Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu dawo domin ci gaba da kawu muku wasu sabbin labarai

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Abba Kabir ya nuna damuwa kan salon wasu ayyukan Hisba a Kano

    ..

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/X

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan salon da hukumar Hisba ke bi wajen yaƙi da masu aikata baɗala a jihar.

    Yayin da yake jawabi a wani taro da ya yi da limaman Kano a gidan gwamnatin jihar, gwamnan ya ce Hisbah, hukuma ce mai albarka da aka ɗauketa da martaba, aka kuma damƙata a hannun bayin Allah da ake ganin za su iya jagorantarta.

    ''Mun ɗora musu amanar al'ummar jihar Kano mazansu da matansu, sannan da amanarmu, mu a matsayinmu na shagabanni'', in ji gwamnan.

    Abba Gida-gida ya ce ma'anar yin hukumar Hisbah shi ne ta yi abin da yake daidai wajen kawar da ɓarna sannan a bai wa gwamnati shawara.

    Amma saɓanin haka, gwamnan ya ce sai hukumar ta ɓuge da aikata wasu abubuwa da ba su dace ba.

    Gwamnan ya ce ya ga wani bidiyo da ya tayar masa da hankali, na yadda ma'aikatan hukumar ke kama waɗanda suke zargi da aikata laifi.

    ''Na ga wani bidiyo, inda ma'aikatan hukumar suka je wurin wasu matasa da ake zargi da aikata laifi, amma yadda aka ɗebo su ana dukansu da gora, suna gudu ana bin su da gora ana taɗe kafafunsu, ana ɗebo su kamar awaki a jefa su cikin mota, Allah ya kiyaye in kashin bayan wani ya karye, ya gama yawo har abada, wannan kuskure ne babba'', in ji gwamnan na Kano.

    ''Ka rungume matashiya ko matashi ka jefa shi kamar akuya cikin mota, wannan sam bai daidai ba ne''.

    ''Na ga wani bidiyo inda aka je ɗakunan ɗaliban jami'ar Bayero, har ɗakunansu ana duka ana rungumo su ana jifansu cikin mota, haƙiƙa wannan batu akwai gyara''.

    Gwamnan ya ƙara da cewa dole ne hukumar ta sake salo a daburunta na yaƙi da baɗala a jihar, saboda a cewarsa an saka hukumar Hisba ne don ta yi wa addinin musulunci hidima, amma idan ta bi wannan hanya, ba za a samu gyaran da ake so ba, domin waɗanda ake ƙoƙarin su gyarun, sai su kangare.

    ''Allah ya kiyaye idan waɗannan yara suka kangare mana to ba mu son halin da jiharmu za ta shiga ba''.

    Abba Kabir ya ce abin da ya kamata hukumar ta riƙa yi shi ne ta riƙa fita tare da 'yan sanda da 'yan sibil difen da jami'an DSS wuraren da ake aikata baɗalar a kamo su a kai su ga hukuma don a gurfanar da su a gaban kotu, ba tare da cutar da su ba.

    ''Allah ba ya son tazarci, kuma duk zunubin da mutum ke yi Allah ba ya son a tozarta shi, kun fi ni sanin haka'', kamar yadda ya shaida wa limaman.

    ''In dai za ku rika hawa mumbari kuna wa'azi da faɗakarwa, insha Allahu za a samu sauyi a ɓangaren tarbiyyar matasanmu'', in ji shi.

    Gwamnan ya kuma ce lallami da jan hankali cikin lumana shi ne abin da zai sa fitinannen mutum ya yi nadama kan munanan ayyukan da yake aiwatarwa.

  3. Waɗanda suka fi mutuwa ta dalilin ta'addanci a yankin Sahel suke - Binkice

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani nazari da aka yi na nuna cewa yankin Sahel da ke Afirka shi ne ya fi asarar mutane ta hanyar ta'adanci a faɗin duniya a shekarar da ta gabata.

    A bincikenta na shekara-shekara kan ta'addanci a duniya, Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki da Zaman Lafiya ta 'Instute for Economics and Peace' da ke birnin Sydney na ƙasar Australiya, ta ce yankin Sahel shi ne yake da kusan rabin yawan kashe-kashen ta'addanci a duniya.

    Binciken ya nuna cewa yankin Sahel ya samu ƙaruwar tashe-tashen hankali, inda yawan masu mutuwa ta hakan ya ƙaru da ninki 30 tun shekarar 2007.

    Rahoton ya kuma nuna cewa Burkina Faso ce ta fi asara, inda yawan masu mutuwar ya ƙaru da kusan kashi 70 cikin 100.

    Nazarin ya ƙara da cewa ta'addanci ya ƙara muni a makwabtan Burkina Faso, Nijar da Mali.

  4. Rooney ya bayyana burinsa na zama kocin Man United

  5. Bai kamata NLC ta kira yajin aiki a wata taran farko na mulkina ba - Tinubu

    .

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu bai dace ƙungiyar ƙwadagon ƙasar tu kira yajin aiki a watanni tara na farkon mulkinsa ba.

    Yayin da yake jawabi a birnin Legas ranar Alhamis lokacin ƙaddamar da layin dogo na Red line, shugaba Tinubu ya yi kira ga ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ta tabbatar da zaman lafiya, yana mai cewa ba ita ce kaɗai muryar 'yan NAjeriya ba.

    Ƙungiyar NLC da ta kira ga mambobinta su gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu, don nuna adawa da tsadar rayuwa da matsain tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar.

    To sai dai bayan zanga-zanga a rana ta farko, ƙungiyar ta janye zanga-zanagr da ta shiya yi a rana ta biyu, tare da bai wa gwamnati wa'adin mako biyu, ta ɓullo da matakan rage tsadar rayuwa a ƙasar.

    To sai dai shugaba Tinubu ya ce bai kamata ƙungiyar ta shirya yajin aiki a watanni tara na mulkinsa ba.

    “Ya kamata NLC ta fahimci cewa komai muka san 'yanci da haƙƙinmu, bai kamata ta kira yajin aiki a watanni taran farkon mulkina ba'', in ji Tinubu.

    “Idan kuna son shiga zaɓe, ku jira 2027. in ba haka ba kuwa, a ɗore da zaman lafiya, saboda ba ku kuɗai ba ne muryar 'yan Najeriya.''

  6. Shugaban Senegal ya tabbatar da lokacin da zai sauka daga mulki

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Senegal Macky Sall ya tabbatar da cewa zai sauka daga mulki idan wa'adinsa ya kare a ranar 2 ga Afrilu.

    A cikin wani sakon da aka wallafa a kan X, Shugaba Sall ya lura cewa "tattaunawar kasa" ta yi kira da a gudanar da zaɓen ƙasar a ranar 2 ga watan Yuni.

    To sai dai shugaban ƙasar bai ambaci ranar da za a gudanar da zaɓen ba.

    Ba a dai san wanda zai jagoranci ƙasar ba bayan Sall ya sauka daga mulki.

    A ranar 25 ga watan Fabrairu ne dai ya kamata a gudanar da zaɓen, amma shugaban kasar ya yi ƙoƙarin ɗage zaɓen har zuwa watan Disamba, domin a warware taƙaddamar cancantar sauran 'yan takara.

    Wannan dai ya haifar da zanga-zangar tarzoma a duk faɗin ƙasar da ke yammacin Afirka da aka saba samun kwanciyar hankali.

    Sai dai babbar kotun ƙasar ta ce an ɗage zaɓen ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasar, kuma ta yi kira da a gudanar da zaɓen cikin "gaggawa".

  7. Tsohon shugaban Tanzaniya Mwinyi ya rasu

    .

    Tsohon shugaban ƙasar Tanzaniya Ali Hassan Mwinyi ya rasu a asibitin birnin Dar es Salaam da ke ƙasar.

    An kwantar da marigayin mai shekara 98, a asibitin kan cutar kansar huhu, kamar yadda shugaban ƙasar Samia Suluhu ta bayyana.

    Mista Mwinyi ne shugaban Tanzaniya na biyu, da ya mulki ƙasar tsakanin shekarar 1985 zuwa 1995.

    Shi ne ya gaji wanda ya kafa ƙasar, Julius Nyerere da ya jagoranci Tanzaniya na tsawon shekara 23, tun bayan samun 'yancin ƙasar a shekarar 1961.

    Marigayin ya taɓa zama shugaban ƙasar Zanzibar tsakanin watan Janairun 1984 zuwa Octoban 1985, inda a yanzu ɗansa Hussein Ali Mwinyi ne shugaban ƙasar Zanzibar na yanzu.

    Mulkin Mista Mwinyi na tsawon shekara 10 ya bayar da damar faɗaɗa ɓangarorin siyasar ƙasar da tattalin arzikin ƙasar.

    Shi ne ya samar da tsarin siyasar jam'iyyu masu yawa a ƙasar a zaɓen 1995, inda Benjamin Mkapa ya zama shugaban ƙasar na uku.

    A lokacin shugabancinsa, kafafen yaɗa labarai da jam'iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula sun samu 'yanci.

    Shugabar ƙasar Sumia Suluhu ta ce za a gudanar da jana'izarsa ranar 2 ga watan Maris.

  8. 'Haɗe jami'ar sojoji da kwalejin horar da su zai sa Boko Haram ta cimma manufofinta'

    .

    Asalin hoton, Babagana Zulum/X

    Gwamnan jiar Borno Babagana Umara Zulum ya yi kira ga shugaban Najerya Bola Tinubu da ya sake nazari kan matakin haɗe Jami'ar Soji da ke Biu a jihar Borno da kwalejin horas da sojoji ta NDA.

    A wani mataki a rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa, gwamnatin ƙasar ta ce za ta haɗe makarantun biyu, a wani ɓangare na aiki da rahoton Steve Oronsaye.

    Yayin da ya ke jawabi ga manema labarai lokacin raba kayan tallafin abinci ga magidanta 100,000 a Maiduguri, Gwamna Zulum ya ce Boko Haram za ta cimma muradinta matuƙar aka soke jami'ar kula da aikin sojin ta Biu.

    “In dai zai yiwu, a bar ta a matsayin jami'ar sojoji, saboda muhimmancin da ilimi a wannan ɓangare na ƙasarmu, inda Boko Haram ke cewa ilimi haramun ne'', in ji Zulum.

    Ya ƙara da cewa ''Ina ganin, idan aka bari aka ɗauke jami'ar sojoji, Boko Haram za su iya cimma ɗaya zuwa biyu daga cikin muradunsu''.

    ''Don haka muna kira ga shugaban ƙasar ya duba wannan al'amari, ta yadda jami'ar sojoji ta Biu za ta ci gaba da kasancewa a matsayinta na jami'a.

  9. 'Mutum 112 sun mutu a hari da aka kai wa dandazon jama'a a Gaza'

    Ma'aikatar Lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce adadin mutanen da aka kashe a wani hari da aka kai musu lokacin da suke zaman jiran karɓar kayan tallafi abinci ya kai 112.

    Mai magana da yawun ma'aikatar, Dakta Ashraf al-Qudra ya ce mutum 760 ne suka jikkata a harin.

    Ya ƙara da cewa, shaidu sun bayyana masa cewa, har yanzu ba a gano gawarwakin wasu mutunen da suka mutun ba a shatale-talen Nabulsi, da ke kudu maso yammacin birnin Gaza.

    Dakta al-Qudra ya ce adadin mutanen da suka mutum ka iya ƙaruwa.

    Ma'aikatar lafiyar Hamas ta zargi dakarun Isra'ila da kai harin.

    Wata majya daga rundunar sojin Isra'ilar ta ce dakarunta sun buɗe wuta kan dandazon jama'ar ne bayan da suka fahimci wasu daga cikinsu na ƙoƙarin tunkurarsu a wani yanayi da ka iya jefa dakarun cikin hatsari.

  10. Hotunan yadda aka ƙaddamar da layin dogo na Red line a Legas

    .

    Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu

    A yau ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da layin dogo na 'Red line' na zamani a birnin Legas.

    .

    Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu

    Bayanan hoto, Aikin - mai tsawon kilomita 37 - zai karaɗe wasu manyan yankunan birnin, wanda shi ne cibiyar kasuwancin ƙasar.
    .

    Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu/X

    Bayanan hoto, Layin dogon na 'Red line' ya tashi ne daga Marina ya bi ta unguwannin Yaba da Mushin da Oshodi da Agege, ya dangana har zuwa Ibadan, sannan ya bi har zuwa filin Jirgin Murtala Muhammad.
    .

    Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu

    Bayanan hoto, A shekarar da ta gabata ne dai tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da layin dogo na 'Blue line' a jihar wanda ya tashi daga Marina zuwa unguwannin Alaba da Mile 2 da Festac da Alajika da jami'ar LASU ya dangana zuwa Maintenance Deport.
    .

    Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu/X

    Bayanan hoto, Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, shugaba Tinubu ya sake nananta ƙudurin gwamnatinsa na inganta abubuwan more rayuwa a ƙasar.
    .

    Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu

  11. Yadda 'yan bindiga suka sace mutum 30 lokacin sallar asuba a Zamfara

  12. Tinubu ya ƙaddamar da layin dogo na 'Red line' a Legas

    .

    Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da layin dogo na 'Red line' na zamani a jihar Legas.

    Aikin - mai tsawon kilomita 37 - zai karaɗe wasu manyan yankunan birnin, wanda shi ne cibiyar kasuwancin ƙasar.

    Layin dogon na 'Red line' ya tashi ne daga Marina ya bi ta unguwannin Yaba da Mushin da Oshodi da Agege, ya dangana har zuwa Ibadan, sannan ya bi har zuwa filin Jirgin Murtala Muhammad.

    A shekarar da ta gabata ne dai tsohon shugaban NAjeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da layin dogo na 'Blue line' a jihar wanda ya tashi daga Marina zuwa unguwannin Alaba da Mile 2 da Festac da Alajika da jami'ar LASU ya dangana zuwa Maintenance Deport.

    Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, shugaba Tinubu ya sake nananta ƙudurin gwamnatinsa na inganta abubuwan more rayuwa a ƙasar.

    Shugaban ƙasar ya ce babu gudu, ba ja da baya dangane da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ƙudiri aniyar aiwatarwa.

    Bayan ɗarewarsa kan karagar mulkin Najeriya shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ke biya, da barin kasuwa ta yi halinta dangane da farashin naira, lamarin da ya haifar da tashin farashin man fetur da hauhawar farshin kayayyaki da tsadar rayuwa

  13. Ana zargin wata jami'ar Kenya da tilastawa dalibai musulmi zuwa coci

    ..

    Asalin hoton, Daystar University

    Shugaban majalisar dokokin Kenya ya umarci ma'aikatar ilimin ƙasar ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da aka yi cewa wata jami'a na tilasta wa ɗalibai musulmai zuwa taron addu'oi a coci.

    Ana zargin jami'ar Daysar da ke zaman kanta wadda take wajen Nairobi, babban birnin Kenya.

    Jami'ar Daystar, wata cibiyar kiristoci ce mai zaman kanta da ke wajen babban birnin ƙasar, Nairobi, ana kuma zargin ta da hana daliban da suka ki halartar ibada a coci makinsu.

    Jami’ar dai ta musanta hakan, ta kuma ce ba ta hana waɗanda ba sa zuwa cocin maki a cewar kafafen yada labarai na ƙasar.

    Wani dan majalisar dokokin Kenya Mohammed Ali ne ya gabatar da zarge-zargen a majalisar, wanda ya ce manufar ta saba wa ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasar ta bayar.

    Ministan Ilimi Ezekiel Machogu ya ba da martanin jami’ar inda ya ce: “Jami’ar ta yi korafin cewa an duk ɗalibin da makarantar ta ɗauka na da cikakkiyar masaniyar cewa jami’ar cibiya ce ta kiristoci'"

    Ma'aikatar ilimin ta kuma ce za ta binciki rahotannin Mista Ali cewa cibiyar tana inganta ayyukan luwaɗi da maɗigo ta hanyar shigar da batutuwa akan su a cikin tsarin karatun ta.

  14. Sukar da ake yi wa Fernandes hassada ce - Ten Hag

  15. Putin ya gargaɗi ƙasashen Yamma game da tura sojoji Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A wani kakkausan saƙon da ya aika wa kasashen yammacin duniya da ke tunanin tura wa Ukraine sojoji, shugaban Rasha, Vladimir Putin ya bayyana cewa cewa ƙasarsa ta mallaki makaman da ke iya kai hari a yankunansu.

    Putin ya kuma yi Allah wadai da abin da ya kira "ƙiyayya ga ƙasar Rasha" wato 'Russophobia', yana mai bayyana 'yan Rasha a matsayin wadanda ke fama da wariya mara tushe.

    Da yake gargadi game da ƙaruwar tashe-tashen hankula, Putin ya bayyana hadarin da ke tattare da shiga cikin rikicin nukiliyar, wanda a cewarsa zai iya haifar da mummunar ɓarna.

    Yayin da wasu mambobin kungiyar tsaro ta NATO da suka haɗa da Amurka da Jamus da Birtaniya suka yi fatali da batun tura sojoji zuwa Ukraine, sanarwar da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi a baya-bayan nan na cewa "babu amfanin nuna wariya".

  16. Shugaban DR Congo ya yi tir da tashe-tashen hankula a ƙasar Chadi, Daga Chris Ewokor, BBC News

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Jamhuriyar Congo, Félix Tshisekedi ya yi tir da rikicin da ake a Chadi sakamakon mummunan harin da aka kai kan hedikwatar hukumar tsaron ƙasar.

    Mutane da dama aka kashe sakamakon rikicin da ya ɓarke.

    Mista Tshisekedi ya bayyana damuwa game da yanayin da ake ciki a Chadi inda ya ce lamarin na iya kawo tarnaƙi ga siyasar ƙasar yayin da zaɓen shugaban ƙasar ke tafe a ranar 6 ga watan Mayu.

    Mr Tshisekedi ya bayyana goyon bayansa ga hukumomin miƙa mulki a ƙasar.

    Ya yi maraba da matakinsu na gudanar da bincike na gaggawa domin gano mutanen da suke da hannu a lamarin sannan a gurfanar da su a gaban kotu.

    Wannan ne karon farko da aka mayar da martani daga wajen Chadi tun harin da gwamnati ta ɗora alhakinsa kan jam'iyyar hamayya ta Socialist Party Without Borders.

    Jam'iyyar dai ta musanta zargin inda ta ce jami'anta na wurin domin neman gawar mamba ɗinsu da aka kama sannan aka kashe

    Ana zaman ɗar ɗar a N'djamena babban birnin kasar Chadi, yayin da ake ci gaba da luguden wuta a yankuna da dama ciki har da hedikwatar jam'iyyar adawa.

  17. An dakatar da Pogba na tsawon shekara huɗu

  18. Yaya Dillo: An kashe jagoran ƴan adawar Chadi

    g

    Asalin hoton, ISSOUF SANOGO

    Wani mai shigar da kara na gwamnati ya ce an kashe wani madugun 'yan adawa a ƙasar Chadi yayin wani artabu da jami'an tsaro.

    Mutuwar Yaya Dillo na zuwa ne bayan da gwamnatin ƙasar ta zargi jam'iyyarsa ta adawa da kai wani mummunan hari da aka kai kan hukumar tsaron ƙasar, lamarin da Dillo ya musanta.

    A ranar Laraba ne aka ji karar harbe-harbe a kusa da hedkwatar jam’iyyarsa da ke babban birnin kasar.

    Mai gabatar da ƙara Oumar Mahamat Kedelaye ya tabbatar da mutuwar Dillo a ranar Alhamis.

    • Manyan tambayoyin da shugaban Senegal ya ki amsawa a jawabinsa
    • Wasu 'yan Najeriya sun ce 'yi wa Ukraine yaki ya fi zama a nan'
  19. 'Muna tsare da shugabannin Binance a Najeriya'

  20. An kashe mutum fiye da 30,000 a Gaza - ma'aikatar lafiyar Hamas

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce fiye da Falasdinawa 30,000 ne aka kashe a Gaza tun harin ranar 7 ga watan Oktoba.

    Wannan adadin ya yi daidai da kusan kashi 1.3 cikin 100 na al'ummar yankin miliyan 2.3 wadda ita ce mafi muni.

    Ma'aikatar ta ce aƙasarin waɗanda aka kashe mata ne da ƙananan yara.

    Alkaluman ba ta banbance tsakanin fararen hula da mayaƙa ba wajen tantance wadanda aka kashe.

    A cikin bayananta na yau da kullun a ranar Alhamis, ma'aikatar ta ce an kashe mutum 81 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin zuwa 30,035.

    Akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya zarce haka saboda adadin bai hada da waɗanda ba su kai asibiti ba, cikinsu har da dubban mutanen da suka rasa rayukansu a karkashin baraguzan gine-ginen da Isra'ila ta kai musu hari.

    Fiye da mutum 70,000 da suka jikkata ne ma’aikatar lafiya ta Gaza ta yi rajistarsu, wanda ita ce kadai hanyar da ta dace kuma za a iya amincewa da ita a hukumance.

    • Mutanen da suka samu mafaka a cocin Gaza 'na cikin fargaba'
    • Mutumin da aka kashe wa duk ƴan'uwansa 103 a Gaza