Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Shugaban MDD ya nemi a yi bincike kan mummunan kisan farar hular Gaza

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya ya nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan mutum fiye da Falasɗinawa 100 lokacin raba kayan agaji a Gaza.

    Aƙalla mutum 117 aka kashe kuma fiye da mutum 760 suka jikkata ranar Alhamis yayin da mutane suka kewaye motocin da ke ɗauke da kayayyakin.

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi tur da lamarin inda ya ce farar hular na buƙatar agajin gaggawa.

    Hamas ta zargi Isra'ila da buɗe wuta kan farar hula sai dai Isra'ila ta ce galibi sun mutu a turmutsitsi bayan da ta yi harbin gargaɗi.

    A ranar Alhamis ne aka kasashen duniya suka soki Isra'ila inda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce sojojin Isra'ila na kai wa farar hula hari.

    Babban jami'i a kungiyar tarayyar Turai, Josep Borrel ya bayyana lamarin a matsayin kisan da ba za a amince da shi ba.

    Da yake mayar da martani, Mr Guterres a shafinsa na intanet ya yi "tur da abin da ya faru ranar Alhamis a Gaza inda fiye da mutum 100 aka ba da rahoton sun mutu ko jikkata yayin da suke neman agaji."

    • Ƙasashen duniya sun kaɗu da kisan Falasɗinawa fiye da 100
    • An kusa ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza - Biden
  2. Tarihin jagoran ƴan adawar Chadi da aka kashe - Yaya Dillo

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Marigayi Yaya Dillo

    Yaya Dillo, mai shekara 49 shi ne jagoran jam'iyyar hamayya ta PSF a Chadi.

    Dillo wanda ya tashi daga zama jagoran ƴan tawaye zuwa minista a majalisar ministoci a jam'iyya mai mulki, mutum ne mai yawan sukar ɗan uwansa wanda shi ne shugaban Chadi, Mhamat Derby.

    Daga baya ya koma ɓangaren hamayya inda ake sa ran ya fafata tare da Derby a zaɓen da za a yi a watan Mayu.

    Shekara biyu da ta gabata, sojoji sun kai samame gidan Dillo a N'Djamena, babban birnin ƙasar inda aka kashe biyar cikin ƴan uwansa har da mahaifiyarsa da ɗansa.

    Takun saƙar da ke tsakanin Dillo da gwamnatin Derby ya haifar da tashin hankali tsakanin ƙabilar Zaghawa wadda ƙabilarsu ce.

    A ranar Laraba ne hukumomi suka zargi jam'iyyar Dillo da kai hari kan hedikwatar tsaron ƙasar.

    Zargin da Dillo ya musanta, ya janyo buɗe wuta a babban ofishin jam'iyyar adawa inda a nan ne ake tunanin an kashe shi.

    Chadi na kasance a ƙarƙashin mulkin soji tun 2021 bayan da ƴan tawaye suka kashe tsohon shugaban ƙasar Idriss Derby inda kuma aka maye gurbinsa da ɗansa.

    Masu suka sun ce mutuwar Dillo na iya kawo cikas wajen miƙa mulki ga farar hula.

    Babu bayani kan yadda mutuwar madugun adawar za ta shafi babban zaɓen ƙasar na watan Mayu.

    • Idriss Deby: Abu biyar da suka kamata ku sani shekara guda bayan kashe shugaban Chadi
    • Yadda Afrika Ta Yamma take matsa ƙaimi a yaƙi da ta'addanci a yankin Sahel
  3. Shugaban RSF na Sudan ya je Libya don tattaunawa kan rikicin ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A jiya ne kwamandan dakarun Rapid Support Forces na Sudan (RSF), Mohamed Hamdan Dagalo, ya gana da firaministan Ƙasar Libya, Abdul Hamid Mohammed al-Dbeibah, a birnin Tripoli.

    A yayin ganawar, Dagalo ya tattauna batutuwan da ke haifar da rikici tare da gabatar da shawarwarin dakatar da yaƙin da ke faruwa tsakaninsu da sojojin Sudan domin samun zaman lafiya, da sake gina kasar Sudan.

    Ziyarar tasa ta biyo bayan wata ziyarar da takwaransa na Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya kai a baya-bayan nan domin tattaunawa da mahukuntan kasar Libya.

    • Rikicin Sudan: Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici
    • Yadda ƴan bindiga ke ƙona ƙauyuka ƙurmus a Darfur
  4. An katse wa majalisar dokokin Ghana lantarki saboda bashin kuɗin wuta

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Kamfanin wutar lantarki na Ghana (ECG) ya katse wutar lantarkin majalisar dokokin ƙasar a ranar Alhamis saboda gaza biyan bashin kuɗi cedi miliyan 23 da ake bin majalisar.

    Wanda yawan kuɗin ya kai dalar Amurka miliyan 1.8.

    Katsewar ya kawo cikas ga muhawarar da ake tafkawa a majalisar kan jawabin da shugaban kasar ya yi, inda ƴan majalisar suka rika rera taken "Dumsor, dumsor," wato matsalar wutar lantarki.

    Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa duk da cewa an kunna janaretan majalisar domin samar da lantarki a lokacin, sauran sassan ginin majalisar sun kasance babu wutar a yawancin ranar.

    Daraktan sadarwa na kamfanin wutar lantarki, William Boateng ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya dauki matakin katse wutar ne saboda ƙin amincewa da majalisar dokokin kasar ta yi na "girmama sanarwar bukatar biyan bashin".

    An dai mayar da wutar lantarkin ne bayan da majalisar ta biya cedi miliyan 13 tare da yin alkawarin sasanta sauran basukan nan da mako guda.

    Daraktan sadarwa na ECG ya bayyana cewa haka za su katse wutar lantarki duk wanda ake bi bashi da kuma ƙin biyan bashin.

    Kamfanin wutar lantarki na Ghana na fuskantar matsalar kudi, lamarin da ke janyo katsewar wutar lantarkin akai-akai daga abokan huldar da yake bi bashi a yayin da ake fama da ƙarancin wutar saboda kalubalen tattalin arziki.

    • Nijar ta shiga matsalar lantarki bayan katsewa daga Najeriya
    • Najeriya: Yadda rashin lantarki ke kassara harkokin kasuwanci a fadin ƙasar
  5. Najeriya ta buƙaci kamfanin Binance ya biya ta diyyar dala biliyan 10

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta buƙaci shafin musayar kuɗin intanet na Binance ya biya ta kuɗi dalar Amurka biliyan 10 a matsayin tara, bisa iƙirarin da gwamnatin ta yi na asarar da ta tafka sanadiyyar ayyukan shafin.

    Gwamnatin ta zargi shafin na Binance da zuzuta farashin musayar kuɗaden waje ta hanyar yin hasashe maras tushe da kuma shaci-faɗin darajar naira, lamarin da ya sa darajar naira ta zube da kimanin kashi 70 cikin 100.

    A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa tana tsare da wasu manyan jami'an shafin Binance biyu, waɗanda jami'an tsaro ke yi wa tambayoyi bisa zargin shafin da zama wata kafa ta halasta kuɗaɗen haram da kuma samar da kuɗi ga ƴan ta'adda.

    Wannan ya biyo bayan iƙirarin da Babban Bankin Najeriya ya yi a ranar Talata cewa kuɗi kimanin dala biliyan 26 ne aka yi safarar su ta shafin Binance daga Najeriya zuwa wasu wuraren da ba a sani ba.

    Bayo Onanuga, wanda shi ne mai magana da yawun shugaban Najeriya ya shaida wa BBC cewa: "Jami'an na Binance na bai wa gwamnati haɗin kai ta hanyar samar da bayanai".

    Har yanzu dai Binance bai ce komai ba game da batun tsare jami'an nasa biyu a Najeriya.

    Babban Bankin Najeriya na shan matsi wajen ganin ya daidaita darajar naira wadda farashinta ke ci gaba da tangal-tangal.

    Faɗuwar darajar naira ta ƙara damalmala halin tsadar rayuwa da al'ummar Najeriya ke ciki sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da na abinci da sufuri, wanda ya haifar da jerin zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar.

    • 'Muna tsare da shugabannin Binance a Najeriya'
    • Abin da ya sa kasuwar Crypto ke rugurguzowa a duniya
  6. Aƙalla mutum 43 sun mutu sanadin gobara a Bangladesh

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Jami'ai a Bangladesh sun ce mutum aƙalla 43 ne suka mutu sanadin tashin gobara a wani rukunin gidaje da ke Dhaka, babban birnin ƙasar.

    Rahotanni sun ce gobarar ta fara tashi ne a wani gidan abinci kuma ta bazu cikin sauri a benen mai hawa bakwai, abin da kuma ya sa mutane da dama suka maƙale a ciki.

    Da dama daga cikin waɗanda suka ji raunuka sun yi tsalle ne daga ginin domin kaucewa gobarar.

    An kuɓutar da mutum 75 sannan mutane da dama suna asibiti.

    Jami'ai sun yi nasarar kashe gobarar bayan sa'a biyu sannan ana gudanar da bincike kan abin da ya haifar da tashin wutar.

    Ministan lafiya na Bangladesh Samanta Lal Sen ya ce aƙalla mutum 33 har da mata da yara ne aka tabbatar da mutuwarsu a asibitin koyarwa na Dhaka.

    Wasu 10 kuma sun mutu a babban asibitin ƙuna da ke birnin. Wasu ashirin da biyu kuma na cikin yanayi mai tsanani, kamar yadda Mr Sen ya bayyana.

    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
    • Me yake jawo gobara a kasuwannin Najeriya kuma yaya za a magance ta?
  7. Ƙasar Chadi ta yi cikakken bayani kan mutuwar jagoran 'yan adawa Yaya Dillo

    ...

    Asalin hoton, ISSOUF SANOGO

    Ministan sadarwa na ƙasar Chadi Abderaman Koulamallah ya sanar da cewa jami'an tsaro sun kashe jagoran 'yan adawa Yaya Dillo ne a ranar 28 ga watan Fabrairu.

    A cewar gidan talabijin na Tele Chad, Dillo ne ya jagoranci harin da aka kai kan Hukumar Tsaro ta Kasa (ANSE) a N’Djamena, babban birnin kasar.

    Ministan ya bayyana cewa Dillo da magoya bayansa sun nufi ginin ANSE ne domin sakin wani ɗan adawar da ake tsare da shi bisa laifin kitsa kisan gillar da aka so yi wa shugaban kotun ƙoli.

    Koulamallah ya bayyana cewa a lokacin da jami'an tsaro suka yi yunkurin kama su Dillo da ƙungiyarsa sun mayar da martani da manyan makamai, lamarin da ya sa sojojin suka kare kansu.

    An bayyana cewa Dillo ya samu rauni ne a yayin musayar wuta kuma daga baya ya mutu.

    Yaya Dillo shine shugaban jam'iyyar Socialist Party Without Borders (PSF) kuma ƙani ga shugaban mulkin soja Mahamat Idriss Deby kuma ɗan takara mai karfi a zaben shugaban kasa da aka shirya yi a ranar 6 ga Mayu.

    • Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe
    • Manyan tambayoyin da shugaban Senegal ya ki amsawa a jawabinsa
  8. Yawan masu matsananciyar ƙiba ya zarce biliyan ɗaya a duniya – Bincike

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutum fiye da biliyan ɗaya ke fama da ƙiba a duniya.

    Bincike ya gano cewa yawan yara masu kiba ya karu sau hudu tun bayan shekarar 1990 yayin da adadin manya masu ƙiba ya ninka sau biyu.

    Masu binciken sun bayyana matuƙar mamaki a kan yadda alƙaluman suka ƙaru cikin sauri.

    Yawan masu fama da ƙiba a ƙasashen yankin Caribbean da Asiya ya ƙaru da kashi 60 cikin ɗari yayin da a Amurka adadin manya masu ƙiba ya kai kashi arba'in cikin 100.

    Wakiliyar BBC ta ce hukumar lafiya ta duniya ta ce ya kamata gwamnatoci da masana'antu abinci su rage farashin abinci mai inganci.

    Ta kuma ce akwai buƙatar a ƙarfafa gwiwar mutane a kan muhimmancin motsa jiki.

    • NFHS-5: Teɓa na kara yawa a jikin Indiyawa - kuma hakan babbar matsala ce
    • Kun san illolin yawan teɓa na dogon lokaci?
  9. Marhabun!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barkan mu da safiyar Juma'a. Da fatan muna lafiya.

    A yau, kamar kullum, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu domin karanta wainar da ake toyawa a duniya. Akwai sauran shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Intagram inda za ku iya zuwa domin karanta karin labarai da kallon bidiyo.