Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba dakawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Matar Navalny ta zargi Putin da zama jagoran masu aikata laifuka

    Matar marigayi jagoran 'yan hamayya na Rasha, Alexei Navalny, ta ce Shugaba Putin ba dan siyasa ba ne, jagora ne na gungun masu aikata miyagun laifuka da sanya wa mutane guba da kuma kisan gilla.

    Da take gabatar da jawabi ga majalisar dokokin Tarayyar Turai a Strasbourg, Yulia Navalnaya, ta buƙaci 'yan siyasa da jami'an Turai su yaƙe shi kamar yadda za su yaƙi, ƙungiyoyin masu aikata miyagun laifuka,

    Kuma su binciki hanyoyin da yake samun kuɗaɗe.

    Ta ce ba ta yadda za a yi galaba a kansa ta hanyar tattaunawa da sanya takunkumi ba.

    Mrs Navalnaya ta kuma lashi takobin ci gaba da gwagwarmayar mijinta, bayan abin da kira kisan gillar da aka yi masa.

  3. Mutum miliyan 61 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a a Iran

    Hukumar zaɓen Iran ta ce fiye da mutum miliyan 61 ne suka cancani kaɗa ƙuri'a a zaɓe ƙasar da ke tafe cikin makon nan.

    Hassan Eslami ya ce mutum miliyan 31 daga cikinsu maza ne, yyin da mata suka kai miliyan 30.

    A ranar Juma'a ne za a gudanar da zaɓen kujeru 290 na majalisar dokokin addinn musuluncin ƙasar, da kuma kujeru 88 na majalisar shuran ƙasar.

    Jagoran addinin ƙasar, Ali Khamenei, ya yi kira ga 'uyan ƙasar da su fito domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen, yana mai cewa babu zaɓen da ba shi da amfani.

  4. Najeriya ta sanya harajin dole ga kamfanonin da ke ɗaukar ma'aikata daga ƙetare

    .

    Asalin hoton, X/Bola Tinubu

    Gwamnatin Najeriya ta sanya harajin dole na shekara-shekara ga kamfanonin da ke ɗaukar ma'aikatan ƙasashen waje.

    Gwamnatin ta buƙacin kamfanonin su riƙa biyan harajin dala 15,000 ga kowane darakta, da kuma dala 10,000 daga sauran ma'aikata.

    Shugaban ƙasar Bola Tinubu, wanda ke cikin matsin lambar inganta tattali arzikin ƙasar, ya ce matakin zai ƙarfafa wa kamfanonin ƙasashen waje gwiwa wajen ɗaukar 'yan ƙasar aiki.

    Dama dai kamfanonin ƙasashen waje na biyan dala 2,000 a kowace shekara domin samun izinin zama a ƙasar ga ma'aikatansa 'yan ƙasashen waje.

    A yanzu kuma za su biya ninki biyar na wannan kuɗi, idan suna son ci gaba da aiki da ma'aikatansu 'yan ƙasashen wajen.

    Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ba ta ɗauki matakin don dankwafe masu zuba jari a ƙasar daga ƙetare ba.

    Ɗaya daga cikin alƙawuran da shugaban ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe shi ne mayar da Najeriya ƙasar da za ta ja hankalin masu zuba jari daga ƙetare.

    To sai dai wannan mataki zai sa da dama daga kamfanonin su ƙaurace wa zuwa ƙasar.

    Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki mafi muni a tarihi, da ake ganin an samu sakamakon tsare-tsaren gwamnati ciki har da cire tallafin man fetur.

  5. MTN ya nemi afuwar abokan hulɗarsa kan ɗaukewar sabis a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, MTN

    Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya nemi afuwar aboka huldarsa sakamakon matsalar ɗaukewar sabis da kamfanin ya fuskanta a faɗin ƙasar.

    Tun da tsakar ranar Laraba ne dai masu amfani da layin MTN suka fara fuskantar matsalar ɗaukewar sabis a layukansu.

    To sai dai kamfanin cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce hakan ya faru ne sakamakon yankewar wasu wayoyin sadarwar kamfanin, lamarin ya ya shafi kira da kuma fannin intanet a layin.

    Kamfanin ya kuma ce injiniyoyinsa na aiki domin shawo kan matsalar, inda ya ce sannu a hankali sabis ɗin ya fara dawowa a wasu yankuna.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. An ji ƙarar harbe-harbe a N'Djamena babban birnin ƙasar Chadi

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    An ji ƙarar harbe-harbe a Djemena babban birnin Chadi bayan mummunan hari kan shalkwatar tsaron ƙasar .

    Mutane da dama ne suka mutu a harin da gwamnati ta zargi jam'iyyar adawa da kaiwa.

    Kamfanin sadarwar intanet na Netblocks ya ce an kaste layukan sadarwa a ƙasar.

    Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin ƙasar ta sanar da cewa za a yi zaɓen shugaban ƙasar ranar 6 ga watan Mayu.

    Cikin wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta fitar, wadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani, gwamnatin ta ce ''za a gurfanar da duk mutumin da aka samu da laifin tayar da zaune-tsaye ko kawo tarnaƙi da tsarin dimokraɗiyya a ƙasar''.

    Gwamnatin ta ce ta kama mambobn jam'iyyar PSF mai mahayya bisa zargin kai hari shalkwatar tsaron ƙasar, ta kuma ce za a gurfanar da su a gaban kotu.

    Ministan sadarwar ƙasar, Abderaman Koulamallah, ya ce shugaban jam'iyyar PSF Yaya Dillo ne ya jagoranci harin, to sai dai har yanzu shugaban bai ce komai ba.

    Mazauna birnin N'Djamena sun bayar da rahoton cewa sun ji ƙarar harbe-harbe a kusa da shalkwatar jam'iyyar PSF ranar Laraba.

    Yayin da suka ce sun ga motocin sojoji na nufar yankin da ake jin ƙarar harbin.

  7. Ghana ta amince da hukuncin shekara uku ga masu auren jinsi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Ghana ta amince da dokar ɗaurin shekara uku ga masu neman jinsi, da kuma shekara biyar ga masu sauya jinsi a faɗin ƙasar.

    Dokar ta sha suka sosai a ƙasar, saboda yadda ake ganin ta tauye 'yancin tsirarun mutane a ƙasar.

    Ghana ce ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta amince da dokar haramta auren jinsi bayan Uganda.

    Sabuwar dokar ta amince da ɗaurin shekaru har zuwa 10 a gidan yari, ga duk wanda aka samu da wallafa wani abu da nufin koyar da yara, ko ɗaukar nauyin ayyukan masu neman jnsi a ƙasar.

    Dokar ta kuma ƙarfafa wa 'yan ƙasar gwiwa da su kai rahoton ayyukan masu neman jinsi ga 'yan sanda, yayin da 'yan jarida za su iya shiga hatsari idan aka same su da laifin rahoton rajin kare masu neman jinsi.

    A watan Agustan 2021 ne dai aka gabatar da ƙudurin a majalisar dokokin ƙasar, inda kuma ya fuskanci suka mai girma a faɗin ƙasar.

    Masu adawa da dokar sun ce za ta tauyen 'yancin jima'i da dokar ƙasa ta bai wa tsirarun mutane

    To amma masu goyon bayan dokar sun ce za ta taimaka wajen kare dokokin iyali na mutanen Ghana.

    Dokar za ta fara aiki ne idan shugaban ƙasar Nana Akufo Addo ya sanya mata hannu.

  8. 'Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 a Taraba

    .

    Asalin hoton, X/Nigeria Police

    'Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 da aka yi garkuwa da su a sansanin masu garkuwa da mutane da ke tsaunin Gongomaliki a yankin ƙaramar hukumar Yorro da ke jihar Taraba.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar, David Iloyanomon, ne ya bayyana haka cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a birnin Jalingo.

    Kwamishinan ya ce jami'an sun samu nasarar kuɓutar da mutanen ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukna ɓata-garin a yankin.

    “Wannan na daga cikin yunƙurin da hukumarmu ke yi na kakkaɓe ayuukan ɓata-gari, musamman garkuwa da mutane da fashi da makami da satar shanu da ke addabar jiharmu,'' in ji CP David Iloyonomon.

    Ya ƙara da cewa hukumar 'yan sanda ta ɗauki matakan tattaunawa da masu ruwa da tsaki kamar mafarauta da 'yan sa kai domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

    Jihar Taraba na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan masu satar mutane domin neman kuɗin fansa, da 'yan fashin daji da masu satar shanu.

  9. A rufe duka layukan da ba haɗa da NIN ba - NCC

    .

    Asalin hoton, .

    Hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC ta sake jaddata umarninta ga kamfanonin sadarwar na ƙasar da su rufe duka layukan wayar da ba a haɗa su da lambar katin ɗa ƙasa ta NIN ba.

    Daraktan yaɗa labaran hukumar, Mista Reuben Mouka, ne ya bayyana umarnin a lokacin wani taron kasuwanci da aka gudanar a Kaduna.

    Mista Mouka ya ce dole ne masu amfani da layin waya su haɗa shi da lambar katin ɗan ƙasarsu ta NIN.

    Ya ce an ɗauki matakin ne don magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

    Mista Mouka ya jaddada wa'adin yau Laraba, 28 ga watan Fabrairu da aka bai wa kamfanonin sadarwar su rufe duka layukan da ba a haɗa da lambar NIN ba.

    Dama dai hukumar NCC ta ɗaɗe tana kiran al'ummar ƙasar da su haɗa lambar wayarsu da ta katin ɗan ƙasarsu wato NIN, a wani mataki na daƙile ayyukan matsalar tsaro a ƙasar.

  10. An sako wasu ‘yan Italiya uku da aka yi garkuwa da su a 2022 a Mali

    ...

    Asalin hoton, AFP

    An sako wasu ‘yan ƙasar Italiya uku da aka yi garkuwa da su a Mali a watan Mayun 2022, kamar yadda wani gidan intanet na Bamako ya ruwaito jiya.

    Rahoton ya ce "An sako Rocco Langone da matarsa ​​Maria Donata Caivano da ɗansu Giovanni Langone, 'yan ƙasar Italiya da aka yi garkuwa da su a ranar 19 ga Mayu, 2022 a kusa da Koutiala a kudancin Mali a daren ranar 26-27 ga watan Fabrairu."

    Rahoton ya bayyana cewa, kungiyar Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin mai alaka da al-Qaida ce ta yi garkuwa da mutanen uku.

    Ba a dai bayyana yadda aka kuɓutar da mutanen uku ba, amma rahoton ya ce jami'an tattara bayanan sirri na Italiya ne suka yi aikin kuɓutar da su ta hanyar tuntubar shugabannin yankin.

    Ƙasar Mali dai na ƙoƙarin shawo kan rikicin da aka kwashe shekaru goma ana gwabzawa da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka kawo tarzoma a yankin, inda ‘yan bindiga ke amfani da ƙasar a matsayin wani shingen kaddamar da hare-hare a yankin Sahel.

  11. Ukraine ta ce an fatakki dakarunta a Donetsk

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Dakarun Ukraine sun ce an fatattake su daga wasu ƙauyuka biyu na yankin Donetsk, yayin da ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO da dama suka ƙi amincewa da buƙatar tura sojojin su domin taimaka wa ƙasar a yaƙin da take da Rasha.

    Wani kakakin rundunar sojin Ukraine ya ce yanzu haka dakarun su sun janye daga wasu sansanoni uku da ke kusa da Avdiivka, tun bayan da sojojin Rasha suka ƙwace garin a farkon watan nan.

    Ya ce Rasha ta tafka gagarumar asara a arangamar da sojojin suka yi a yankin.

    Sai dai ya ce dakarun Ukraine sun janye daga yankin Avdiivka, ne saboda ƙarancin kayan yaƙi, da suka haɗa da bindigogi da harsasai da kuma manyan makamai.

    Shekara biyu da fara wannan yaƙi dai, Ukraine ta dogara ne ga ƙasashen Yamma wajen samun makamai.

    Amurka da Jamus da Italiya da kuma Birtaniya duk sun ce ba za su tura dakarunsu Ukraine ba, bayan shugaba Macron na Faransa ya ce bai kamata a ƙayyade irin taimakon da za a iya bai wa ƙasar a yaƙin da take da Rasha ba.

    Kalaman na shugaban Faransa sun janyo martani daga fadar Kremlin, wadda ta ce za ta ɗauki duk wani mataki na tura dakarun NATO Ukraine a matsayin yin fito na fito da ita, lamarin da kuma ta ce ba za ta ɗauka da wasa ba.

  12. 'Babu wanda zai rasa aikinsa lokacin haɗe hukumomin gwamnati'

    .

    Asalin hoton, X/Mohammed Idris

    Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce babu ma'aikacin da zai rasa aikinsa wajen aiwatar da rahoton Oronsaye, wanda ke neman a haɗe ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.

    Idris ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba a taron manema labarai karo na hudu na ministoci.

    “Abin nufi shi ne gwamnati na son rage tsadar kayayyaki da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyuka. Ba wai yana nufin gwamnati na shirin korar ma’aikata ko jefa mutane cikin kasuwar kwadago ba,” inji shi.

    Ministan ya ce aiki da rahoton wata alama ce karara ta jajircewar Shugaba Tinubu na yin taka-tsantsan a kasafin kudi da gudanar da mulki ta hanyar yin nazari mai zurfi a kan kwamitocin gwamnati, da hukumomi, da ma’aikatun gwamnati.

    Ya ce amincewa da yin aiki da rahoton na Orosanye, wanda ya biyo bayan nazari mai zurfi, shi ne tabbatar da cewa ba a yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyuka masu muhimmanci, sannan kuma a magance bukatun ‘yan kasa yadda ya kamata tare da sanya bukatun al’umma a gaba.

    “Ta hanyar aiwatar da rahoton Oronsaye, Shugaba Tinubu yana da niyyar cimma babban tanadin farashi ta hanyar kawar da kwafin ayyuka da daidaita tsarin gudanarwa, da inganta rabon albarkatu."

    Wannan tsari na sa ido zai bai wa gwamnati damar gudanar da aiki yadda ya kamata tare da kiyaye inganci da isar da ayyuka ga al’ummar Najeriya,” inji shi.

    Ministan wanda ya ce ‘yan Najeriya sun fara ganin alfanun sauye-sauyen da shugaban ƙasa ke jagoranta a sassa daban-daban, ya jaddada cewa rahoton da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar na nuni da cewa Najeriya ta samu ƙaruwar kuɗin da ake samu a cikin ƙasa da kashi 3.46 cikin 100.

  13. Benin za ta aika da jami'an tsaro sama da 1,000 zuwa Haiti

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jamhuriyar Benin na shirin tura jami'an 'yan sanda da sojoji sama da 1,000 zuwa ƙasar Haiti domin taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci a yankin Caribbean, kamar yadda gidan rediyon Faransa RFI ya ruwaito.

    Duk da yake ba a bayar da sanarwar a hukumance ba, ana ci gaba da shirye-shiryen.

    Ministan harkokin wajen Benin Olushegun Bakary da babban hafsan hafsan sojin kasar Janar Fructueux Gbaguidi sun halarci taron ministocin harkokin wajen ƙasashen G20 da aka yi a Brazil a makon jiya domin tattaunawa da gabatar da shirye-shiryen tura jami'an tsaron.

    An kiyasta jimillar tawagar jami'an tsaron tsakanin 1,000 zuwa 1,500.

    Ƙasar Benin dai tana da tarihin bayar da gudunmawar jami'an tsaro ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya a Haiti tun daga shekarar 1994.

    Sai dai kuma tawagar Haiti karkashin jagorancin Kenya ta fuskanci tsaiko saboda kalubalen shari'a, da karancin kuƊade, da kuma batutuwan kayan aiki.

  14. Ƴan sanda sun kama mahaifin da ya harbe ɗansa kan abinci a Abiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansanda a jihar Abiya ta kama wani mutum da ake zargi da harbe ɗansa bayan da ya fusata saboda ya cinye abinci.

    Lamarin ya faru ne a yankin Eziama Lokpaukwu da ke ƙaramar hukumar Umunneochi a jihar Abiya.

    Shaidu sun ce ɗan ya shiga gidan inda ya ɗauki abincin da aka ajiye a tukunya tare da cinyewa.

    Lamarin ya fusata mahaifinsa saboda rashin neman izini kafin cinye abincin sai kuma suka ce ya shiga ɗaki tare da harbe ɗansa.

    Mutanen yankin sun fusata inda suka damke mahaifin tare da ƙulle shi kafin ƴan sanda su bayyana.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar Maureen Chinaka ta tabbatarwa da BBC faruwar lamarin.

    Ta ce rundunar ƴansandan ta samu rahoto game da lamarin inda jami'ai suka cafke shi tare da ɗauke gawar yaron domin gudanar da bincike a kanta.

    Maureen Chinaka ta ƙara da cewa an miƙa batun ga sashen da ke lura da manyan laifuka domin ci gaba da bincike.

    • Uba 'ya kashe 'yarsa' a Kano don ta dame shi da kuka
    • An kama matashin da ake zargi da kashe kishiyar mahaifiyarsa a jihar Katsina
  15. NLC na shan suka saboda ɗage zanga-zangar tsadar rayuwa

  16. Mun gano haramtattun matatun mai 84 cikin mako ɗaya – NNPCL

    ..

    Asalin hoton, @nnpclimited/X

    Kamfanin sarrafa albarkatun mai na Najeriya, NNPCL ya ce ya gano haramtattun matatun mai 84 da haramtattun bututan mai 66 cikin makon da ya gabata a yankin Neja Delta.

    Cikin wani saƙo da NNPCL ya wallafa a shafin X, ya ce "a makon da ya wuce, an gano haramtattun bututan mai 66 da haramtattun matatun mai 84 a yankin Neja Delta."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Satar ɗanyan mai babbar matsala ce a Najeriya - ɗaya cikin mambobin ƙungiyar ƙasashe masu arzikin mai kuma ɗaya daga cikin ƙasashen nahiyar Afirka mafi samar da arzikin mai.

    Najeriya dai tana asarar kusan gangar mai dubu ɗari biyu a duk rana saboda masu haramtattun matatun mai da kuma masu satar man.

    Galibin mutane a yankin Neja Delta na rayuwa cikin talauci duk da cewa ƙasar ce mafi samar da man fetur a Afirka inda take samar da kusan ganga miliyan biyu duk rana.

    • Kamfanin NNPC ya ƙara farashin man fetur a Najeriya
    • NNPC zai soma hako danyen mai a jihar Nassarawa
  17. Ko kun san makomar masu adawa da Putin?

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Akwai makoma guda ɗaya ga wadanda suka ƙalubalanci Shugaba Vladimir Putin a Rasha.

    Dukkan su sun yi mutuwar da take da alamar tambaya.

  18. Mutum biyar sun mutu bayan rushewar gini mai hawa biyu a Anambra

    ..

    Asalin hoton, @CCSoludo/X

    Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya tabbatar da mutuwar mutum biyar da jikkatar wasu 26 sakamakon rushewar wani gini mai hawa biyu a kasuwar Odu-Igbo a birnin Onitsha.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin da lamarin ya faru bayan da ya je domin duba ibtila'in.

    A cewar gwamnan, gwamnati za ta biya kuɗin maganin mutanen da ke samun kulawar likitoci a asibitoci.

    Ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a lamarin.

    Gwamnan ya kuma umarci ɗan kwangilar da ke kula da ginin da ya kawar da ɓuraguzon ko ya fuskanci fushin hukuma.

    Ya ce gini ba bisa ƙa'ida ba na ci gaba da zama babban ƙalubale da jihar ke fuskanta.

    Ya kuma ba da umarnin cewa sai an samu amincewar gwamnati kafin tada gini a duk wata kasuwar jihar Anambra.

    • Mutum 11 ne suka mutu a rushewar gini a Legas
    • Abu 10 da muka sani bayan rushewar gini mai hawa 21 a Legas
  19. Abin da rahoton Oronsaye ya ƙunsa

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  20. Za a binne Alexei Navalny ranar Juma'a a birnin Moscow

    ...

    Asalin hoton, shutterstock

    A ranar Juma'a ne za a binne gawarAlexei Navalny a wata maƙabarta a birnin Moscow, kamar yadda wani mai magana da yawu ya tabbatar.

    Za a fara taron adu'o'i a maƙabartar Borisovskoye bayan bikin bankwana a gundumar Maryino.

    A farkon makon nan, mai magana da yawun Navalny ta bayyana kalubalen da tawagarsa ke fuskanta wajen neman wurin da za ayi jana'izarsa inda wasu wuraren suka ki karbar bakuncin hidimar jana'izar bayan sanin asalin wanda ya mutu.

    Navalny, wanda fitaccen ɗan adawa ne, ya mutu a wani gidan yari na Arctic a farkon wannan watan.

    An san shi da kakkausar suka ga shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin, Navalny ya dade yana fice a fagen siyasar Rasha.

    • Taron G20: Ƙasashe sun soki Rasha kan mutuwar Alexei Navalny
    • Yevgeny Prigozhin: Putin ya miƙa ta'aziyya kan mutuwar shugaban Wagner