Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Cutar sanƙarau ta kashe ɗalibai 20 a Yobe

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Dalibai 20 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a makarantun sakandaren mata guda uku da kwalejin ‘yan mata ta gwamnatin tarayya da ke kananan hukumomin Potiskum da Fika a jihar Yobe.

    Kwamishinan Ilimi na primary da Sakandare na Jihar Yobe, Mohammed Sani-Idris a hirarsa da BBC ya tabbatar da mutuwar ɗaliban inda ya ce 17 daga cikin ɗaliban da suka mutum ƴan makarantar kwana ne kuma ragowar mutum uku ɗin ƴan primary ne.

    Kwamishinan ya kuma ce an kwantar da ɗalibai da dama a asibiti amma an sallame su.

    Ya kuma ƙara da cewa shi da sauran jami’ai sun koma garin Potiskum na ɗan wani lokaci domin hana yaɗuwar cutar.

    A halin da ake ciki Gwamna Mai Mala Buni wanda mataimakinsa Idi Barde-Gubana ya wakilta ya ziyarci makarantun da lamarin ya shafa domin ganin halin da ake ciki.

    Gwamnan ya ce: "A wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na shawo kan cutar tare da maganceta yadda ya kamata, gwamnati ta riga ta samar da magungunan gaggawa tare da tura tawagar gaggawa zuwa dukkan yankunan da abin ya shafa".

    A asibitin ƙwararru na Potiskum kuma, an samu adadin mutane 214 da suka kamu da cutar sannan uku kuma suna cikin sashin kula da lafiya na asibitin suna karbar magani.

    Irin wannan barkewar cutar ta kashe mutane da yawa mazauna yankin Degubi a karamar hukumar Fika ta jihar a watan Afrilun 2023.

    • Abin da ya sa cutar sanƙarau ke tasiri a Arewacin Najeriya
    • Alamomin kamuwa da cutar ƙyanda
  2. An halaka mutane a Chadi bayan yunƙurin kashe shugaban kotun ƙolin ƙasar

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Chadi ta ce an kashe mutane da dama bayan wasu mutane ɗauke da makamai, wadanda ake zargin 'yan jam'iyyar adawa ta Socialist Party without Borders ne suka kai wa hukumar tsaron kasar hari.

    Ministan sadarwa Abderaman Koulamallah ya fada a ranar Talata cewa, hakan ya biyo bayan yunkurin kashe shugaban kotun ƙolin kasar, yana mai zargin sakataren kudi na jam'iyyar adawa ta Socialist Party without Borders da hannu a shirin.

    An kama jami'in jam'iyyar da ake zargi amma a ranar Talata, kuma 'yan jam'iyyarsa sun ce "an kashe shi".

    Gwamnatin ta ce ta kama wasu da dama da suka kai harin, yayin da ake ci gaba da neman sauran amma kuma babu tabbas kan cewa an kama shugaban jam'iyyar, Yaya Dillo, amma a wani sako da ya wallafa a Facebook da safiyar Laraba, ya ce sojoji sun kewaye su.

    Wannan na zuwa ne mako guda bayan da shugaban kotun kolin ya bayyana cewa an kai wa ofishinsa hari.

    A halin yanzu jami'an tsaro na sintiri a titunan N'Djamena, yayin da al'ummar ƙasar suka shiga cikin fargaba.

    • Rikicin Chadi: Dakarun ƙasar da 'yan tawaye sun ci gaba da gwabza faɗa a Lardin Kanem
    • Kawuna sun rabu kan korar da sojojin Nijar ke wa ƙasashen duniya
  3. Ƙasar Chadi za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 6 ga Mayu

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    A ranar 6 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaɓen shugaban kasar Chadi, wanda zai kawo karshen mulkin soji na shekaru uku da aka soma bayan shugaba Mahamat Idriss Deby Itno ya hau ƙaragar mulki bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 2021.

    Shugaban hukumar zaɓen kasar Ahmed Bartchiret, ya bayyana muhimman ranakun da za a gudanar da zaben shugaban kasar a lokacin da yake ganawa da manema labarai a babban birnin kasar, N'Djamena, kamar yadda shafin intanet na Tchadinfos mai zaman kansa ya ruwaito.

    Bartchiret ya jaddada muhimmancin gudanar da zaɓen kafin lokacin damina, inda ya buƙaci abokan huldar fasaha da na kudi da su ba da hadin kai ga shirin zaɓen kasar.

    Yayin da har yanzu shugaba Deby bai bayyana sake tsayawa takara ba a hukumance, ‘yan adawa sun buƙaci da kada ya sake neman wani wa’adi

    Deby, mai shekaru 38, ya yi alkawarin shirya zaɓuka cikin watanni 18 bayan ya ɗare kan ƙaragar mulki a watan Afrilun 2021.

    Duk da haka, gwamnatinsa ta soji ta ci gaba da riƙe madafun iko, inda ta ƙara wa'adin mulkinta da ƙarin watanni 18.

    • Ana zaben shugaban kasa a Chadi da Jamhuriyar Benin
    • Rikicin Chadi: Dakarun ƙasar da 'yan tawaye sun ci gaba da gwabza faɗa a Lardin Kanem
  4. An tsayar da ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Senegal

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    A jiya ne aka kammala tattaunawar da shugaban kasar Senegal Macky Sall ya kira kan rikicin siyasar kasar tare da yarjejeniyar gudanar da zaɓe a ranar 2 ga watan Yuni, kamar yadda gidan talabijin na ƙasar RTS ya ruwaito.

    Duk da cewa mafi yawan 'yan adawa sun kaurace wa tattaunawar, waɗanda suka mamaye taron ƴan ƙawancen Sall ne.

    Wakilai, da suke magana a RTS, sun nuna cewa ranar da aka zaɓa za ta ba da damar gudanar da zabukan bayan sallar Idi da kuma gabanin damina.

    Duk da iƙirarin da Shugaba Sall ya yi na cewa wa'adinsa zai kare ne a ranar 2 ga Afrilu, mahalarta taron sun ba da shawarar ya ci gaba da aiki a matsayin shugaban ƙasar har sai an rantsar da magajinsa.

    Waɗannan shawarwarin daga tattaunawar za su buƙaci amincewar shugaban kasa kafin a mika su ga Majalisar Tsarin Mulki don tabbatar da su.

    Ƙasar Senegal dai ta tsinci kanta a cikin rikicin siyasa mafi muni cikin shekaru da dama bayan da shugaba Sall ya yanke shawarar ɗage zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.

    • Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe
    • Ɗage zaɓen Senegal ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasar - kotu
  5. Mutum 31 sun mutu bayan da mota ta faɗo daga gada a Mali

    ..

    Asalin hoton, REUTERS

    Mutum 31 ne suka rasa rayukansu a Mali bayan da wata motar bas ta kife sannan ta faɗo daga wata gada da ke kudu maso yammacin ƙasar.

    Akalla mutum goma ne suka jikkata, wasu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.

    Motar dai ta taso ne daga garin Kenieba na ƙasar Mali kuma tana kan hanyar zuwa Burkina Faso mai maƙwabtaka lokacin da hatsarin ya faru.

    Jami’ai sun ce watakila motar bas ɗin ta kuɓuce ne daga hannun direban shi yasa ta faɗo daga gadar.

    ..
  6. Yadda mata za su kaucewa matsalolin da daina al'ada kan haifar

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon bincike ya nuna cewa mata da suka daina jinin al'ada waɗanda ke fama da matsalolin da suka shafi lafiyarsu za su iya samun sauƙi ta hanyar sauya halayyarsu da tunaninsu.

    Masu bincike daga jami'ar kwalejin Landan sun yi nazari a kan mata masu fama da wannan larura fiye da dubu uku daga ƙasashe 13.

    Sun yi nazari kan tasirin hanyoyin warkewa a kan yadda mata ke tunani da kuma ingancin rayuwarsu.

    Ƙwarrarun sun ce za a iya amfani da tsarin wajen taimaka wa mata masu wannan lalura a maimakon basu magunguna.

    • Me ya sa mata ke samun sauye-sauyen halayya a lokacin jinin al'ada?
    • Me ya sa wasu mata ke daina al'ada a lokacin da suke kan ganiyarsu?
    • Ko shekarun daina al'adar mace na illa ga rayuwar aurenta?
  7. Abin da ya sa mata ba sa haihuwa a Koriya ta Kudu

    ..

    Asalin hoton, JEAN CHUNG

    Gwamnatin Koriya ta Kudu ta ce an samu matuƙar raguwa a yawan mata masu haihuwa a ƙasar duk da cewa ta kashe biliyoyin kuɗi a shirye-shiryen ƙarfafa gwiwar mata wajen samun ƙarin yara.

    Yawan yaran da ake sa ran mace za ta haifa a rayuwarta a Koriya ta Kudu ya ragu ƙasa da kashi ɗaya cikin 100 a bara.

    Wakiliyar BBC ta ce ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka samu wannan raguwa shi ne kawo yanzu mata na ganin cewa ba za su iya aiki tare da samun iyali ba.

    An dai yi hasashen cewa idan yanayin haihuwar ya ci gaba da kasancewa haka, yawan shekarun masu aiki a ƙasar zai rabu gida biyu nan da shekaru arbain masu zuwa.

    • Matan da aka juyar musu da mahaifa saboda suna da cutar HIV
    • Yaushe ne za a ce namiji ya tsufa da haihuwa?
  8. Assalamu Alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa assalamu alaikum. Barkan mu da safiya.

    Ku kasance da mu a wannan shafi don karanta labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sasssan duniya.

    Da fatan za ku biyo mu. Kuna iya zuwa shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da kuma Instagram inda za ku karanta arin labarai da kallon bidiyo.