyyun hamayya sun ce alamu sun nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu bai fahimci mulkin kasar ba.

    Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya, Abdul Ahmed Ningi wanda ɗan jam’iyyar hammaya ta PDP ne, ya ce abubuwan da shugaba Tinubu ya samu a ƙasa sun tabarbare saboda irin wahalhalun da jama'a ke ciki.

    Ya ce: ''Bola Tinubu bai fahimci wannan kasar sosai ba, kuma bai fahimci wahalar mulki na kasa irin Najeriyar nan ba. Ba na ganin laifin sa da yawa saboda lokacin da yake neman shugabanci, ba wani alkawari da ya yi tsakanin sa da mutane, kawai mutane sun rufe ido ne sun zabe shi watakil saboda ya goyi bayan Buhari a lokacin da ya ke neman shugabanci, wasu kuma suna ganin ai musulmi ne saboda haka a goyi bayansa ko zai iya ko ba zai iya ba.''

    Sanata Ningi ya kuma yi zargin cewa babu wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin mutanen da suka shige gaba wajen neman a zabi Tinubu a Arewacin Najeriya, da kuma shugaban kasa, ta fannin tsare tsaren ayyukan da ya kamata a yi wa yankin a lokacin mulkin sa.

    Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriyan ya kuma koka da halin da yan adawa suka shiga a majalisar dokokin kasar, wanda ya ce yana faruwa ne saboda yadda aka yi wa yan adawar karfen kafa wajen nadin shugabanni.

    Latsa lasifikar da ke ƙasa domin sauraron tattaunawar da Buhari Fagge ya yi da Sanata Ningi.

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraro
  3. RANAR MATA: Oluremi Tinubu ta buƙaci a bunƙasa rayuwar mata

    Oluremi Tinubu

    Asalin hoton, OLUREMI TINUBU/FACEBOOK

    Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta yi kiran a kara mayar da hankali wajen inganta rayuwar mata.

    Ta yi wannan kiran ne a sakonta na taya murnar ranar mata ta bana, inda ta yi nuni da bukatar a bayar da himma wajen tafiya da mata a fannin tattalin arziki da ci gaban al'umma.

    Sanata Oluremi Tinubu ta ce; “Lokaci ya yi da za a karfafa gwiwar mata fiye da yadda aka saba a baya. Mata suna da muhimmanci sosai ga kokarin kawo ci gaba, saboda da haka ya kamata a tsara duk wata harkar ci gaba tare da su.

    Uwargidan shugaban Najeriyar ta ce tana kallon bunkasa rayuwar mata a matsayin hanyar kawo ci gaban kasa da al'ummar ta.

    Ta ce; “Tambayata ga mata ita ce: me kuke yi wajen taimakon sauran mata? Ta wace hanya kuke kokarin inganta rayuwar mata?

    • Matar da ke gyaran burtsatse don samar wa mutanenta tsaftataccen ruwa
    • Asali da muhimmancin ranar mata ta duniya
  4. Yadda wani yaro ya kulle damisa cikin a ɗakinsa

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Wannan bidiyon ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda wani yaro mai shekara 12, mai suna Mohit Ahire daga jihar Maharashtra ya kulle wata damisa a cikin ɗakinsa bayan da ta kutsa ɗakinsa.

    Ahire yana tsaka da yin game a waya, a kusa da kofar ɗakinsa, yayin da damisar ta kutsa kanta cikin ɗakin nasa.

    Sai ya yi a hankali ya zare cajar wayarsa, ya janye jikinsa daga ɗakin, tare da rufe ƙofar ya barta a ciki.

    Daga baya dai jami'an hukumar lura da gandun dajin jihar sun kamota tare da mayar da ita inda take.

  5. 'Yan sanda Hong Kong za su riƙa tsare waɗanda ake zargi har tsawon kwana 16

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Hong Kong ta tafka mahawara kan wani daftarin dokar tsaron kasa da masu sukar gwamnati ke cewa zai ƙara rage hakkin alummar yankin.

    Dokar za ta bai wa 'yan sanda damar tsare waɗanda ake zargi na tsawon kwanaki 16 ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba.

    A halin yanzu dai 'yan sandan za su iya tsare waɗanda ake tuhuma ne na tsawon kwanaki biyu ne kawai.

    Haka kuma ƙudurin ya nemi a yanke hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan yari a kan abinda ya kira bayanan da aka wallafa domin tayar da zaune-tsaye

  6. MDD ta fitar da rahoton cin zarafin Falasɗinawa a Zirin Gaza

    .

    Asalin hoton, Reuters

    BBC ta ga wani rahoto na cikin gida na wata hukumar MDD da ke aiki a zirin Gaza da ya bayyana yadda aka rika cin zarafin Falasɗinawa a cibiyoyin tsare mutane na wucin gadi na Israila.

    Takardun na hukumar kula da falasɗinawa masu gudun hijira ta UNRWA sun dogara ne a kan hirar da aka yi da fiye da mutum 100 da aka sako daga wasu cibiyoyin tsare mutane na rundunar sojin Israila tun watan Disamban bara.

    Mutanen da aka tsare sun yi bayani a kan yada aka tuɓe su tare da yi mu su dukan tsiya sannan karnuka sun riƙa kai mu su hari, sannan kuma an tsaresu na tsawon sa'o'i a cikin wani yanayi mai wahalar gaske tare kuma da cin zarafinsu ta hanyar lalata .

    Bayanan sun yi kama da bayanan da ƙungiyoyin kare hakkin bil-dama na Israila da Falasɗinawa suka wallafa a baya bayanan.

  7. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkan mu da wannan rana ta Juma'a da Hausawa ke yi wa kirari da Haji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza tare da Haruna Ibrahim Kakangi ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, don kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta