Yau ce rana ta ƙarshe ta tattaunawa don warware rikicin siyasa a Senegal
A yau ne aka kawo karshen taron kwanaki biyu na taron kasa da shugaban kasar Senegal Macky Sall ya kaddamar a daidai lokacin da shugabannin siyasar kasar ke kokarin warware rikicin siyasar da ba a taba ganin irinsa ba, sakamakon ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a wannan watan zuwa Disamba.
Shafin yaɗa labarai na PressAfrik ya bayar da rahoton cewa, Sall ya shaida wa mahalarta taron a jiya cewa, a wannan makon ne majalisar za ta amince da yi wa jiga-jigan ƴan siyasa da ake tsare da su daga shekarar 2021 zuwa 2024 afuwa gaba daya, domin sassauta takun-saka dangane da ɗage zaɓen.
Shugaban ya ce tattaunawar da mutum 17 daga cikin 19 da aka tabbatar sun kauracewa zaɓen na da nufin cimma matsaya kan ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da aka ɗage.
Wa'adin shugaba Sall dai zai ƙare a ranar 2 ga watan Afrilu, amma ba zai yiwu a kammala tsarin zaɓen wanda zai gaje shi ba a lokacin.
- Manyan tambayoyin da shugaban Senegal ya ki amsawa a jawabinsa
- Ɗage zaɓen Senegal ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasar - kotu