Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Habiba Adamu
Rufewa
Masu bibiyar mu duka-duka a nan muka kawo karshen kawo muku labaran kai tsaye. Da fatan za ku kasance da mu a ranar Laraba da safe inda za mu ci gaba da kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. Kafin nan ku ci gaba da kasancewa da shafukan BBC Hausa domin karanta labarai da rahotanni na musamman da muka wallafa muku.
Usman Minjibir da Aisha Babangida ke fatan Allah ya tashe mu lafiya.
Gwamnatin Japan za ta ba da tukwici domin ƙarfafa aure da hayayyafa
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Japan ta ce za ta ba da tukwici domin ƙarfafa yin aure da hayayyafa a ƙasar.
Gwamnatin ta ce akwai tsare-tsare na ɓullo da doka kan hakan.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da yawan mutanen Japan ya ragu da kusan mutane miliyan guda a bara, yayin da kuma waɗanda suka tsufa ne suka fi yawa.
Yawan jama'ar ƙasar ya yi kasa da dubu dari takwas da talatin yayin da kuma yawan haihuwa ya yi ƙasa sosai -- kuma an samu ƙarancin aure fiye da kowane lokaci tun bayan yaƙin duniya na biyu.
Raguwar yawan al'ummar ƙasar na faruwa ne cikin sauri fiye da yadda ake tsammani.
Gwamnatin Japan ta ce kasar tana da wa'adi zuwa shekarar 2023 kacal domin ta shawo kan lamari.
Jimlar jama'ar Japan ya kai kusan miliyan ɗari da ashirin da uku ne.
Za a gudanar da zaben shugaban kasar Chadi a watan Mayu
Hukumomin Chadi sun ce zaben shugaban kasar
da aka jinkirta, a yanzu za a gudanar da shi a watan Mayu.
Ana sa ran zaben ya kawo karshen
mulkin rikon kwarya da aka fara a 2021 lokacin da aka kashe tsohon
shugaban kasar, Idriss Déby, a fagen daga, bayan shekara
talatin (30) a kan mulki.
A wani mataki da ya saba wa tsarin mulki, an
nada dansa Janar Mahamat Déby a matsayin magajinsa, inda ya yi alkawarin mayar
da kasar ga mulkin dumukuradiyya.
An jinkirta zaben, kuma ana sa ran Janar
Débyn ya tsaya takara.
Masu sharhi na cewa abu ne mai wuya a ce
hukumar zaben kasar ta kasance 'yar-ba-ruwanmu, kuma 'yan hamayya na
fargabar ci gaban mulkin iyalan gidan na Déby a Chadi.
"Ana muzgunawa ma'aikatan agaji a Gaza"
Hukumomin bayar da agaji na Majalisar Dinkin
Duniya sun ce, ana hana su gudanar da ayyukansu a Gaza, sannan kuma ana kai wa
ma'aikatansu hari.
Hukumar jin-kai ta majalisar ta ce sojojin
Isra'ila sun hana ma'aikatanta kwashe marasa lafiya daga asibitin, Al Amal da
ke Khan Younis a shekaran jiya Lahadi.
Wakiliyar BBC ta ce, ''wasu daga cikin
marassa lafiyar da ba sa ma iya tafiya, an tilasta musu ficewa daga motocin
asibiti, ma'aikatan lafiya kuma ana tilasta musu cire tufafinsu.''
Har yanzu dai Isra'ila ba ta ce komai ba a kan zargin.
A yau sojojin sama na Masar sun jefa tan 45 na kayan agaji a arewaci
da tsakiyar Gaza. Sun kuma ce nan da wani lokaci za su kara kaiwa.
Mitoma zai yi jinya har zuwa ƙarshen kakar wasa
An ci tarar tsohon ministan kuɗi na Zimbabwe kan cin mutunci
Asalin hoton, AFP
An ci tarar fitaccen dan siyasar ƙasar Zimbabwe kuma tsohon ministan kudi, Tendai Biti dalar Amurka 300 da kuma zaman gidan yari na tsawon watanni shida bayan da wani alƙalin kotu ya same shi da laifin barazana.
Kotun ta ce ya yi wa wata ‘yar kasuwa ‘yar kasar Rasha tsawa a shekarar 2020.
A cikin shari'ar da aka shafe tsawon shekaru hudu ana yi, shaidu sun ce Biti ya far wa wata mata mai suna Tatiana Aleshina bayan zaman kotu a shekarar 2020, inda ya zage ta da kiranta wawuya tare da nuna ta da yatsa a hanyar da ta yi imanin cewa ya yi mata barazana.
Biti ya musanta zargin da ake masa, kuma ya ce tuhumar ba ta da inganci.
Lauyan Biti, Alec Muchadehama ya ce sun ji takaici matuka amma ba su yi mamakin hukuncin ba. Suna shirin daukaka kara kan tuhumar da ake musu.
Sankarau ya yi ajalin dalibai 20 a Yobe
Akalla dalibai 20 ne suka rasu a wasu makarantun sakandiren kwana da ke kananan hukumomin Potiskum da Fika da Fune a jihar Yobe sakamakon cutar sankarau.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa bayanan da ta samu sun nuna an samu rashe-rashen ne a makarantun Government Science Technical College da Government Girls Science Technical College da kuma Federal Government Girls College dukkan su a karamar hukumar Potiskum.
Bayanan na nuna cewa da dama daga cikin karin wasu da cutar ta shafa suna asibiti suna karbar magani.
Kwamishinan Ilimin firamare da na Sakandare na jihar, Dr Muhammad Sani Idris ya tabbatar da barkewar cutar inda ya kuma amince da mutuwar daliban guda 20. Kamar yadda ya shaida wa jaridar da Daily Trust.
Labarai da dumi-dumi, NLC ta dage zanga-zangar ranar Laraba
Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC ta sanar da janye zanga-zangar neman saukin tsadar rayuwa a ranar ta biyu wato ranar Laraba.
Kungiyar ta ce ta dage zanga-zangar ne ta ranar Laraba ne saboda ta sake bai wa gwamnati karin makonni biyu har zuwa 13 ga watan Maris domin biyan bukatunta.
A ranar Talata ranar farko ta zanga-zangar, daruruwan masu zanga-zangar neman saukin matsin rayuwa da ake ciki a Najeriya ne suka fantsama kan titunan biranen kasar bisa umarnin kungiyar ta kwadago.
Kungiyar kwadago dai ta yi kira da a yi zanga-zangar gargadi ta kwana biyu. To sai dai yanzu kungiyar ta sanar da janye zanga-zangar ta rana ta biyu wato ranar Laraba 28 ga watan Fabrairu.
Kaso 75 na al'ummar Gaza sun rasa matsugunansu
Asalin hoton, EPA
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kusan kashi 75 cikin 100 na al'ummar Gaza, kusan mutane miliyan 1.7, sun riga sun yi rajista a matsayin 'yan gudun hijira kafin Isra'ila ta ba da gargadi ga Falasdinawa su fice daga arewacin Gaza.
'Yan gudun hijirar Falasɗinawa, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana, "mutane ne wadanda Falasɗinu ne wurin zamansu a tsakanin 1 ga Yuni a 1946 zuwa 15 ga Mayu 1948, kuma wadanda suka yi hasarar gidajensu da hanyoyin rayuwa a sakamakon yakin shekarar 1948".
Sama da ƴan gudun hijira 500,000 suna zaune a sansanoni takwas masu yawan jama'a da ke warwatse a ko'ina cikin yankin.
Bayan gargadin da Isra'ila ta yi bayan ranar 7 ga Oktoba, yawancin 'yan gudun hijirar, tare da dubban daruruwan wasu, an tilasta musu barin gidajensu, a cewar MDD.
A halin yanzu, kimanin Falasdinawa miliyan 1.7 ne suka nemi mafaka a matsugunai na wucin gadi ko wuraren da aka kafa a kusa.
Kafin rikicin, yawan al'ummar Gaza ya kai sama da mutum 5,700 a kowace kilomita, kwatankwacin matsakaicin yawan jama'a a birnin London.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa sama da rabin al'ummar Gaza a yanzu suna mafaka a Rafah, garin na mutane 250,000 kacal.
An kashe Musulmi da Kirista a masallaci da coci a Burkina Faso
Akalla mutum 14 ne aka kashe a ranar 25 ga watan Fabrairu a wani hari da aka kai a wani masallaci a garin Natiaboani da ke gabashin ƙasar Burkina Faso.
An kuma harbe wasu masu zuwa coci 15 a wani yanki na kasar, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na cikin gida da dama suka rawaito, ciki har da gwamnatin kasar, kamAR yadda kamfanin dillancin labarai na AIB ya rawaito.
Ƙungiyar hadin kan Musulmai ta ƙasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce mutum 12 ne suka mutu a cikin masallacin yayin da wasu biyu kuma suka mutu sakamakon raunukan da suka samu a cibiyoyin kiwon lafiya na yankin.
Jaridar Daily l'Observateur Paalga ta ruwaito cewa 25 ga Fabrairu "rana ce ta musamman ga fararen hula na Sahel da yankunan gabas".
An kai harin kan mabiya addinin Kirista a yankin arewacin Sahel yayin da Natiaboani ke yankin gabas.
Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin wannan tashin hankalin, amma kungiyar al-Qaeda ta Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) ta yi ikirarin cewa ta ƙwace wani sansanin soji da ke Natiaboani a ranar da aka yi kisan.
Hare-haren ‘yan bindiga kan cibiyoyin tsaro da ma’aikata da kuma fararen hula sun zama ruwan dare a lungunan da ke kan iyakokin Burkina Faso da Nijar da Mali.
Ko ta yaya cigaban tattalin arzikin Najeriya ko akasi ya shafe ku?
Everton da Nottingham Forest ba su da tabbas kan makomarsu
Zalensky na Ukraine ya gana da Yarima mai jiran gado
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine yana kasar Saudiyya domin tattaunawa da Yarima mai jiran gado, Crown Prince Mohammed bin Salman.
Ana dai sa ran za su tattauna yiwuwar shigar Saudiyya domin sansanci wajen musayar fursunoni tsakanin Ukraine da Russia.
Mista Zalensky ya ce za su duba yiwuwar sa hannun Saudiyyar wajen sake gina kasar tasa da kuma taron koli kan zaman lafiya da aka tsara a kasar Switzerland.
A ranar Litinin ne dai Yarima mai jiran gado, Prince Mohammed bn Salman ya karbi bakuncin kakakin majalisar Russia, Vyacheslav Volodin.
Kayan agaji daga Masar sun isa Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Dakarun sojin saman Masar sun rinka jefa kayan abinci ga dandazon 'yan gudun hijra a arewaci da tsakiyar Gaza.
Masar ta ce nan ba da jimawa ba za a kai karin kayan agajin kari a kan na yanzu mai yawan tan 45.
Tallafin kayan agajin da Masar ta samar wa Gaza na da matuƙar muhimmanci yayin da a makon da ya gabata Hukumar Abinci ta Duniya ta dakatar da isar da kayayyaki zuwa arewacin Gaza saboda ana wawashe kayan abinci.
Hukumomin agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun ce an hana su gudanar da ayyukansu a Gaza, kuma ana kai wa ma'aikatansu hari.
Hukumar jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya, Ocha, ta ce sojojin Isra’ila sun hana tawagar kwashe marasa lafiya daga asibitin Al Amal da ke Khan Younis a ranar Lahadi.
Ya ce an tilasta wa marasa lafiya fita daga motocin daukar marasa lafiya yayin da kuma aka sa tawagar likitocinsu su tuɓe.
Har yanzu dai Isra'ila ba ta ce uffan ba game da lamarin ba.
Za a shigar da kayan agaji zuwa Gaza
Isra’ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar kai agaji Gaza
Arteta zai iya komawa Man United - Rio Ferdinand
Malamai a Senegal sun yi watsi da burin Marky Sall na dage zabe
Wasu manyan malaman addinin Musulunci masu fada a ji a Senagl sun yi
fatali da bukatar shugaban ƙasar Macky Sall na jinkirta gudanar da zaɓen kasar
da aka saka ran gudanarwa a cikin watan Yuli.
Shugaban malaman na wannan bayani ne, bayan wani taron kasa da suka
gudanar inda suka tattauna kan samar da sabuwar ranar da za a gudanar da zaɓen,
wanda shugabanin siyasa da na addini masu yawa suka kauracewa.
Babban sakataren kungiyar malaman, MaIsmael Ndiaye, ya shaida wa BBC cewar ba su amince
da a gudanar da zabe ba bayan wata Afrilu ba.
Ya kara da cewa ba za su shiga
cikin wannan tattanawa ba ta bogi.
"Tilas ne shugaban ƙasar ya samar da sabuwar
ranar da za a gudanar da zabe nan da 2 ga wtaan Afrilu." In ji MaIsmael Ndiaye.
Shi ma tsohon ministan kasar, Thierno Alassane Sall, daya ne daga cikin ‘yan
takarar shugabancin kasar da ya ƙauracewa tattaunawar, ya shaida wa BBC cewar sun
bukaci majalisar da ke da alhakin kula da tsarin mulkin kasar su tabbatar
shugaba Macky Sall bai ci gaba da kasancewa a kan mulki ba har zuwa ranar 2 ga
watan Afrelu.
Shugaba Sall ya kuma sanar da aniyarsa ta mika wata takardar bukata a
yau Laraba gaban majalisar kasar don duba bukatar sakin daruruwan mutane, da
aka tsare su a zanga-zanaga daban daban.
Addinin musulunci dai shi ne addini da mafi rinjaye da ‘yan ƙasa ke
bi, wanda matsayar malaman na da matakuar tsiri.
Yan takara a Senegal sun buƙaci a yi zaɓe cikin mako 6
ƙasashe shida da dakarun Ecowas suka taɓa kai wa yaƙi
Hotunan ɓarnar da harin Isra'ila kan Rafah ta haddasa
Har yanzu muna ci gaba da kawo muku labarai game da rikicin Isra'ila da Gaza da kuma halin da mutanen Gaza ke ciki.
Ga wasu hotuna da ke nuna irin ɓarnar da wani harin sama da Isra'ila ta kai a Rafah dake kan iyaka da kudancin kasar inda a halin yanzu Falasɗinawa kusan miliyan 1.5 ke mafaka.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
An sassauta harajin sukari a Zanzibar saboda Azumi
Asalin hoton, BBC Good Food
A cikin watan Ramadan, ƙasar Zanzibar za ta sassauta harajin da aka ƙara kan sukarin da ake shigarwa kasar don sauƙaƙa matsalolin kuɗi.
Shugaban kasar, Hussein Ali Mwinyi ya gargadi ‘yan kasuwa game da hauhawar farashin kayan abinci, inda ya danganta tashin farashin kayyayaki na baya-bayan nan da karancin sukari.
Duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na magance hauhawar farashin kayayyaki, Shugaba Mwinyi nuna rashin jin daɗinsa da ’yan kasuwa marasa gaskiya saboda yadda suke ci gaba da tsadar kayayyaki wanda ke shafar muhimman abubuwa kamar rogo da kifi da kayan lambu da kuma 'ya'yan itatuwa.
Yayin da watan Ramadan ke gabatowa, al’ummar Musulmi masu rinjaye a kasar na neman sauki daga matsalolin tattalin arziki.
Harajin VAT: Muhawara ta barke tsakanin 'yan Najeriya kan daina raba harajin jihohi
Abin da 'yan Najeriya ke son sani kan badaƙalar kudin harajin bankuna
Yadda aka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa a Abuja
'Yan sanda sun kama mai satar jama'a da ake nema ruwa a jallo a Abuja
Asalin hoton, NPF
Rundunar 'yan sandan birnin tarayya wato FCT ta ce ta kama wani mai garkuwa da mutane da ta dade tana nema ruwa a jallo.
Rundunar ta ce mutumin shi ne na biyu a jerin mutanen da suka dade a komarta.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, Sama'ila Wakili da aka fi sani da Habu Ibrahim na daga cikin mutanen da ministan Abuja ya sanya biyan tukwici ga duk wanda ya kama su.
Sanarwar ta kara da cewa an kama Habu Ibrahim ne a dajin Sardauna Forest da ke yankin garin Toto na jihar Nassarawa mai makwabtaka da Abuja, yayin wani samame da rundunar ta kai.
Daga karshe rundunar ta ce mutumin da ake zargin ya amsa laifukansa inda ya amince shi ne ya kitsa da aiwatar da sace-sacen jama'a da dama a Abujar.
Masu garkuwa da mutane sun ɓullo da sabon salon karɓar kudin fansa a Najeriya