Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge
Bankwana
Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.
Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.
Kashi 95 na waɗanda malaria ke kashewa a Afrika suke - WHO
Ministocin lafiya a ƙasahsen da ke fama da yawan Malaria a Afrika, sun ɗauki alƙawarin kawo ƙarshen mace-macen da cutar ke yanjowa.
Wannan na zuwa n yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da cewa yankin Afrika ne ke samar da kashi 95 na mace-macen da ake yi sakamakon malaria.
WHO ta wallafa a shafinta cewa Ministocin yayin wani taro da suka yi a birinin Yaounde na Kamaru sun sanya hannu kan wani ƙudiri na gagguta kawo ƙarshen malariya da ke yi wa Afrika barazana.
A cewar alƙaluman WHO yankin Afrika ne ke ɗauke da ƙasashe 1 da ke samar da kimanin kashi 70 na matsalar malaria.
Cikin ƙasashen akwai Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da Ghana da Mali da Mozambique da Niger da Nigeria.
Sauran su ne Sudan da Uganda kuma Tanzania waɗanda dukansu ke fama da cutar ba dare ba rana tun daga shekarar 2017.
Unicef ta yi alla-wadai da sace ɗaliban Kuriga
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya yi tur da hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan makarantu a jihar Kaduna.
Shugabar Asusun a Najeriya, Cristian Munduate, ta nuna rashin jin daɗinta sakamakon harin, inda ta ce ya kamata kowane yaro ɗan Najeriya ya samu damar koyon ilimi cikin kwanciyar hankali.
Ta ce ya kamata a ce makarantun su zama wurin koyo da ci gaba, ba wai wuraren fargaba da tashin hankali ba.
Cikin sanarwar, "na kaɗu matuƙa da rahotannin satar ɗalibai a jihar Kaduna. Ƙaruwar irin waɗannan sace-sace a sassan ƙasar na nuna wata matsala da ke buƙatar a gaggauta ɗaukan mataki daga dukkan matakan gwamnati da kuma su kansu al'umma." in ji Munduate.
Unicef ya kuma buƙaci a gaggauta ɗaukan matakin tabbatar da maido da yaran da aka sace, inda kuma ya yi kira ga hukumomi da su ɗauki ƙwararan matakai don tabbatar da tsaro a sassan Najeriya.
A cewarta, ya zama dole a tabbatar wa ɗalibai da malamansu tsaro domin makarantu su iya sauke nauyinsu na zama wuraren samun ilimi da ci gaba.
A shekarun baya-bayan nan ana samun ƙaruwar satar ɗalibai a makarantu a sassa daban-daban na Najeriya.
- Matsalar ƴan bindiga ta dawo sabuwa a wasu yankunan jihar Katsina
- Ƴan Boko Haram sun sace gwamman mutane a Ngala na jihar Borno
Lemar tallafin kayan abinci ta kashe mutum biyar a Gaza
Wani tallafin kayan abinci na jin kai da aka jefa daga jirage ta sama a yankin zirin Gaza ya kashe akalla mutum biyar.
An ce lamarin ya auku ne a sansanin 'yan gudun hijira na Al Shati da ke arewacin zirin, sakamakon yadda lemar sauka da aka makala kayan jin kan ta gaza budewa kamar yadda aka saba.
Wani wanda ya gane wa idonsa aukuwar hadarin, ya ce laimar ta dira ne da karfin gaske.
Muna cikin ibtila'in rashin ƴaƴanmu da aka sace a Kuriga – Iyaye
Ɗaya daga cikin iyayen ɗalibai 287 da ƴan bindiga suka sace daga wata makarantar Firamare a Kuriga da ke jihar Kaduna ta yi kira ga hukumomi su yi duk abin da ya kamata domin kuɓutar da yaran.
A hirarta da BBC, mahaifiyar wadda har yanzu bata ga 'yarta ba, ta bayyana yadda ta rabu da ƴartata gabanin a kai harin da aka yi garkuwa da su.
"Ta fita da larura, jikinta ba ta jin daɗi, na kora ta a kan ta tafi makaranta kar ta yi latti ko karyawa ba ta yi ba, ƴan bindiga suka kawo mamaya, sun mamaye makarantar nan,"
"Ba ta inda yaranmu za su fita sai wanda Allah ya tseratar, sun bar mu cikin halin ibtila'i, muna hangen ƴaƴanmu ana kora mana su, mun yi kuka, Uba Sani ka taimaka mana." in ji mahaifiyar.
Ta ce akwai matsalar rashin tsaro a Kuriga gami da yunwa da suke fama da ita a yankin.
A cewarta, makarantar ce kaɗai abin da suke cin moriya daga gwamnati.
Cikin shesshekar kuka ta ce ƴan bindigar "sun hana a yi noma, sun hana a yi kiwo, an bar mu cikin talauci kamar ba ma tare da gwamnati." kamar yadda ta faɗa.
Ita ma wannan mahaifiyar ta bayyana yadda lamarin ya faru "ina zaune a cikin gida, kawai sai na ji ƙarar bindiga, sai aka ce ɓarayi ne, sun tattara mana yara sun tafi da su.".
Ta nemi hukumomi su kai musu ɗauki ganin yadda mazajensu suke kwana a tsaye inda suke kai kawo domin tabbatar musu da tsaro.
A cewarta, yankin Kuriga na fama da matsalar rashin jami'an tsaro, abin da ke jefa rayuwarsu cikin barazanar hare-haren ƴan bindiga.
ECOWAS za ta nemi masu su shiga tsakani kan lamarin Mali da Nijar da kuma Burkina
Kungiyar Raya Tattalin ƙasashen Afrika ECOWAS ta ce za ta nemi masu shiga tsakanin domin shawo kan lamarin ƙasashe uku masu muhimmanci a ƙungiyar da suka haɗa da Mali da Burkina Faso da Nijar, waɗanda suka nuna muradinsu na barin ƙungiyar.
Kwamishinan kula da lamuran siyasa na ƙungiyar da tsaro da zaman lafiya, ambasada Abdel-Fatau Musah ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka yi a hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja.
Ya nuna cewa an cire duka takunkuman da aka sanya wa ƙasahsen uku, yanzu kuma ana aiwatar da wasu dabaru da za su nuna musu muhimmancin da suke da shi a ECOWAS.
"Ana ta tattaunawa tun da daɗewa, ba kuma kawai ECOWAS ba ce har da wasu masu shiga tsakani, kuma ana yin hakan ne don mu duka mu san muna buƙatar juna.
"Muna dai jiran waɗannan ƙasashen ne da nake yawan maimaitawa suna da matuƙar muhimmanci a matsayinsu na mambobin ECOWAS. Kuma idan babu su akwai wasu ƙalubale da idan ba su ba za mu iya ganin bayansu ba a yankin.
"Kamar matsalar ta'addanci da ake fama da ita n faruwa ne a yankin, kuma mu babban burinmu shi ne yadda za a kawo ƙarshen matsalar, da kuma yadda za a riƙa shige da fice tsakanin ƙasashenmu ba tare da damuwa ba," in ji Musah.
Ya yake bayani game da matakin ƙasashn uku na kafa tawagar tsaro da za ta yaƙi masu ikirarin jihadi, sai ya ce abu ne mai kyau kuma ko ECOWAS za ta so ta taimaka kan hakan.
An ji ƙarar fashe-fashe a kusa da cibiyar lantarki ta Zaporizhzhia
Kwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke sanya ido kan nukiliya, sun ce sun ji ƙarar fashe-fashe a kusa da cibiyar wutar latarki ta Zaporizhzhia da ke Ukrain.
Kwararrun da aka girke a wurin sun ce, fashewar ta wani gagarumin makami ce da aka yi amfani da shi a yankin.
Cibiyar wutar ita ce mafi girma a nahiyar Turai. Kuma ta kasance ƙarƙashin ikon Rasha na tsawon shekaru biyu.
Ministan makamashin Ukraine wanda yake halartar taro a Vienna ya ce lamura a yankin Zaporizhzhia kullum ƙara taɓarɓarewa suke.
An haramta sayar da nama a birnin Kampala na Uganda
Hukumomi a Uganda sun haramta sayar da nama a Kamfala babban birnin ƙasar, a wani mataki na hana yaɗuwar wata cuta da ke kama kofato da kuma bakin dabbobi.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito ma'aikatar noma da kiwo ta ƙasar na cewa "An haramta shiga da fitar da dabbobi cikin birnin, da ma wucewa da su, har sai yadda hali ya yi.''
Ma'aikatar ta ce "An rufe duk wata kasuwar dabbobi da mayanka da kuma sauran wuraren sayar da dabbobin da nama na cikin birnin."
Hukumomin sun ce za su yi aiki tare da jami'an da suka dace wajen tabbatar da bin dokar, duk da cewa akwai rahotonannin da ke cewa wasu shagunan siyar da nama suna aiki a birnin.
Cutar da aka gano mai kama kofato da bakin dabbobi na yin barazana ga lafiyar jama'a.
Rasha ta yi barazanar korar jami'an diflomasiyyar Amurka
Gwamnatin Rasha ta yi wa ambasadan Amurka kiranye zuwa Moscow babban birninta, tare da yin barazanar koarar jami'an diflomasiyyar Amurka domin nuna ƙin amincewa da katsalandan ɗin da Washington ke neman yi mata cikin harkokinta na gida.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rashan ta fitar ta zargi Amurka da bai wa ƙungiyoyin da ke adawa da gwamnatin Rasha kuɗi domin su yaɗa labaran ƙarya kan zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan gobe.
Wakiliyar Amurkan a Rasha Lynne Tracy har yanzu ba ta ce komai ba kan batun.
Tana cikin jami'an diflomasiyya masu yawa da suka halarci jana'izar shugaban 'yan adawa Alexei Navalny wanda ya mutu a gidan yari.
Tinubu ba shi da cikakken tsarin kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga – Amnesty
Ƙungiyar Amnesty International ta ce sace fiye da ƴan gudun hijira a jihar Borno da ɗalibai ɗari biyu da tamanin da bakwai da malamai a yankin Kuriga a jihar Kaduna na nuna gazawar hukumomin Najeriya na kare al'umma daga hare-haren ƴan bindiga da suka kashe dubban ƴan ƙasar cikin shekara biyar da ta gabata.
Ƙungiyar, cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a ta hannun shugabanta a Najeriya, Isa Sanusi, ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da mutanen da aka sace domin haɗa su da iyalansu.
A cewar ƙungiyar, dole ne hukumomi su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yawaitar sace-sacen da ake yi a sassa da dama na Najeriya tare da gabatar da sakamakon binciken ga al'umma sannan su tabbatar an hukunta waɗanda aka samu da hannu a garkuwa da mutane.
Amnesty ta ce, "sace-sacen mutane da dama a baya-bayan nan ƙarara sun nuna cewa shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa ba su da tsayayyen tsari na kawo ƙarshen miyagun laifukan ƴan bindiga da ke cin karensu babu babbaka a sassan jihohin Najeriya. Duk matakan tsaron da shugaba Tinubu da gwamnatinsa ke aiwatarwa ba sa tasiri," in ji Isa Sanusi.
"Ganin yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa a Najeriya a yanzu, a bayyane take cewa batun kare rayuwa da dukiyoyin al'umma ya na ƙasa cikin jerin abubuwan da gwamnati ta sa a gaba. Bai kamata a ƙyale mutane su zauna cikin fargaba da tsoron hari da garkuwa ba.
Yawan gazawar hukumomin Najeriya wajen kare mutane abu ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba kuma dole ne a kawo ƙarshen sa," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Amnesty ta kuma yi kira da a tabbatar da waɗanda ke da nauyin samar da tsaro a yankunan da aka yi sace-sacen jama'a su yi bayani kan gazawar da ta jefa rayuwar ɗaruruwan mutane cikin haɗari.
A ranar Alhamis ne wasu ƴan bindiga suka kai hari kan wata makarantar Firamare a Kuriga da ke jihar Kaduna inda suka sace ɗalibai kimanin 287 da malaminsu guda ɗaya, sai dai malamin ya samu kuɓuta sai kuma ɗalibi guda da ya mutu.
- Sace-sacen ɗalibai a makarantu 10 da suka girgiza Najeriya
- Ɗalibai 287 ne ƴan bindiga suka sace a Kuriga - Malamin makaranta
IS ta ɗauki nauyin harin da aka kai kan coci a Burkina Faso
Ƙungiyar IS ta ɗauki nauyin kai harin ranar 25 ga watan Fabarairu a kan wani coci a Burkina Faso wanda ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 15.
IS ta yi iƙirarin a ranar 7 ga watan Maris cikin jaridarta ta al-Naba wadda ke bayyana ayyukan ƙungiyar na baya-bayan nan a yankin Sahel.
Ta ce mayaƙan IS ɗauke da bindiga sun kai hari kan wata majami'a a ƙauyen Essakane a Lardin Oudalan kusa da iyakar ƙasar da Mali, suna tsaka da taron addu'oi ranar Lahadi.
Ƙungiyar ta ce "lokacin da ƴan ƙungiyar suka shiga cocin, sun buɗe wuta kan mabiya addinin kirista inda suka kashe fiye da 15 a cikinsu."
Ƙungiyar IS dai tana yawan kai hari kan mabiya addinin kirista da kuma wurarensu na ibada a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da Mozambique, inda take da rassa. Irin waɗan nan hare-hare da IS ke kaiwa a Burkina Faso abu ne da ba a saba gani ba. Hare-haren IS a can suna shafar sojoji ne.
A ranar da aka kai harin kan cocin, wasu da ba a san ko suwa ne ba sun kai hari kan wani masallaci a gabashin Burkina Faso a garin Natiaboani, lamarin da ya hallaka gomman mutane.
Har yanzu dai babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki nauyin harin, sai dai ƙungiyar al-Qaeda da ke takun saƙa da IS ta ɗauki nauyin kai hari kan sojoji a garin kuma a ranar.
Gwamnatin Kebbi za ta raba motocin abinci 200 don rage raɗaɗi
Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, ya ce gwamnatinsa za ta raba manyan motoci 200 ɗauke da abinci dangin hatsi don rage wa al'ummar jihar raɗaɗin tsadar rayuwa da suke ciki.
Cikin wata sanarwa gwamnatin jihar ta fitar a shafinta na X, ta ce ta sayi hatsin ne da nufin tallafa wa rayuwar al'ummar jihar.
''Gwamnatinmu ta sayi na'urorin sola don samar da wutar lantarki, da kuma injunan samar da ruwan sha masu amfani da man gas na CNG don inganta noma da samar da abinci'', in ji sanarwar.
A wani labarin na daban kuma gwamnan ya sanar da bai wa kungiyar 'yan sintiri ta Vigilanti tallafin naira miliyan 50 don inganta ayyukanta na samar da tsaro a jihar.
Gwamnan ya kuma alkawarta sayen motoci da sauran kayan aiki ga kungiyar.
Gwamnan ya ce ingantuwar tsaro a yankunan Zuru da Yauri ya sa manoman yankunan sun koma gonakinsu, lamarin da gwamnan ya ce ya taimaka wajen ƙaruwar samar da abinci a yankunan.
Me ya sa tallafa wa mata ke da muhimmanci?
'Babu wanda ya rasu a hatsarin jirgin sojin Najeriya'
Matuƙan jirgin saman sojin Najeriya biyu sun tsira da rai, bayan jirgin ya yi hatsari.
Hatsarin ya faru ne a kusa da barikin sojin saman da ke Arewacin jihar Kaduna.
Rundunar sojin saman Najeriyan ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin ke dawowa daga tuƙin koyo.
Kakakin rundunar Edward Gabkwet, ya ce “An yi sa'a duk matuƙan jirgin sun tsira da rai,”
Rundunar sojin saman ta ce an ƙaddamar da bincike kan abin da ya haddasa hatsarin.
Jami'an tsaro na neman ɗaliban Kuriga da 'yan bindiga suka sace
Jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da neman fiye da dalibai 280 na makarantar furamare da ƙaramar makarantar Kuriga da 'yan bindiga suka sace ranar Alhamis a jihar Kaduna.
Lamarin ya shafin duka duka al'ummar garin.
A yau da rana ne wani ɗalibi da 'yan bindigar suka harba a lkacin harin ya rasu bayan kwantar da shi a asibiti sakamakon raunukan da ya ji.
Hukumomin ƙasar sun sha alwashin kuɓutar da duka ɗaliban bayan da aka jibge tarin jami'an tsaro a yankin.
Tuni dai shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi Allah wadai da sace ɗaliban, tare da umartar jami'an tsaro su gaggauta kubutar da su
Sojojin Najeriya sun tarwatsa cibiyar ESN
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun tarwatsa wuraren da ake zargin shalkwatar dakarun rundunar tsaro ta gabashin Najeriya, wadda ke aiki a matsayin rundunar ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra ta IPOB.
Shalkwatar rundunar sojin Najeriya ta wallafa hotunan cibiyar da ta tarwatsa, inda ta nuna irin abubuwan da ta samu a wuraren.
Shalkwatar Sojin Najeriyar ta ce ta kai samame ne a cibiyar rundunar ESN a tsibiran da suke kananan hukumomin Orsu da Ihiala na jihar Imo da kuma Anambra.
Ta kuma ce bayanan sirri da ta tattara sun nuna cewa daga cibiyoyin ne kungiyar ke kitsa duk wani mummunan aiki da take gudanarwa a ƙarƙashin ESN.
Tinubu ya buƙaci a gaggauta ceto ɗaliban Kaduna da 'yan gudun hijirar Borno
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi Allah wadai da satar ɗalibai a jihar Kaduna da ƴan gudun hijra a Borno tare da bayar da umarnin a gaggauta ceto su.
Mai taimaka wa shugaban ƙasar na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a wata sanarwa ya ce shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta ceto ɗaliban da ƴan gudun hijirar da kuma hukunta masu hannu a lamarin.
Sanarwar ta ayyano shugaban Najeriyan ya na cewa "Shugabannin hukumomin tsaro sun yi mani bayani a kan abin da ya faru a Borno da Kaduna kuma ina da yaƙinin cewa za a ceto su.''
Shugaba Tinubu ya ce ba zai lamunci duk wani uzuri ba har sai an ceto yaran da aka yi garkuwa da su.
Ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa, tare da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin dawo da ƴanuwan su.
- Sace-sacen ɗalibai a makarantu 10 da suka girgiza Najeriya
- Ɗalibai 287 ne ƴan bindiga suka sace a Kuriga - Malamin makaranta
MDD ta yi kiran tsagaita wuta a Sudan saboda azumin Ramadan
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi kiran a gaggauta tsagaita wuta a Sudan.
Bayan shafe aƙalla shekara ɗaya ana gwabza yaƙi tsakanin rundunar sojin Sudan da mayaƙan RSF, Mista Guterres ya buƙacin ɓangarorin biyu su tsagaita wuta albarkacin watan Ramadan.
Kiran nasa na zuwa ne yayin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke tattaunawa kan tsagaita wutar domin samu damar shigar da kayan agaji kai tsaye yankin.
Akwai yiyuwar za a kaɗa ƙuri'a kan batun a yau Juma'a.
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar ya yi gargadin cewa ci gaba da yaƙin zai jefa Sudan cikin mummunan yanayin buƙatar ayyukan jin ƙai wanda zai shafi abubuwa da dama a ƙasar.
Aƙalla mutum 14, 000 aka kashe tun da aka fara yaƙin.
Dalibin Kuriga da mahara suka harbe lokacin sace ɗaliban makarantar ya rasu
Dalibin makarantar Kuriga da 'yan bindiga suka harbe lokacin sace ɗaliban makarantar da ke jihar Kaduna ya rasu.
An kwantar da ɗalibin mai shekara 14 a asibiti ranar Alhamis bayan 'yan bindiga sun harbe shi.
Maharan ɗake da makamai a kan babura sun yi wa makarantar ƙawanya tare da sace ɗalibai 287, waɗanda shekarun suka kama daga takwas zuwa 15.
Wani malami a makarantar ya ce ɗalibai 25 sun kuɓuta daga hannun maharan alokacin da suke kora su zuwa daji, to sai dai har yanzu sauran daliban na hannunsu.
Mazauna garin Kuriga sun ce lamarin ya shafi kusan duka al'ummar garin.
Wani mutum mai suna Hassan Abdullahi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 17 daga cikin ɗaliban da aka sacen 'ya'yansa ne.
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a dajin domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.
- Matsalar ƴan bindiga ta dawo sabuwa a wasu yankunan jihar Katsina
- Ɗalibai 287 ne ƴan bindiga suka sace a Kuriga - Malamin makaranta