A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kusan kashi 75 cikin 100 na al'ummar Gaza, kusan mutane miliyan 1.7, sun riga sun yi rajista a matsayin 'yan gudun hijira kafin Isra'ila ta ba da gargadi ga Falasdinawa su fice daga arewacin Gaza.
'Yan gudun hijirar Falasɗinawa, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana, "mutane ne wadanda Falasɗinu ne wurin zamansu a tsakanin 1 ga Yuni a 1946 zuwa 15 ga Mayu 1948, kuma wadanda suka yi hasarar gidajensu da hanyoyin rayuwa a sakamakon yakin shekarar 1948".
Sama da ƴan gudun hijira 500,000 suna zaune a sansanoni takwas masu yawan jama'a da ke warwatse a ko'ina cikin yankin.
Bayan gargadin da Isra'ila ta yi bayan ranar 7 ga Oktoba, yawancin 'yan gudun hijirar, tare da dubban daruruwan wasu, an tilasta musu barin gidajensu, a cewar MDD.
A halin yanzu, kimanin Falasdinawa miliyan 1.7 ne suka nemi mafaka a matsugunai na wucin gadi ko wuraren da aka kafa a kusa.
Kafin rikicin, yawan al'ummar Gaza ya kai sama da mutum 5,700 a kowace kilomita, kwatankwacin matsakaicin yawan jama'a a birnin London.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa sama da rabin al'ummar Gaza a yanzu suna mafaka a Rafah, garin na mutane 250,000 kacal.