Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza

  1. Majalisar ministocin Senegal ta amince da dokar yin afuwa ga fursunonin siyasa

    ...

    Majalisar ministocin Senegal ta amince da dokar yin afuwa da nufin 'yantar da masu zanga-zanga da 'yan adawa da aka kama yayin zanga-zanga tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024, in ji shafin intanet na Dakaractu.

    Shugaba Macky Sall ya buƙaci a gabatar da kudirin a gaban majalisar dokokin kasar.

    Shugaba Sall bai bayar da karin bayani kan dokar da kuma yadda za ta iya shafar fitattun 'yan adawar kasar ciki har da madugun 'yan adawar kasar Ousmane Sonko da ke tsare a gidan yari a halin yanzu ba.

    Rahoton ya ƙara da cewa Sall ya kuma buƙaci gwamnati da ta ba da taimako ga iyalan wadanda suka mutu a zanga-zangar da ta barke a baya bayan nan.

    A ranar 3 ga Fabrairu, Sall ya ba da sanarwar ɗage zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa tun a ranar 25 ga Fabrairu, shawarar da Majalisar Tsarin Mulki ta soke ranar 15 ga Fabrairu.

    • Sojoji sun saki fursunonin siyasa a Guinea
    • Za a gafarta wa fursunonin siyasa a kasar Congo
  2. Amurka ta nuna damuwa kan dokar hana neman jinsi a Ghana

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce ta damu matuƙa da yadda Ghana ta amince da ƙudurin dokar hana neman jinsi abin da ta ce na barazana ga ƴancin tsarin mulki.

    "Ƙudurin zai kuma lalata tsarin lafiyar al'umma na Ghana da kafofin yaɗa labarai da tattalin arziki," in ji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Matthew Miller, cikin wata sanarwa.

    Amurka dai ta nemi a sake nazarin matsayin ƙudurin a kundin tsarin mulki.

    Sabon kudurin dokar da aka amince da shi ranar Laraba ya tanadi hukuncin shekara kusan uku a gidan yari ga duk wanda yake nuna kansa a matsayin mai neman jinsi.

    Ya kuma tanadi hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar ga wanda ya kafa ƙungiyar neman jinsi ko ɗaukan nauyin masu aƙidar.

    Ƙungiyoyin kare ƴancin bil adama sun caccaki matakin amincewa da ƙudurin dokar.

    Ƙungiyar Rightify Ghana ta yi kakkausar suka kan matakin wanda a cewarsu ke zama barazanar mutuwa ga ƴancin masu neman jinsi a ƙasar".

    Shugabar hukumar UNAIDS mai yaƙi da cutar ta HIV Aids ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya, Winnie Byanyima ta ce idan ya zama doka, yana iya janyo hatsaniya a tsakanin ƴan Ghana.

    Za a gabatar da ƙudurin dokar ga shugaba Nana Akufo Addo inda yake da mako ɗaya ya sanar da shugaban majalisa kan ko ya amince da ƙudurin ko kuma a a, kamar yadda kundin tsarin mulkin Ghana ya tanada.

    Idan kuma ya ƙi sa hannu, yana da kwana 14 ya bayar da dalilan da ya sa yake ganin ya kamata majalisa ta sake nazari a kai.

    • An tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk mutumin da ya ce mai neman jinsi ne a Uganda
  3. An dakatar da Ronaldo na wasa ɗaya

  4. Masu gidajen burodi sun janye yajin aiki a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya (AMBCN) ta bayyana cewa ta janye yajin aikin da ta shiga bayan wata tattaunawa da ta gudanar da jami'an ma'aikatar noma ta ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun shugabanta, Mansur Umar, ƙungiyar ta ce ta cimma wasu yarjeniyoyi da gwamnatin Najeriya a tattaunawar tasu, wanda hakan ya sanya ta sanar da janye yajin aikin wanda ta fara a ranar Talata.

    Daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyar da gwamnati sun haɗa da fitar da metric tan 25,000 na alkama nan take ga kamfanonin fulawa domin sarrafawa da samar wa masu sana'ar burodi.

    Haka nan ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya kan sake duba shirin samar da fulawa daga rogo da dankali da kuma dawa.

    Sannan kuma an cimma yarjejeniyar tallafa wa masu sana'ar ta burodi ƙarƙashin wani shiri na ma'aikatar noma ta Najeriyar.

    Masu gidan burodin a Najeriya sun shiga yajin aiki ne bayan kokawa da tsadar farashin kayan aiki, lamarin da ke kawo tarnaƙi a harkar sana'ar tasu.

    Najeriya na fama da tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ake dangantawa da cire tallafin man fetur a ƙasar da kuma wanu manufofi na gwamnati.

    • Masu gidajen burodi za su fara yajin aiki a Najeriya
    • Kotu ta dakatar da ƙungiyoyin ƙwadago daga shiga yajin aiki a Najeriya
  5. Kotu za ta yanke hukunci kan ko Trump na da kariya daga tuhuma

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun ƙolin Amurka ta amince ta yanke hukunci a kan ko za a iya gurfanar da tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump a gaban shari'a a kan zargin yunƙurin soke zaɓen shugaban ƙasar na shekarar 2022.

    Tuni dai kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da buƙatar da Mista Trump ya shigar a gabanta a kan cewa yana da rigar kariya a matsayinsa na shugaban ƙasa.

    A wani labarin kuma wata kotu a New York a jiya Laraba ta ƙi amincewa da buƙatar Mista Trump ɗin ta jinkirta biyan tarar dala miliyan 450 don aikata zamba.

    An dai gano cewa tsohon shugaban ƙasar Amurkan ya yi ƙarya game da darajar dukiyarsa domin kaucewa biyan haraji da inshorar lafiya.

    • Kotu ta umarci Donald Trump ya biya diyyar dala miliyan 83 ga wata marubuciyya
    • Me ya sa Trump ya fi sauran ƴan takarar Republicans farin jini?
  6. 'Likitocin da ke yajin aiki a Koriya ta Kudu na iya fuskantar matakin shari'a'

    ..

    Asalin hoton, REUTERS

    Gwamnatin Koriya ta Kudu ta yi barazanar ɗaukan matakin shari'a a kan dubban likitocin da ke yajin aiki idan ba su koma bakin aiki ba a ƙarshen wannan rana ta Alhamis.

    Ta kuma ce za ta dakatar da lasisin aikinsu.

    Kusan kashi uku bisa huɗu na ƙananan likitocin ƙasar sun dakatar da ayyukansu a makon da ya gabata.

    Likitocin dai na adawa ne da shirin gwamnatin ƙasar na ƙara yawan ɗaliban da ke karatun likitanci a kowace shekara.

    Wakiliyar BBC ta ce likitocin na ganin cewa matakin ba zai shawo kan matsalar ƙarancin likitocin da ake fuskanta a yankunan karkara da kuma sashin ba da kulawar gaggawa ba.

    Likitocin dai sun dage da cewa ya kamata a fara shawo kan kura-kuran da ke tsarin kiwon lafiyar ƙasar da suka haɗa da rashin biyansu albashi mai tsoka da kuma yanayin aiki.

    • Yadda yajin aikin likitoci masu neman kwarewa ya yi tasiri a asibitocin Najeriya
    • Yadda likitocin kasar waje ke fadawa halin da ka iya cutar da marasa lafiya yayin aiki a Birtaniya
  7. Ministan Burtaniya ya yi tayin ganawa da dangin wata macen Kenya da aka kashe

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ministan Sojin Birtaniya ya yi tayin ganawa da iyalan wata mata ‘yar Kenya da ake zargin wani sojan Birtaniya ne ya kashe ta fiye da shekaru goma da suka gabata.

    James Heappey ya shaida wa BBC cewa "kasancewar" ya fahimci irin radadin da 'yan uwan ​​Agnes Wanjiru ke ciki, wanda aka gano gawarta a shekara ta 2012 a cikin wani tanki mai ɗauke da ruwa a kusa da wani sansanin sojojin Birtaniya da ke Nanyuki a tsakiyar kasar Kenya.

    Da yake magana da BBC a wata ziyara da ya kai ƙasar, ya ce: "Na fahimci radadin da suke ciki..zan yi farin cikin haduwa da tattaunawa da kuma fahimtar yadda za a iya taimakawa iyalinta".

    A ziyarar da ya kai Kenya a baya, Heappey ya ba da shawarar ganawa tsakanin jami'an Burtaniya da dangin Wanjiru, amma ba a samu ko daya ba.

    A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne iyalanta suka rubuta budaddiyar wasiƙa zuwa ga Sarki Charles suna cewa "da alama jami'an Birtaniya ba su damu ba" game da ƴar su da aka kashe, kuma sun nemi sarkin ya kai masu ziyara a lokacin da yake tafiya kasar.

    Shekaru bakwai bayan mutuwar Wanjiru, wani bincike da aka gudanar a Kenya ya tabbatar da cewa sojojin Birtaniya daya ko biyu ne suka kashe ta.

    Bayan rahotannin da ake zargin an yi rufa-rufa ne, ma'aikatar binciken manyan laifuka ta Kenya ta buɗe wani bincike, amma har yanzu ba ta tuhumi kowa ba.

    • An saki wani mutum bayan kuskuren ɗaure shi tsawon shekara 28
    • An kama matashin da ake zargi da kashe kishiyar mahaifiyarsa a jihar Katsina
  8. Assalamu alaikum!

    Jama'a, barkan mu da safiyar Alhamis. Da fatan muna cikin ƙoshin lafiya.

    A wannan shafi na kai tsaye, BBC Hausa, kamar kodayaushe, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa musamman a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu, kuna kuma iya zuwa shafukanmu na sada zumunta inda za ku ga ƙarin labarai.