Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Indiya ta buƙaci ƴan ƙasar da ke Isra'ila da su tashi zuwa wurare marasa haɗari

    Ofishin jakadancin Indiya a Isra’ila ya shawarci ƴan ƙasarta da ke zaune kusa da iyakokin Isra’ila da su tashi zuwa wurare marasa haɗari.

    Ƙasar ta kuma buƙaci dukkan mutanenta da ke zaune a Isra’ila, musamman ma waɗanda ke aiki a yankuna da ke kusa da iyakoki da ke arewaci da kuma yammaci ko masu kai ziyara yankunan, da su tashi zuwa wasu wurare.

    Ofishin ya kuma bayar da wani layin waya wanda ƴan ƙasar za su iya kira idan suna buƙatar taimako.

    Ya kuma buƙaci mutane da su yaɗa shawarwarin zuwa ga sauran ƴan Indiya da ke zaune a Isra’ila.

    Hakan na zuwa ne bayan da wani ɗan Indiya ya mutu da kuma jikkata wasu mutum biyu sakamakon harin da ƙungiyar Hezbollah ta kai wani kauye da ke arewaci.

  3. Yara 70 sun ɓata bayan harin masu iƙirarin jihadi a Mozambique

    Hukumomi a arewacin Mozambique sun ce aƙalla yara 70 ne suka ɓata bayan hare-haren da masu iƙirarin jihadi suka kai.

    Ana fargabar cewa mayakan ISIS sun yi garkuwa da wasu daga cikin waɗannan yaran.

    Irin waɗannan hare-hare sun dawo ne a watan Disamba bayan samun zaman lafiya na watanni.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an ɗaiɗaita kusan mutum 100,000 tun soma kai waɗannan hare-hare.

    Ƙungiyoyin agaji sun ce rabin mutanen sun kasance yara, kuma iyalan da aka ɗaiɗaita na cikin tsananin buƙatar taimakon abinci, matsuguni da kuma kulawa ta lafiya.

    Ƙasashe da dama sun aika dakaru zuwa ƙasar ta Mozambique domin taimaka mata wajen yaƙi da ayyukan masu iƙirarin jihadi wanda ya fara tun shekara ta 2017.

  4. Yadda tsadar rayuwa ta jefa mutanen Kamaru cikin wani hali

  5. Dubai ba ta ɗage haramcin bai wa 'yan Najeriya biza ba

    Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ba ta ɗage haramcin bai wa ƴan ƙasar biza ba.

    Wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X da yammacin Talatar nan, ta ce UAE ba ta koma bai wa ƴan Najeriya biza ba.

    Tun da farko dai wasu rahoatanni sun ruwaito cewa Dubai ɗin ta ɗage haramcin biza kan Najeriya, sai dai Onanuga ya yi watsi da iƙirarin.

    "Bayanai da ke yawo cewa Dubai ta koma bai wa ƴan Najeriya biza ba gaskiya bane. Bayanin ba daga gwamnatin Najeriya ko UAE ya fito ba," in ji Onanuga.

    A watan Oktoban 2023 ne Haɗadɗiyar Daular Larabawa ta haramta wa ƴan Najeriya da wasu ƴan ƙasashe 19 daga nahiyar Afrika shiga ƙasarta.

    • Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da ƴan Najeriya daga shiga ƙasarta
    • Yadda za ku samu bizar shekara goma ta zama a Dubai
  6. Al Nassr ta yi rashin nasara a gasar zakarun Asia

  7. Kotu ta haramta bincike kan Ganduje game da bidiyon dala

    Wata babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar ba ta da ikon ta gayyaci ko ma ta gudanar da bincike kan tsohon gwamnan Kano kuma shugaban Jam'iyyar APC ta ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje game da bidiyon dala.

    Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman ne ya yanke hukuncin ranar Talata a ƙarar da Ganduje ya shigar kan hukumar ta PCACC, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Ganduje ya shigar da ƙarar a watan Yulin 2023 inda ya nemi a kare masa ƴancinsa bayan da shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya gayyace shi da ya bayyana domin amsa tambayoyi kan bidiyon dala.

    Kotun ta ba da umarnin hana gayyata ko kuma bincikar Ganduje har sai abin da kotu ta tsayar a ƙarshe.

    A 2018 ne jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a lokacin da Ganduje yake gwamna, bidiyon ya nuna shi yana karɓar damun daloli daga hannun wani ɗan kwangila.

    Sai dai Ganduje ya musanta zargin inda ya ce haɗa bidiyon aka yi.

    Lauyan hukumar ta karɓar ƙorafe-ƙorafe, Usman Fari ya ce ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin kotun ta yanke hukunci a ƙarar da aka shigar tun Yulin bara inda ya ce tuni ya samu izinin wanda yake ƙarewa domin ɗaukaka ƙara.

    Lauyan Ganduje, Mathew Burkaa mai mukamin SAN ya ce hukuncin kotun ya tabbatar da matsayinsa cewa hukumar ba za ta iya yin bincike kan wanda yake karewa ba kan wata doka da ke ta tarayya.

    • Manyan ƙalubale huɗu da ke gaban Ganduje
    • Mun shawarci Ganduje kada ya amsa gayyata kan ‘bidiyon dala’ - APC
    • Abu huɗu da Muhuyi zai binciki gwamnatin Ganduje a kai
  8. Radhika Merchant: Matar da za ta auri ɗan mutum mafi arziƙi a Indiya

  9. Ukraine ta ce mutum bakwai sun mutu a wani hari kan jirgin ruwan Rasha

    Jami'an leken asirin Ukraine sun ce mutane 7 ne suka mutu sannan wasu 6 suka jikkata bayan da wani jirgin ruwan Rasha da ke sintiri ya nutse a wani harin da aka kai a cikin teku.

    An kai wa jirgin hari da sanyin safiyar Talata.

    Hukumar leken asirin sojin Ukraine ta ce an lalata ɓangaren hagu da dama na jirgin ruwan na Bahar Maliya.

    Har yanzu fadar Kremlin ba ta ce uffan ba, amma masu wallafa labarai a shafukan intanet na ƙasar ta Rasha sun tabbatar da nutsewar jirgin mai suna Sergei Kotov.

    BBC ba ta iya tantance irin ɓarnar da aka yi wa irgin ba.

    A cikin wani sako a shafin Telegram, Babban Hukumar Leken Asiri ta Ukraine ta ce an kwashe ma'aikatan jirgin 52.

    Jirgin mai suna Sergei Kotov na ɗaya daga cikin jiragen sintiri guda huɗu da aka kammala aikin sojan ruwan Rasha mai lamba 22160.

    A baya Ukraine ta kai masa hari a watan Satumban bara.

    • Wane zaɓi ya ragewa ɗaliban da ke karatu a Ukraine kafin yaƙi?
    • Amsar muhimman tambayoyi biyar kan shekara biyu na yaƙin Ukraine
    • Ƙauyen da ya zama na marayu zalla bayan mummunan harin Rasha a Ukraine
  10. EFCC ta kama manyan motoci 21 maƙare da kayan abinci

    Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin ƙasa ta'annati ta sanar da kama motocin dakon kaya 21 maƙare da kayan abinci da wasu kayayyaki da ke kan hanyar N'djamena a jamhuriyar Chadi da jamhuriyar tsakiyar Afirka da Kamaru.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, an kama manyan motocin ne yayin wani samame da aka ƙaddamar kan titunan Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama a jihar Borno.

    Binciken da aka gudanar ya nuna wasu kayan abinci da aka yi dabarar ɓoye su cikin motocin da za su iya wucewa ba tare da an gano ba.

    Ƙarin binciken da aka gudanar ya nuna takardar da aka nannaɗe kayan da ke cikin motar ta nuna kayan za a kai su N'djamena a ƙasar Chadi da jamhuriyar Afirka ta tsakiya da kuma Kamaru.

    Ana sa ran kamen motocin zai kawo ƙarshen matsalar abincin da ake fama da shi sakamakon yadda wasu ke fasaƙwabrinsa.

    Ana gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

  11. Wasannin Afirka: Dama ta musamman ga mai masaukin baƙi Ghana

  12. Majalisar Gambiya na duba yadda za a haramta kaciyar mata

    Wani ɗan majalisa ya gabatar da ƙudurin neman haramta yi wa mata kaciya gaban majalisar dokokin Gambiya.

    A 2015 ne aka haramta yi wa mata kaciya a ƙasar da galibin al'ummarta Musulmai ne lokacin Yahya Jammeh na shugaban ƙasa.

    Sai dai fitattun malaman addinin musulunci sun yi ta neman a soke haramcin yayin da ƙungiyoyin kare haƙƙin mata suka sha alwashin ci gaba da fafutuka domin ganin dokar ta tsaya a haka.

    Mulkin Mista Jammeh ya zo ƙarshe a 2016 bayan ya shafe shekara 22 kan karaga.

    An yi wa fiye da kashi uku bisa huɗu na matan Gambiya ƴan shekara tsakanin 15 da 49 kaciya, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Mabiya wani fitaccen malami Abdoulie Fatty, sun nuna goyon bayansu ga ƙudurin jim kaɗan bayan an gabatar da shi a zauren majalisar.

  13. Facebook da Instagram sun dawo aiki bayan tsayawa na sa'o'i

    Shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram sun dawo aiki bayan tsayawa na tsawon wasu sa'o'i a wasu sassan duniya.

    Tun da farko, mutane da dama dai sun kasa shiga shafukansu sakamakon matsalar da aka samu.

    An fara fuskantar matsalar tun da tsakar ranar yau Talata.

    Duk wani kokari da masu amfani da shafukan suka yi don hawa zaurukan guda biyu ya ci tura, inda aka buɗe wani maudu'i a shafin X mai taken "Facebook and Instagram down" ma'ana Facebook da Instagram sun tsaya aiki.

    Babu wani bayani daga Meta, mallakin shafukan kan abin da ya janyo tsayawar.

  14. Aurena na ƙarshe shi ne mafi muni - Ƙalubalen da Mr Ibu ya fuskanta kafin rasuwa

  15. Ba mu da niyyar yin katsalandan a dimokraɗiyyar Najeriya – Janar Lagbaja

    Babban hafsan sojin ƙasa a Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja ya jaddada ƙudurin rundunar soji na kare martabar dimokraɗiyyar ƙasar.

    Da yake yi wa mahalarta taron ƙarawa juna sani kan aiki da hedikwatar rundunar ya shirya a Abuja, Janar Lagbaja ya ce rundunar ba ta da burin yi wa dimokraɗiyyar ƙasar maƙarƙashiya.

    Ya yi kira ga sojojin ƙasar su ci gaba da ba da himma wajen gudanar da ayyukansu.

    Alƙawarin da Janar Lagbaja ya ɗauka na zuwa ne sakamakon yunƙurin da aka yi na kifar da gwamnati a yankin Afirka ta yamma da tsakiyar Afirka da suka fuskanci aƙalla juyin mulki bakwai cikin shekara huɗu da ta gabata.

    Mali da Guinea da Burkina Faso sai a baya-bayan nan Nijar - dukkansu mambobin ECOWAS sun fice daga ƙungiyar cikin shekaru huɗu da suka gabata.

    Chadi da Sudan da ba sa yankin Afirka ta Yamma suma sun fuskanci juyin mulki a 2021.

    • Me ya sa juyin mulki ke sake dawowa a Afirka?
    • Juyin Mulkin Nijar: Jarrabawa ga dimokraɗiyyar Afirka ta Yamma
  16. Yadda tsadar rayuwa ta jefa mutanen Kamaru cikin wani hali

    Al'umma a Kamaru na fama da matsin rayuwa sakamakon ƙara farashin man fetur karo na biyu a wannan shekarar.

    Lamarin ya ƙara jefa mutane cikin matsanancin hali inda mutane ke fama wajen samun abincin da za su kai baka saboda tsadar farashin kayan masarufi.

    A wannan bidiyon, BBC ta bibiyi Stella Anchu, wata mazauniyar babban birnin Yaounde don jin yadda take jurewa tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar.

    • Zaftarewar ƙasa a Kamaru: Na kuɓutar da ƴaƴana uku amma ban iya ceton na huɗun ba
    • Yadda maƙwabtan Najeriya suka shiga tasku bayan cire tallafin man fetur
  17. Arsenal ba za ta ɗaga ƙafa ba - Arteta

  18. 'Gwamnatin Enugu ta kashe kaji 30,000 a yayin rusau'

    An shiga halin fargaba a unguwar Nike da ke jihar Enugu a kudancin Najeriya, bayan gwamnati ta fara rusa gidajen mutane don gina wani sabon birni.

    Mai gonar UD da ke unguwar ta Nike, Ngozi DeDe cikin hawaye ta bayyana cewa an kashe mata dabbobin da take kiwo da suka haɗa da kifi da kaji da darajarsu ta kai naira miliyan 30.

    Mazauna unguwar da dama sun koka cewa gwamnati ba ta basu wata sanarwa ba kan rushe gidajen nasu, sai kawai a ranar Talata suka ga an fara rusau.

    Ngozi ta shaida wa BBC cewa " A ranar talata sai jami'an hukumon ma'aikatar Enugu suka fado mana, suka rusa gidan kaji na, kuma ba a bani wata sanarwar yin hakan ba kafin sannan."

    A cewarta a bara gwamnatin ta bayar da takarda, amma ita an gaya mata cewa bata cikin waɗanda abin zai shafa, sai gashi an zo an rushe mini gidan kaji."

    Ngozi Dede ta ce an kashe mata kaji 30,000 da kifi tarwaɗa 1,000 a gidan kaji uku da tare da lalata mata gidan ma'aikata biyu.

    Yayin rusau da gwamnatin ta yi ya shafi kimanin gidaje 50.

    Gwamnatin jihar ta Enugu ta sanya hannu a wata takarda na gina wani sabon birni a unguwar ta Nike.

    Sai dai ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, gwamnatin ta Enugu bata kai ga mayar da martani ko amsa sakonnin da BBC ta tura mata game da wannan batu.

    • Enugu: Yadda kudirin biyan gwamnoni da matansu fansho ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya
    • Yadda ango da ƴan uwansa biyar suka mutu 'bayan cin abincin biki'
  19. Sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan fashin daji a Katsina

    Dakarun sojin Najeriya sun hallaka gawurtaccen ɗanfashin dajin da ake kira, Maikusa, wanda shi ne mataimakin shugaban gungun ƴan'ta'adda da suka yi ƙaurin suna wajen addabar mutane a jihar katsina, Najeriya.

    Wanda ke shugabantar gungun ƴanfashin da maikusa ke ciki, an fi kiransa da Modi Modi.

    Dakarun sun ce sun harbe Maikusa da wasu ƴan'ta'adda uku a wata musayar wutar da aka yi a ranar Litinin, 4 ga watan Maris, 2024.

    Sojin sun ce an yi arangamar ce a yayin da suke ayyukansu na kawo ƙarshen tayar da ƙayar baya a ƙananan hukumomin Kurfi da Safana da ke jihar Katsinan.

    A cewar sojin sun kuma samu nasarar ƙwato bindigogi biyu ƙirar AK-47, da kwanson albarusai 65 da wata bindiga ƙirar hannu da kakin soji.

    Inda suka ƙara da cewa sun kuma lalata maɓoyar ƴanfashin a ƙauyukan Wurma, Shaiskawa, Yauni da Dogon Marke duka a ƙaramar hukumar Kurfi da kuma ƙauyukan Ummadau da Zakka a cikin Safana.

    Jihar ta Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da suka kwashe shekaru suna fama da matsalar ƴanfashin daji, da satar mutane, da hare-haren ta'addanci da ya kai ga asarar daruruwan rayuka da dumbin dukiyoyi.

    • Gudunmawar masu kuɗi a yaƙi da 'yan fashin daji a Katsina
    • Yadda ‘yan fashin daji suka mayar da wasu mazauna kauyukan jihar Katsina bayi
  20. Ghana ta fitar da jadawalin babban zaɓe

    Hukumar zabe ta ƙsar Ghana ta fitar da jadawalin zaben gama-gari na shekarar 2024.

    A cewar hukumar, za a fara karɓar sunayen ƴantakarar shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki daga ranar 9 zuwa 13 ga watan Satumbar 2024.

    Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin tsunduma kakar siyasa gadan- gadan a ƙasar.

    Bayan haka kuma za a sanya sunayen ƴan takarar a takarda kada kuri`ar zaben shugaban ƙasa a ranar 23 ga Satumba, 2024.

    Sannan na ƴan majalisa a ranar 24 ga Satumba, 2024.

    Inda ake sa ran bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2024 cikin kwanaki uku bayan an yi zaben, idan komai ya tafi yadda aka tsara.

    • Mata a zaben Ghana: Ga biki babu zanin daurawa
    • Zaɓen Ghana: Ƴan adawa sun yi zargin tafka maguɗi