Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Elon Musk ya tashi daga attajirin da ya fi 'kowa kuɗi a duniya'

    A karon farko a cikin watanni tara, Elon Musk ya tashi daga kasancewa mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya.

    Jeff Bezos ya maye gurbin Musk, bayan hannayen jarinsa na kamfanin Tesla ya fadi da kashi 7 da digo biyu cikin ɗari a ranar litinin.

    Maunin hamshaƙan masu kudi na Bloomberg ya nuna cewa a yanzu Musk yana da arzikin da yawansa ya kai dalar Amurka 197.7 billiyan, yayin da shi kuma Beros ke da dala 200.3 billiyan.

    Haka kuma wannan ne karon farko da hamshaƙin mai kuɗin, mai shekara 60 a duniya, mai kamfanin Amazon ya ɗare wannan matsayi na hamshaƙan masu kuɗin duniya na Bloomberg tun shekarar 2021.

    Giɓin duniya da ke tsakanin Musk, mai shekara 52 a duniya da kuma Bezos, wanda a baya ya kai dala $142 biliyan, yana raguwa yayin da hannayen jarin Tesla da Amazon ke yin hannun babbar riga.

    Duk da cewa duka kamfanonin biyu na daga cikin waɗanda suka fi bunƙasa kasuwar shunku ta Amurka, sai dai hannayen jarin Amazon ya ruɓanya tun shekarar 2022 ya zamo mafi ƙarfi.

    Yayin da na Tesla kuwa ke faɗuwa da kusan kashi 50 cikin ɗari tun bayan ganiyarsa a shekarar 2021.

    • Elon Musk na fuskantar shari'a kan sakon da ya janyo wa masu hannun jarin Tesla asarar biliyoyin dala
    • Elon Musk ya kafa tarihi bayan arzikinsa ya ragu
  2. Binance zai daina hada-hada da Naira

    Babban shafin hada-hadar kuɗin kirifto mai suna Binance ya ce zai daina musayar Naira na Najeriya daga ranar takwas ga wannan watan na Maris.

    A cikin wata sanarwa da kamfanin na Binance ya wallafa a shafinsa na intanet, ya ce duk waɗanda kuɗinsu na Naira ya rage a cikin asusunsu, zai a mayar da shi kuɗin kirfito na stablecoin idan wa'adin ya cika.

    Matakin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da gwamnatin Najeriya ta tsare wasu manyan jami'an kamfanin Binance a birnin Abuja.

    Hukumomi na zargin shafin na Binance ne da laifin "ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen waje a ƙasar".

    Darajar takardar kuɗin Najeriya - Naira dai ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba a tarihi tun bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ƙyale kasuwa ta tantance darajarta.

    Lamarin ya ƙara jefa tattalin arziƙin Najeriya da kuma al'umma ƙasar cikin garari, abun da ake ganin ya samo asali daga cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

    • 'Muna tsare da shugabannin Binance a Najeriya'
    • Mene ne shafin hada-hadar kudi na Binance?
  3. Katsewar lantarki ya jinkirta zaman majalisar dattawan Najeriya

    Wutar lantarki da aka ɗauke a zauren majalisar dokoki ta kawo jinkirin fara zaman ƴan majalisar dattijai a yau Talata.

    Sanatocin sun tsaya na wani lokici yayin da suke jiran kamfanin rarraba lantarki na Abuja AEDC ya dawo da wutar.

    Zauren Majlisar ya kasance cikin duhu yayin da wasu tsiraru daga cikin ƴan majalisar suke zaune suna jiran a dawo da wutar.

    Sai dai daga baya shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya buɗe zaman bayan dawowar lantarkin.

    Dama dai kamfanin lantarki na AEDC ya koka kan cewa akwai ma'aikatu da hukumomin gwamnati da dama waɗanda yake bi bashi, har ma ya yi barazanar yanke musu lantarki matuƙar ba su biya bashin da ake bin su ba.

    Najeriya dai na fama da ƙarancin wutar lantarki, inda ƙasar ta gaza samar da isasshen wutar lantarki da zai wadaci al'umma da masana'antu.

  4. Shugaban Ghana ya jinkirta sanya hannu kan dokar tsaurara hukunci kan masu auren jinsi

    Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ce ba zai sanya hannu kan dokar hukunta masu neman jinsi ɗaya ba har sai kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci kan batun.

    Gabanin haka, ministan kuɗi na ƙasar ya yi gargaɗin cewa ƙasar za ta iya yin hasarar biliyoyin kuɗi na dala daga Bankin Duniya.

    Dokar, wadda majalisar dokokin Ghana ta amince da ita a makon da ya gabata, ta tanadi hukuncin ɗauri da zai iya kai na shekara uku da duk wanda ya bayyana kansa a matsayin mai neman jinsi ɗaya, da kuma ɗaurin da zai iya kaiwa na shekara biyar ga duk wanda ke ƙarfafa gwiwar neman jinsi ɗaya.

    Ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama sun je kotu domin ƙalubalantar batun gabanin ƴan majalisar su amince da ƙudurin.

    Dama dai luwaɗi da maɗigo haramun ne a dokar ƙasar ta Ghana, inda doka ta tanadi hukuncin ɗauri na shekara uku ga wanda aka kama da laifi.

    Sabuwar dokar ta tsaurara hukunci kan masu neman jinsi - mai taken dokar kare rayuwar iyali da ɗabi'un tarayyar ma'aurata - ta samu amincewar dukkanin manyan jam'iyyun siyasa na Ghana, sai dai ba a iya fara amfani da ita har sai shugaban ƙasar ya sanya mata hannu.

    Dama dai ƙasashen Birtaniya da Amurka sun yi kakkausar suka kan dokar, kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun bayyana ta a matsayin koma-baya.

    A baya, shugaban ƙasar Nana Akufo-Addo ya ce zai sanya hannu kan dokar matuƙar mafi yawan al'ummar Ghana suka buƙace shi da yin hakan.

    To amma yanzu da alama yana son nuna wa ƙasashen waje cewar yana son kare hakkin bil'adama.

  5. Jiragen sama biyu sun yi karo a Kenya

    Hukumar da ke sanya ido kan sufurin jiragen sama a ƙasar Kenya ta tabbatar da cewa jirgin Fasinja na Safarilink ya yi karo da wani jirgin da ke atisaye a sama.

    An fara bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin.

    "An fara bincike mai zurfi ta bangarorin hukumomi da dama, wanda ma'aikatar binciken hatsarin jiragen sama za ta jagoranta da kuma hukumar ƴansanda ta ƙasa don gano musabbabin hatsarin," a cewar hukumar sa ido a kan sufurin jiragen sama na ƙasar.

    Mutane biyu da ke cikin jirgin da ke atisayen duk sun mutu, amma an samu ceto fasinjoji 39 da ma'aikatan jirgin Safarilink biyar.

    Kamfanin jiragen Safarilink ya bayyana a shafinsa na X cewa, jim kaɗan bayan tashin jirgin ne da misalin ƙarfe 3. 45 agogon ƙasar, aka yi wata ƙara mai ƙarfi.

    • Yadda faɗa tsakanin mata da miji ya tursasa wa jirgin sama saukar gaggawa
    • Fasinjan da bai iya tuki ba ya saukar da jirgi bayan da matukinsa ya suma a Amurka
  6. An sanya wa'adin rufe rajistar aikin Hajji a Kamaru

    Hukumomi a jamhuriyyar Kamaru sun sanya ranar 15 ga watan Maris, 2024, a matsayin ranar da za a rufe rajistar maniyyata aikin hajjin bana.

    A cikin sanarwar da ministan cikin gida kuma shugaban hukumar aikin hajji na Kamaru, Paul Atanga Nji ya fitar, ya ce Saudi Arabia ta ware wa ƙasar kujeru 10,000.

    Kuma idan aka cike dukannin kujerun, za a rufe rajistar gabannin cikar wa'adin.

    Sai dai gabannin a bayyana sabon farashin zuwa hajjin, wanda ya ƙaru a bana da CFA 33,100, shugabannin tawagogin maniyyatan sun fara kira da su yi rajista domin kaucewa cunkoson karshen lokaci.

    A bana hukumomin Saudiyya sun sauya tsarin bayar da takardun bizar aikin hajjin, inda suka ce zasu rufe da wuri.

    • Hotunan yadda aka yi hawan Arfa na hajjin bana - 2023
    • 'Tsadar rayuwa ta sa kuɗina ba za su kai ni Hajji ba a yanzu'
  7. Ɗaliban Yamai sun koka kan rashin biyan alawus

    Ƙungiyar ɗaliban jami'ar birnin Yamai a jamhuriyar Nijar ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda hukumomin mulkin sojan ƙasar suka bar ɗaliban jami'ar cikin mawuyacin halin rayuwa da na karatu.

    Ɗaliban sun kasance a sahun gaba wajen goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar.

    A cewar ɗaliban yanzu haka an kwashe watanni 10 ba tare da ba su kudin alawus-alawus na karatu ba.

    Kazalika ɗaliban jami'ar ta Yamai wadanda yawansu ya kai mutun dubu 40, sun koka kan matsalar karancin ɗakunan ɗaukar karatu da na kwana.

    Wannan shi ne karo na farko tun bayan juyin mulki da daliban ke fitowa su bayyana wa mahukuntan mulkin soja rashin jin dadinsu kan halin da aka bar su a ciki.

    • Manyan matsalolin tsaro uku da suka addabi Nijar bayan juyin mulki
    • Ana korafi kan rufe rajistar Ƴan Nijar mazauna ƙasashen waje da ke zaune a Najeriya
  8. Amurka ta ƙaƙaba wa shugaban Zimbabwe sabbin takunkumai

    Amurka ta sanya sabbin takunkumai a kan sugaban ƙasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa kan cin hanci da take haƙƙin ɗan'adam.

    Sabbin takunkuman sun kuma haɗa da wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar - waɗanda ta hana taɓa kadarorinsu da ke Amurkar tare da hana zu kai ziyarar ƙashin kansu ƙasar.

    Sabbin takunkuman sun maye gurbin waɗanda aka sanya wa ƙasar ta Zimbabwe kimanin shekara 20 da suka wuce.

    "Muna ci gaba da ganin yadda ake keta haddin ƴansiyasa da wasu haddin da suka shafi tattalin arziki da na bil'adama." A cewar wata sanarwa ta fadar White House.

    "Ana harin ƙungiyoyin fararen hula tare da hana ƴansiyasa sakat, ta hanyar take muhimman haƙƙoƙinsu na walwala, yayin da manyan jami'an gwamnati ke ci-gaba da sace kuɗaɗe daga lalitar gwamnati don amfanin kansu," a cewar sanarwar.

    "Munanan ayyukansu na taimakawa tare da tallafawa manyan gungun masu aikata manyan laifukan cin hanci na duniya, fasakwauri, halalta kuɗin haram da ke ƙara jefa al'umomin Zimbabwe da kudancin Afrika da wasu sassan duniya. "

    • Yadda ake cinikin takardun kuɗi don kauce wa tsadar rayuwa a Zimbabwe
    • Rashin abinci ya sa ƴan Zimbabwe tunanin ko dawa da gero na iya maye gurbin masara
  9. Fasa rumbunan ajiye abinci babban laifi ne - Minista

    Ƙaramar ministar Abuja ta bayyana ayyukan fasa rumbun ajiye abinci da wasu mutane suka yi a birnin da cewa babban laifi ne.

    Dr. Mariya Mahmoud ta bayyana hakan ne bayan kai ziyarar gani da ido don shaida irin ɓarnar da aka yi a wajen ajiye abincin da aka tatuke.

    A shafinta na X ta wallafa cewa: "Na je rumbun ajiye abinci a Gwagwa-Tasha don tantance irin ɓarnar da zauna-gari-banza suka yi a ranar Lahadi. Wannan abin ya wuce yunwa, babban laifi ne!!!

    Abin da na gani abu ne mara daɗi, yanayi ne da wasu zauna -gari-banza suka wawushe duka hatsain da sauran kayan abinci da ke wurin...

    Wani ɗankasuwan da BBC ta zanta da shi a unguwar karmo da ke birnin, ya bayyana cewa mutane sun wawashe masa kayan abinci a wurin ajiyar kayan da ke Karmo.

    Mutumin ya ce lamarin da ya faru a ranar Lahadi, ya janyo masa asarar sama da naira miliyan 100.

    Yayin da mutanen da ke maƙwaftaka da wurin suka bayyana yadda masu fasa rumbun suka zo da da makamai da suka haɗa da adduna da sanduna da wuƙaƙe wajen fasa rumbun.

    • Halin da ake ciki bayan wawar abinci a jihar Adamawa
    • Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya
  10. 'Karyewar naira ta durƙusar da kamfanoni 300 a Najeriya'

    Ƙungiyar masu kamfanonin samar da kayayyaki a Najeriya, MAN, ta ce kamfanoni kusan dari uku ne suka durƙushe tun bayan da aka fara samun karyewar darajar kuɗinƙasar, Naira.

    Karyewar darajar naira dai ta jefa tattalin arzikin Najeriya cikin wani hali, lamarin da masu masana'antun ke cewa suma basu tsira ba.

    Alhaji Sani Hussaini mamba a majalisar zartarwa a ƙugiyar kamfanoni a Najeriya, ya ce faɗuwar darajar naira ta kai ga tashin sama da kashi ɗari na abubuwan da suke sarrarafawa.

    Kuma ba za su iya ƙara farashin kayyakinsu ya kai wannan farashinba a kasuwa.

    Haka zalika kayan abinci su ne suka fi tafiya a kasuwa, lamarin da ya sa idan ba su kamfani ke sarrafawa ba, kasuwarsa na ci baya.

    Inda ya ce kashi 80 cikin ɗari na kayyakin da kamfanonin ke amfani da su shigo da su a keyi daga waje.

    Lamarin da ya ce ya jefa wasu ƙarin kamfanoni kimanin 150 cikin tangal-tangal.

    Daidaituwar farashin kuɗaɗen waje, musamman dalar Amurka, a cewarsa zai taimaka gaya wajen tafiyar da ayyukan kamfanoni da masana'antu a ƙasar.

    Tun bayan bullo da garambawul ta fuskokin da suka haɗa da janye tallafin man fetur da daidaita kasuwar musayar kuɗaɗen wajen a bara ne, ƙasar ta shiga wani hali.

    Yayin da al'ummarta ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa.

    • Mummunar faɗuwar darajar naira a tarihi
    • Me ya sa darajar naira ke daɗa karyewa?
  11. Gaza na fuskantar ƙarancin agaji da gangan - MDD

    Shugaban hukumar agajin gaggawa na Majlisar Ɗinkin Duniya a Gaza, ya yi korafin cewa suna fuskantar ƙarancin kayan agaji da gangan da nufin kawo karshen aikin hukumar a Gaza.

    Philippe Lazzarini ya shaida wa zauren MDD a birnin New York cewa ana yaɗa bayanan ƙarya kan hukumar ga masu ba da agajin da hukumar ke tafiyar da aikinta da shi.

    Mista Lazzarini ya ƙara da cewa dagula ayyukan hukumar zai haddasa durƙushewar ayyukan jin kai a Gaza.

    Ya ce yin hakan tamkar mun sadaukar da ɗaukacin al'ummar yaran da aka samar a tushen kiyayya da tashin hankali nan gaba.

    Isra'ila ta gagara yin cikakken bayani kan zargin da ta yi wa hukumar a watan Junairu, na hannun jami'anta 11 a harin da Hamas ta kaddamar ga Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktobar bara.

  12. Trump ya yi nasara a kotun ƙoli kan hana cire shi a cikin ƴan takara

    Kotun ƙolin Amurka ta garƙame ƙofar duk wani yunƙuri na Colorado na cire sunan Donald Trump a cikin takardun kada ƙuri'a na zaɓen fidda gwani na ƴantakarar shugaban ƙasa.

    Haka kuma hukunci ya sahfi sauran jihohin da ke da aniyar ɗaukar irin wannan mataki, ko duk wani yunƙuri da haramta masa takara.

    Hukuncin kotun ya ce majalisar dokokin ƙasar ce kalai ke da alhakin cire sunan tsohon shugaban a kan takardar kada ƙuri'a kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar da aka yi wa garambawul na 14 ya tanada.

    Mista Trump ya yi maraba da hukuncin da kotun ta yanke a ranar Litinin, yana mai cewa:"wannan kyakkyawar rana ce ga Amurka."

    Hakan babbar nasara ce ga Donald Trump, amma hukuncin ya zo ne a makon da ya ke da shari'o'in zargin aikata laifuka.

    Kotun kolin ta yi watsi ne da hukuncin da babbar kotun Colarado ta yanke na hana Trump tsayawa takara saboda goyon bayan harin da magoya bayansa suka kai majalisar dokokin Amurka a shekarar 2021.

    • Yadda zargin aikata lalata ke neman ɗaure Donald Trump
    • An zargi Trump da jirkita bayanai don ɓoye laifuka