DR Kongo ta musanta ƙulla yarjejeniya da Rasha
Gwamnatin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ta musanta Ƙulla yarjejeniyar soji da Rasha.
A farkon wannan mako ne kamfanin dillancin labarai na Rasha Tass ya bayar da rahoton cewa Moscow ta amince da daftarin yarjejeniyar haɗin gwiwa da DR Kongo da ta ƙunshi atisaye da horas da dakarun ƙasar.
Batun yarjejeniyar haɗin gwiwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun takun saka tsakanin DR Kongo da makwabciyarta Rwanda.
Gwamnatin Kinshasar na zargin Rwanda da mara wa 'yan tawayen gabashin ƙasar baya, zargin da Kigalin ta sha musantawa.
- Isra'ila ta hana shigar da abinci Gaza - MDD
- Yadda karancin maganin kashe radadi ke jefa mutane cikin mawuyacin hali a Gaza